← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 116

Sashe 13

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sallah irin haka har ta manta, ma fi yawan lokuta dama Mamanta ke tashinta daga bacci, sauran lokuta kuma ita ke tashi da kanta da taimakon wayar Mamanta, juyowa tayi ta kalli Hameeda da ta sake gyara kwanciyarta tace "Dan Allah ki tashi Hameeda, ki tashe su suma su yi sallah." Shigewa ban- akin ta yi ta gabatar da abinda za ta yi ta fito a gaggauce, yanda ta barta haka ta sameta, ganin za ta ata lokaci wajen tashinsu ita ta makara su su rasa yasa kawai ta canza kayanta ta kabarta sallarta, duk da farilla ce a kanta yanzu, amma saida ta fara yin raka'atanil fijir saboda ta ji fatawar da aka ce indai ka saba yin raka'a biyu kafin fitowar alfijir, to ba laifi idan wani dalili ya sa sallah ta kubce maka ka yi kafin ka yi ta farilla, har ta idar da sallata su Hadeeya ba su motsa ba, cike da takaici ta mi e ta koma ban- akin ta auko aramar buta da ruwa a ciki, dan su ne ka ai za su iya tashinsu, ta na zuwa kam aya bayan aya ta dinga watsa musu suna tashi a zabure kamar wa anda aka firgita. Cike da tsiwa da rashin kirki Ummee tace "Malama me ye haka? Wannan wane irin jahilci ne? Ya mutane suna bacci za ki tashesu da ruwa? Ba ki da hankali ne?" an cije le e Saleema ta yi ta lumshe idonta, hakan ya bata damar ha e abunda ke ranta kafin ta bu e ta kalleta tace "Ku yi sallah, lokaci na wucewa." Hadeeya ce tace "Saboda hakane ki ka tashemu? Dan baki san darajar an adam ba." Da alamu irin na ba ta jin da in maganar ranta kuma ya fara acewa ta kawar da kanta ka an tace "Da sallah ku ka je kuka gabatar ya fi muku alkairi." Juyawa tayi tana cire hijabinta Ummee tace "An i a yi sallar to, dole n..." Fauuuu! Cikin zafin nama Saleema ta kashe fuskarta da mari, a ki ime Ummee ta dafe kunci tana kallon Saleema, Hadeeya da Hameeda ma a tsorace da kuma mamaki suke kallon Saleema, yo ko su dake annenta ba ta ta a marin aya daga cikinsu ba, hasalima ko fa a irin wannan na yara ba su cika yi ba. Girgiza kai Saleema tayi cikin jin haushi tace "Kin gani, kin hassalani, kina ar musulma ne za ki furta wannan kalmar? Kin kuwa san hukuncinki a wannan lokacin?" Ummee da takaici ya gama kasheta a mugun haukace ta nuna kanta tace "Ni kika mara?" A tausashe ka rantse ba ita ce ta mareta ba tace "An mareki, ki rama mana." A harzu e Ummee ta sauko daga kan gadon ta yi hanyar fita tana fa in "Na zan rama da kaina ba, amma zan kira wanda zai rama min." e baki Saleema tayi da tunanin Allah yasa ma rayuka su ace ta samu damar tafiyarta daga wannan gida mai cike da kuraye ta ko ina, wa ya sani ma ko gado sukayi? A nutse ta gyara aurin an-kwalin doguwar rigar da ta saka ta jawo silifas inta ta saka, ta kala hanya za ta fita ta juyo ta kalli su Hadeeya da har yanzu ke kallon kamar ba sa hayyacinsu tace "Sallar fa?" Da sauri Hameeda ta sauko daga gadon ta nufi ban- akin da alamar ta tsorata, Hadeeya kula saida ta murgu a baki kafin ta sauko ta nufi ban- akin ta tsaya tana jiran fitowar Hameeda. Murmushi tayi da ke nuna "Ku shiga hankalinku tun wuri." Za ta fita a akin amarya ta banko kai cike da masifa hannunta ri e da hannun Ummee, a bayanta kuma Alhaji Auwal ne da Hajia babba a gefenshi. Kallon kallo suka dinga yi kafin amarya ta nuna Saleema tace "Ke! A kan wane dalili ki ka marar min Saleema dake mamakin ganin yanayinsu dukansu, kayan da ke jikinsu bai nuna alamar su kansu sun yi sallah ba, dama-dama ma Hajia babba da alamar ruwa a jikinta, wata ila alwala ta yi dan ko hular kanta bata ora dai-dai ba, cike da kunya ta kalli amaryar a ladabce tace "Aunty, sallah na tashesu su yi ba su tashi ba, shi ne ita ta ke fa in wai an i a yi sallar, shiyasa na mareta." umbin mamaki amarya tace "Shiyasa kika mareta? Ke baki san fuska daraja ne da ita ba? Kawai sai ki mareta dan ta ce an Da mamaki Saleema ta kalleta tace "Fuskar ce ke da daraja? Wa ya fa Cike da sababi amarya tace "Ai ko a wa'azi ana fa a cewa babu kyau dukan mace a fuska saboda tana da daraja." Wani an murmushi Saleema tayi cike da raha tace "To aunty ai wanda ya ba fuskar daraja shi ne kuma ya ce shi ka ai yake so a turmusa fuskar nan asa dominshi, kenan ya dace ta ce ba za ta yi ba?" A hassale amarya ta sake nunota da yatsa tace "Ke Saleema! Tunda kika zo gidan nan dama na fahimci wani tsageran iskanci