Sashe 109
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko? To ai ka san bana sallah, ba dan haka ba ai kasan ni mai amsa kiranka ce a kowane lokaci." aga kanshi yayi dake kwance a irjinta yace" Na sani, yanzun ma tallafinki nake nema dan na samu bacci ya aukeni." Murmushi ta sakar masa ta an juya ka an ta kalli Abdallah dake zaune bakin gadon yana ta danna waya, kallonshi ta sake yi tace" Ya zamuyi da shi? Kafi kowa sanin rigimar Abbanmu." Girgiza mata kai yayi yace" Ba dai Abbana ba, sai dai anki." Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tace" A gafarceni to, anka." agata yayi ya tashi tsaye tare da nufa wajen yaron yace" Bari na mi a shi wajen Ummi." Rusunawa yayi gaban Abdallah yana son kar e wayar yace" Yarimana, an Abbanshi, tashi muje wajen Mamie, za tabka alawa mai da Kallonshi yaron yayi sai kuma ya sake maida dubanshi ga wayar, Mi ewa yayi tsaye dan dama yasan ba saurarenshi zaiyi ba, cak! Ya aukeshi daga shi har wayar ya fita daga akin yana ci gaba da rarrashinshi. Ganin sun fita yasa ta saurin tattara kayan data baza ta ajiye kan kujera da sauri ta fa a ban akin shi dan sake watsa ruwa a jikinta. *Bayan Wata Biyu* Da fara'a da kuma mamaki ya arasa shigowa falon hannayensa biyu da ledoji, a tsakiyar falon ya aje yana kallon Safiya dake cin abinci saboda azumin da tayi yasa sai yanzu take ci yace "Umman gimbiya sa o ne daga arki fa, duba mana ki gani me ye?" arin cire hannunta tayi tana fa in "To, sa o kuma? Wa ya kawo yanzu a daren nan?" Kujerar kusa da ita ya zauna yana fa in "Baki ji an ce ana sallama ba? Ina fita na ga dreban can gidan..." Sai kuma ya kalli Ardiya dake fitowa daga falonshi tana kwashe kwanukan abinci yace "Yawwa uwar an matana. Zo duba mana..." Ya fa a yana kallon Safiya da har ta mi e yace "Zauna ma bari ta duba." arasowa Ardiya tayi tana aje kwanukan bakinta har kunne tana murmushi ta dur usa tace "Tohh! Abban Hadeeya me muka samu? Ba dai kayan sallah ka aro mana ba?" Murmushi yayi yana kallon ledar da take kiciniyar bu ewa yace "Ke dai bu e mu gani." A hankali ta fara ciro kayan ciki tana zazzaro idanu saboda dole ta nutsu wajen cirosu dan a goge suke a kwance, saida ta gama fito dasu gaba aya ta aje kan ledojin sannan ta fara kallon kayan. Sak iri aya ne kayan, sai dai kowane an an li a wani aramin kati mai auke da tambarin sunan *gimbiya Couture* aya an rubuta sunan *Mama Sofee*, ayan kuma an saka sunan *Mama Deeya*, sunan data karanta yasa ta sakin murmushin da bata shirya ba dan kuwa zahirin gaskiya daga zuciyarta ya fito, abu aya da ta kawo a ranta shine *tabbas aikin Saleema ne*, dan ita ka ai za ta basu wannan darajar. A hankali ta kai hannunta ta shafi lafiyayyar shaddar nan da ake wa la abi da *miel*, kuma tabbas ta ci sunanta dan kuwa haka take mai o tana aukar idanu ga mai kallonta, a dai yanzu a saninta nan kusa shaddar nan idan ba ita ce ta farko a farashin arshe ba to ba zata gaza zuwa ta biyu ba. Ga kuma an uban leshen da ita dai ta san ku inshi an ce mata dubu ari biyu har da sittin a haka fa wai daga Kano ma ba a nan garin ba. Ita yanzu abinda ba ta gane ba shine... Sai kuma ta juyo da sauri ta kalleshi tace "Alhaji, kayan waye wannan? Wa ya aiko su?" e baki yayi yace "Aka ce wai daga gi..." Wayarshi da tayi ruri ne yasa ya yi shiru ya shiga lalubenta a aljihu, yana ganin Saleema ce ya aga yace "Hajiata." aga angarenta a nutse tace "Abba, ai an kawo sa on ko?" "E an kawo, gashi kuma sai tambayata suke wa ya aiko?" Ya fa a yana tsare Ardiya da idanu, a ladabce tace "Abba, na kune mana kai da su Mama da aunty, kowane da sunanshi a kai." Numfasawa tayi kafin tace "Envelope in kuma, shi ya ce a baku tun kafin su tafi Saudia." Da fara'a yace "Masha Allah Hajiata, yanzu ke kika musu wannan inkin? To angode sosai." A nutse sosai kuma a sanyaye tace "Abba..." Sai kuma tayi shiru tayi saurin fa in "Saida safe." Kashe wayar tayi duk da ta so ta ro eshi sa albarkarshi, wanda har yanzu take tsumayin ji daga bakinshi, tana so ta ji ya ce ina alfahari da ke kamar yadda ya dinga sakawa su Hadeeya a gabanta tana arama, amma da ta tuna ai ro ane za ta yi kenan