Sashe 107
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
envelope na gani, da gaske Yaya Huzeifa zan kai wa?" Murmusawa Saleema tayi tace "Da gaske mana, zan miki wasa ne Fareeda?" Jinjina kai Fareeda tayi tace "To shikenan, zan tafi yanzu na kai mishi, Allah yasa alkairi ne." Dariya Saleema tayi tace "Alkairi ne ma in sha Allah." Da haka suka yi sallama Fareeda ta auki adaidaita zuwa gidansu bayan ta sanar da mijinta ya ce ba damuwa, a shago ta sameshi daidai Sudeis ya kawo mishi ruwa daga cikin gidan ya fita, da kallo ta bi yaron da tausayi kafin ta araso ta zauna suna gaisawa yace "Daga ina kike?" "Yaya daga gida." Ta fa a tana ciro envelope in nan a jakarta ta mi a mishi, kallonta ya fara yi yace "Me ye kuma wannan?" Murmushi tayi tace "Karb'i mana Yaya, sa o ne aka ce na kawo maka." "In ji wa?" Ya fa a yana kallonta sosai, saida ta sauke ajiyar zuciya tace "In ji gimbiya Saleema uwa ga mutan mara awa." Gabanshi ne ya fadi sosai har saida ya an dafe irjinshi ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Sai kuma ya kara kallonta yace "Wasa kike min Fareeda?" Sani dake zaune gefensu ne yace "Ta ya zata maka wasa da sunan gimbiya kuma? Kar a ka gani malam." Fareeda kuma sake mi a mishi tayi ya kar a jiki a sa ule ya shiga bu ewa dan hada tambarin dake nuna lallai daga masarautar mara awa sa on ya fito, fito da abun ciki take suka waro idanu dukansu, kallon Fareeda yayi yace" Ku i ne fa." Jinjina masa kai tayi tace" Ta tambayeni ko har yanzu kana inki ne na ce me kuwa zai sa ka daina, ta tambayeni maganar karatunka fa? Na ce rayuwa ce ta sa ka ajiye neman aikin ka ci gaba da sana'arka, shine ta turo wannan ta ce na kawo maka kayi anfani da shi." Kallon ku in yake irin yadda suke mi e zatt sai yalli suke, a hankali ya fara maidasu a envelope in yana fa in" Kenan bata manta dani ba? Kullum gulmata kuke ko?" Dariya Fareeda tayi tace" A'a wallahi Yaya, ni ina ga ma sau biyu ka ai muka ta a... " Da sauri ta nuna mishi wata ar takarda da ta fa o daga ku in tace" Yaya takarda." Aje ku in yayi ya auki takardar ya warware, da manyan ba i da kuma harshen hausa ne aka rubuta sa o kamar haka _" Ka auki hakan a matsayin kyauta daga anwarka, ban ji da in yadda komai ya faru ba, hakan yasa ko godiya ban maka ba, ina ma za ka ga shagon inkina? Na san da ka fini farin ciki."_ Daga asa ka an aka rubuta _*" Nagode Yaya Huzeifi, daga Saleema.*"_ Tun yana sakin murmushi har ya fashe da sanyayyar dariya yana ara kallon takardar kamar wani zararre yake fa in" Allah sarki, Allah sarki, ka ji ita ma shago ta bu e na inki, tabbas na ji da i kula ina miki fatan alkairi, kuma dama na jima da hango hakan, da yardar Allah sai kin fini shahara da cin anfanin inki." Sai kuma ya kalli Fareeda dake ta doka murmushi yace "Ashe bata manta sunan nan ba Huzeifi, ina ma zan ganta da idona ta kirani da Huzeifi ko alhudahuda?" ewa Fareeda tayi tana sa a jakarta tace "Ba ko za ka ganta ba wallahi, dan ko mijinta ba lallai ka gani ba idan ba a tv ba." Hannu ta tara mishi tace "A bani ku in adaidaita to." Dariya yayi ya ciro jaka goma a cikin ku in yace "Fareeda ai kin fi k'arfin na adaidaita, kar i ke ma kisha shagalinki." Godiya ta masa sosai dan ta san dama zai iya yi mata hakan dan har yanzu tsaye yake a kansu da bu atunsu, har za ta fita yace "Idan kunyi waya ki gaidamin ita, kuma ki ce nagode sosai." Jinjina kai tayi ta fita a shagon, Sani dake kallonshi da mmaki ne yace "Ban ta a ganin an maka kyauta ka kar a lokaci guda ba bare kuma har kayi ta wannan farin cikin." Girgiza kai yayi yana murmushi yace "Wannan kyautar ta musamman ce, ku in nan da takardar tamkar kayan tarihi haka zan adanasu." Murmushi Sani yayi yace "To a bani ladar ganin idanuna dai kafin a kaisu gidan tarihin?" Ba musu shi ma ya bashi kamar yadda ya ba Fareeda sauran kuma ya maida a envelope in tare da takardar sannan ya jawo an gidan da ake ajiye zae da allura ya saka ciki kafin ya tashi tafiya gida. Tsananin farin cikin da ya shiga ne ma ya mantar da shi yawan uncin da yake shiga idan Sudeis na kukan Mamanshi wacce yanzu ta kusa kile shekara aya a gidan yari tana kar an hukunci, shi ba dan yaron nan ba da ko tunanin Sharhasila ba zai sake yi ba a rayuwarshi, shiuasa ma haka na faruwa ya tattaro kayan yaron dake gidansu Sharha ya mi awa matarshi amana, yanzu haka ta ha a Sudeis in da aninshi da ta haifa mishi ko wata aya ba'a yi ba. _______________ Abdallah na kwance kan irjinshi yana bacci ita kuma kanta na kan cikinshi tana zanenta a takarda kamar yadda ta saba, kallon yadda take zanen yake yi yace "Matanmu, wato ni ne aka auka shashasha ko?" Kallonshi tayi tace "Lahh! Da aka yi me gwanina?" Hararanta yayi yace "Sai kawai kika koyi inkin mata, ko sau aya ba ki yi tunani a kaina ba." Dariya tayi ta mi afarta aya tace "Kwantar da hankali shalele, ina nan ina zanen yadda babbar rigarka za ta kasance." "Da gaske?" Ya fa a yana kallonta, aga masa gira tayi tace "Da gaske mana." Lumshe idanu yayi yace "Kin san me, ya kamata ki maida hankali kiyi zane na musamman da zaki shigar da kayan gasar fitattun inkuna na wannan shekarar wacce ake yi tsakanin asa da asa." e baki tayi ta zaro idanu tace "Wace ni yalla ai? Ka san da ko shiga nayi sai nayi nasarar lashe gasar a iya nan garin fa kafin na wakilci Mara i mu isa ga matakin arshe a babban birni, haba daina maganar nan ma." A hankali ya tallabo Abdallah ya kwantar da shi gefenshi sannan ya aga kanta sukayi zaune suna kallon juna, hannayenta ya ri e yace" Kinsan wani abu?" Girgiza kai tayi alamar a'a, a nutse yana wasa da yatsunta yace _" Ni ba ma inkiya nake gani a nan zaune tare dani ba, * AR BAIWA* nake gani, Saleema ba wai burinki na son inki ya kasa cika da wuri bane saboda an hanaki cimmasa, ni abinda nayi tunani shine, burinki bai cika da wuri bane saboda babban buri kike auke dashi, ba kowane mai inki bane ke iya zanawa sannan ya fitar, amma kowane mai zane ma inki ne, *Ummu Abdallah*, ki kalli kanki a madubi sannan ki tambayi kanki wa annan amsoshin, na farko wacece ke? Na biyu, me kike so a rayuwarki? Na uku, ya matsayin da kike kai yanzu? Na hu u kuma ki tambayi kanki *Mecece Baiwarki*?"_ afafunshi yayi tare da jawo kanta ya ora a cinyarshi yana shafawa yace" Idan kika samo wannan amsoshin to za ki san manufar da ta sa kika ala antu da inki, baiwarki ba za ta tsaya wajen yi ma mata inkin biki ko na anko bane, idan kika yi tunanin ciyar da harkokinki gaba, ina mai tabbatar miki za'a kai matsayin da duk wata celebrity idan ba ke kika zana mata kayanta ba to za ta ji kamar ba ta cika mace ba." Tunda ya fara magana zuciyarta ke kakkarwa jikinta na tsuma tamkar an fara mata ki an gangi, yanzun da kanta ke saman cinyarshi sai ta shiga sakin murmushi tana shafa cinyarshi, tabbas gaskiya ya yi, kuma ya kamata ta yi wannan tunanin tun tuni, amma hankalinta bai zo nan ba sai yanzu da adalin mijinta ya hasko mata shi. Ha a ba abinda za ta ce ma bawan nan sai godiya, da fari ya cika mata burinta wanda ko iyayenta basu iya taimaka mata da komai ba, yanzu kuma gashi yana son sake orata a hanyar da za ta nemo *BAIWARTA* a duk inda take. *Washe gari* da safe tsaye take gaban madubi tana arewa kanta kallo tamkar yadda yace, irin yadda ta mulmuje tun bayan haihuwarta da kyawun da fatarta tayi, sannan wani leshe ne a jikinta da ta ma sassau inki amma ya yi kyau sosai, ance idanu tayi ta furta "Wacece ni?" Ta jima tana kallon kanta kafin tace _"Wacce aka haifa da buri, sannan za ta mutu da buri, haka Allahn daya haliccemu ya fa a."_ Sai kuma ya karkace kanta tana tuno tambaya ta biyu cewa me take so a rayuwarta? Tsayar da kanta tayi wuri aya tace _"Ina son mijina, iyayena, ana da wa anda zai haifa anan gaba, surukata mai aunata, sai kuma jama'ar da mijina ke mulka... Ummmm! Sai kuma...*sana'ata*."_ Murmushi tayi sannan tace" Sai na uku." Alamar tunani tayi kafin tace _"Matsayi ne na shahara da ban ta a tunanin zan samu kaina a ciki ba."_ Rumgume hannaye tayi tace _*" BAIWATA?* TANA INA? TA YA ZAN SAN TA?"_ urawa kanta idanu tayi ka auka baiwar ce z ata fito a idanunta ta ganta, ta jima haka da sauri ta yasta hannu tace _*" Ilimina na addina, Zanena, inkina, mijina shine *BAIWATA.*"_ Da sauri ta juya ta fita a akin ta nufi akinshi dan sanar dashi ta gano *BAIWARTA* itama yanzu, abu ne da bata ta a tunanin kawoshi a ranta ba bare ta tambayi kanta mecece baiwar ta ta, amma sanadiyar mijinta gashi yau ta gano baiwarta, a hakan ma wai wanda suka bayyana a gareta ne, baya ga hadda data samu ta Al ur'ani a yanayin da babu wanda yayi tsammanin za'a samu duba da a tarihi ita kanta ba ta san wani da ya samu karatu a yadda ta samu ba ba tare da ya dur usa gaban malami ba, hakan ma babbar *BAIWARTA CE*, ta san kuma Allah ya yassare mata lamarin ne saboda halin da ta samu kanta a ciki na matsi da takuran mahaifi