kike ji, to ni bana son irin haka, ki tsaya a matsayinki kawai, amma ya za ki zo gidan uban yarinya kuma ki mareta, ina aka ta a haka?" Gyara tsayuwa Alhaji Auwal yayi wanda da farko jikinshi ne yayi sanyi, duba da an mari arsa akan ba ta yi sallah ba, to ya kenan shi idan ta ji bai tashi ba sai kukan Ummee ne ya tasheshi shi da uwar Ummeen? Cikin nutsuwa ya kalli Ummee yace" Ke je kiyi sallah." Sai kuma ya kalli Saleema yace" Shikenan ya wuce, kowa ta je ta yi sallah." Cike da damuwa Saleema tace" Ni na yi sallah Abba, amma dai ka fa a musu su dinga tsayar da sallah a kan lokacinta, kamar Ummee da su Hadeeya idan aka umarcesu suyi sallah su ka i kuma ba tare da wani uziri ba, sannan sun yarda babu abun bauta da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne, aka tabbatar sun yarda da duka shika-shikan musulunci, to fa wasu suna ganin kashesu za'ayi ta hanyar cire musu kai, wasu kuma suna ganin a'a za'a jinkirta musu ne su yi sallar sannan ya kashesu..." Tausasa murya tayi sosai sannan tace" Abba, yanzu duk lamarin da aka tanadar wa wannan hukuncin bai kamata mu ri eshi iya arfinmu ba? Manyan Malamai magabata akwai masu fahimtar wanda duk ya bar sallah ta kubce masa da-gangan to ya zama kafiri, idan har zai yi sallah ta gaba ko ya ranka wannan sallar to a ganinsu sai an kuma bashi kalmar shahada, inda wasu malaman ke ganin a'a ba ka kafirta ba, sai dai ko kayi sallar ba lallai ubangiji ya amsheta ba saboda kayi kan lokacinta ba, dan haka wasu suke ganin kar ma kayi shi ya fi." Raunana murya tayi kamar za ta fashe da kuka tace" Ta ya bayan na san wannan zan zuba ma an uwana ido suyi wasa da sallah, bayan dukaninmu nan mun san ita ce kawai ta bambamta mu da kafiri, indiyawa su na azumi dan bu atunsu da al'adunsu, mu ma musulmi munayi, krista suna raba dukiyarsu ga mabu ata, akwai daga cikin wa anda ba su da addini da suke zuwa ziyarar akin Allah, imma dan bu atarsu ko kuma ganin al'ajabin wurin da aukar rahoto, sannan kafirai dayawa sun yarda akwai Allah kuma shi ya haliccesu kamar dai mu, sannan sun yarda Annabi Manzonsa ne, imani da shi ne kawai ba su yi ba, to ku fa a min a nan me ya rabamu da su? Sallah ce kawai ko arne ya ga mai yin ta zai sa wannan musulmi ba tare da ya yi tambaya ba." Kallon Ummee ta yi da jikinta ya mutu sosai tace" Ki tsayar da sallarki, za ta zame miki haske a abarinki, sannan idan sallarki ta yi kyau a sikelin lahira, to hisabi ma bai zama lalle gareki ba." Ita kanta amarya da bala'i ne ya kawota sosai jikinta mutu ta ji zuciyarta na dukan tara-tara tunawa da yanda ita ta auki sallarta, sai kawai ta juya jiki a sanyaye ta bar akin, haka Alhaji Auwal da Hajia Rabi ma suka fita suna jin gaba- aya yarinyar ta gama auresu da wasu manya-manyan igiyoyi da ba zasu iya kwance kansu ba. Ganin haka Saleema ta fita a akin ta hauro asa tare da Hajia babba wacce yanzu akinta ke asa sablda wuyar da hawa saman ke mata, cikin ladabi ta tabayeta "Mama, zan iya shiga madafa?" Murmushi ta sakar mata tace "Me zai hana Saleema, ki shiga ki auki duk abinda kinke so." Girgiza kai Saleema tayi tace "A'a Mama ba dan bu atata ba ne, abun kari zan ha a, na ga mai aiki ba a nan take kwana ba." Girgiza kai tayi ita ma tace "A'a Saleema, ki bari na gama sallah sai na ora, dama sai rana ta yi take zuwa, iya shara da wanke-wanke da sauran ayuka take yi, amma girki mu ke yi sai dai ta taimaka mana da wani abun kawai, dan Alhaji baya son cin abincin mai aiki." ar dariya tayi tace" Hakan ya yi kyau, kamar Babana shi ma haka yake, amma ki bari ni zan ora, idan da bu ata ku sai ku ora na Abba idan kun ida sallah." a murmushi tayi tace" Nagode Saleema, Allah miki albarka." Da fara'a ita ma ta amsa da" Nagode Mama, amma me za'a dafa?" Da fara'a tace" Saleema ko me kika dafa ma ai ya yi, ki duba a madafar akwai duk abun bu ata, idan kuma kin rasa wani abun ki min magana." Jinjina kai tayi cike da ladabi ta wuce madafar inda ta fara da abinda ta gani kuma ta iya sarrafawa. Hajia Rabi na idar da sallah ta fito za ta shiga wajen Alhaji dan tambayarshi abinda zai ci, Mu'az ne ya shigo gidan dan bai kwana a gida ba, tsaye tayi har ya araso yana gaisheta da "Ina kwana Mama." Na wasu da u ta fara zuba masa ido kafin tace "Ba'a gida ka kwana ba ko?" Ba tare da damuwar komai ba ya amsa da "E Mama." Ba alamar wasa a tare da
Chapter 13 · 0% Book details