ba ta cancanta ba har yanzu? Sai kawai ba ta fa in ba ta yalleshi da tunanin watarana zai fa a dan ganin damarshi. Tunda ta fahimci wayar da yake fa tana tabbatar da wannan kayan nasu ne yasa ta sake aukan wanda ke da sunanta tana dubawa, har Alhaji Yusuf ya taso ya kai hannu kan kayan ya auki envelope in bata san yayi ba, Mi ewa tayi tsayetana fa in "Ikon Allah! Aaaa... Saleema ce ta aiko mana wannan kayan?" Sai kuma ta aje nata ta auki na Safiya data koma ta zauna ko kallon kayan ba ta sake yi ba tunda ta ji suna waya ta mi o mata tace "Kin gani fa *Maman Hajia*?" aga kai Safiya tayi ta kalleta jin sunan data kirata da shi, sai kuma ta kalli kayan ta yi murmushi tace "Masha Allah, Allah yasa albarka, idan na gama zan duba." Dariya Ardiya tayi tace "To shikenan, bari na aje miki." Ta aje kayan kan aramin teburi ta auki nata ta juya zata wuce akinta dan magana ta gaskiya ihu take so ta tsala, idan tana gabansu kuma ba zata iya ba, dan yanzu ma wannan fara'ar so take ta oye amma ta oyuwa, tana daf da wucewa Alhaji Yusuf yace "Ga ku in ragunan layyarku ma sun samu." Juyowa tayi tace "Kuma dai?" Jinjina mata kai yayi alamar e, dariya tayi tace "Ina zuwa." Shigewa tayi shi kuma ya bita da kallo, yadsa ya santa da son ku i ai ya auka za ta dawo ne ta tambayeshi nawa ne kafin ta yi arin rabashi da wani abu, hakan yasa ya tabbatarwa kanshi lalle abinda aka bata yafi wanda ke hannunshi yawa. Sake aukar kayan yayi na maza da Ardiya ko ta kansu bata bi ba, galleliyar gezna ce wacce daga amshin ya gane haka, tasha babban inkin daya dace da ita ga kuma kwalin daya tabbatar masa da turare ne mai sunan 24h, murmushi ya saki a fuskarshi tare da furta " *Hajiata kenan, akwai sanin takamata.*" akinshi ya nufa da nashi kayan su ka bar Safiya ita aya a falon a zuciyarta tana ta saka mata albarka tana kuma kara kallon kayan wanda alamu suka nuna tabbas hada na Ahmad, amma Ardiya da ta ci karo da wannan tsadaddi ta kuma tabbatar hada ita sai bata sake bi ta kan komai ba duk ta rikice. Tana shiga akinta wayarta ta auka ta kira Agaishat, saidai tana agawa Agaishat in tace "Ba dai ke ma abinda kika kira ki fa a min ba kenan?" Da mamaki Ardiya tace "Me fa?" Daga wajen Agaishat tace "Ko baki ji yarinyar nan ta haihu bane?" Da jin haushi Ardiya tace "Wace yarinya kuma? Wai ya kike bani bayani a dun ule?" "Khairat mana, kishiyar Hajia Iklima." Ta fa a tana daga murya, tsaki Ardiya tayi tace "To me ya dame mu, kinga can fa matsalarta ce, ita ba ta nuna ba'a isa a mata kishiya ba? To ai gashi nan da ranta tana gani kishiyar na ta haihuwa, sai me kuma?" Kallon kanta tayi a madabi tace "Kinsan wani abu? Yarinyar nan fa..." Sai kuma shiru kamar mai tunani kafin tace "Yaushe ta haihu?" "Ta ce min azu da yamma ne." Cewar Agaishat, murmushi Ardiya tayi tace "Rana kamar ta yau suna kenan? Bikin matar gwamna, duk da tenure ta kusa arewa, amma dai nasan za'a tara manyan mata, dan haka na fasa fa a miki abinda yasa na kiraki, ranar sunan idan mun ha e kin gani." Da mamaki Agaishat tace "Za ki je kenan? Bayan kisan haihuwarta ta farko ma da muka je muka dinga wula anta dangin amaryar saida ran Hajia I lima ya ace a wajen shi excellency?" Yatsina baki tayi tace "Sai me? Zamu je, kuma babu abinda za'a fasa, kinsan me? Ita Iklimar nan ba tana ganin tafi kowa saka abu mai kyau da tsada ba? To za ta gani ranar sunan nan, ai na so ma ace ita ce ta haihu wallahi ta ga rashin mutumci, da ta ga yadda zan jera kafa a da kafa a da ita tsabar ha uwa." Dariya Agaishat tyi tace" Ga dukkan alama akwai babban kamun da kika yi, zan zuba idanu na ga wannan shirin naki." "Zaki gani." Ardiya ta fa a cike da tabbaci kafin tace "Saida safe malama, yau da gobe duk nice aiki, gyaran nama na can na jirana, dan ma na sa mai aiki ta fara kafin na fito." Da dariua Agaishat tace "To sai da safe, ni ai nayi sa'a yau na saki, amma a banza tunda waccen uwar shishigin da matar Mu'az sune ke mata aikin ita tana zaune." Dariya Ardiya tayi tace "To ai ta haifa ne, kinga dole ta huta." e baki Agaishat tayi tace "Hmmmm! Ke dai saida safe." Da haka sukayi sallama kowa da abinda ke zuciyarshi.