Sashe 68
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasu lokutan da take hakan ba da sanin mahaifinta ba. Kwana biyu ya rage ta kammala abinda take mahaifinta ya ce ta dawo, ba ta yi gardama ba ta dawo gidan, sai dai da ta zo daga inda ya kaisu ita da Hameeda da Hamdeeya ya nuna mata yana musu shirin tafiya ne, sai dai bai fa a musu ba kuma ba ta tambaya ba. *Bayan Wata Uku* Da mamaki Saleema ta sake kallon Khairat in tace "Da gaske wai kike ko wasa? Ni dai a sanina ban ji an kawo kayanki ba? Kuma..." Sai tayi murmushi tace "Kai ban ma yarda ba sam." Dariya Khairat tayi ta ri o hannun Saleema tace "" Wallahi da gaske ne Saleema, kin san me yasa haka?" Da kallon tuhuma ta bita tace" Yanzu Khairat har gobe za'a aura miki aure amma ki kasa fa a min, halan wani abu na miki da kika ri eni?" Girgiza mata kai tayi tace" A'a Saleema ko aya, ki tsaya ki saurareni mana sai ki ji dalilin da yasa haka ta faru." Kawar da kai tayi tace" ina jinki to." Cikin nutsuwa Khairat ta fara fa in" Kinsan ai gwamna Alhaji Nasir ya zo lokacin saukarmu? To shine wata aya da ya wuce sakataranshi ya zo wajen Yaya (malaminsu) ya ce gwamna ne ya wakiltashi ya sama mishi yarinya mai hankali da nutsuwa yana so zai ara aure, to da sukayi shawara da Mamanmu sai ta fara tuntu ata da maganar, dan ita a ganinta bai kyautu idan haka zai zama sharri ya faru ga waya ar da Yayana ya za a mishi ba, amma idan ni ce ba wanda zai zargesu duba da bayanin sakataran ya ce sa o daga gwamna ko da an samu yarinyar to ana son wacce iyayenta zasu amince a anin lokaci saboda baya so kowa ya ji bare a kawo masa tangar a game da maganar, shiyasa Mamana ta shawarce ni ta ce na amince, idan alkairi ne zasuyi farin ciki da haka, idan kuma sharri ne ya tsaya iya kanmu kawai, amma idan kan waya ar ne da Yaya zai yi shugabanci za'a iya cewa dama an sani aka ha ata da shi in, duk da a yanzu ma wasu na ganin kwa ayi ne ya samu yin haka duba da mu ba masu ku i bane, amma na taushe kunnuwana tamkar yadda Yaya da Mama suka fa amin, to shiyasa kika ga ba'a sanar da kowa maganar ba, dangin mahaifina ka ai dake da alhakin sani suka sani, dan aurin auren ma a masallaci za'a yi gobe bayan sallah juma'a." A sanyaye cike da rarrashi tace" Kiyi ha uri Saleema da ban fa a miki da wuri ba." Murmushi Saleema tayi tare da nuna tamkar bata san ma waye gwamnan ba da abinda ya shiga tsakaninsu tace" A gaskiya Khairat na miki murna da samun nagartaccen mutum kamar wannan, Allah yasa hakan ya zama alkairi a rayuwarki, Allah yasa shine abokin tarayyarki ma fi alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ta gari." Murmushi Khairat tayi tace" Nagode sosai, amma dai za ki zo goben ko? Dan a goben fa zan tare." Waro idanu Saleema tayi tace" Iyee! Khairat a matse kike ne?" Dariya ta yale da ita tace" To idan ban kasance haka ba ya kike so na yi? Kuma fa ni ba abinda nake nufi ba kenan." Dariya Saleema tayi tace" Shikenan Allah kaimu goben." "Ameen." Khairat ta fa a tana sakin hannunta, wata hirar suka ci gaba da yi har azahar kafin Saleema ta koma gida dan dama kiran Khairat in ne ya sa ta zuwa gidan da ta jima ba ta je ba, dan malaminsu yana yawan yi mata maganar ta dawo makaranta, ita kuma tsoron abinda Abbansu zai ce yasa take kasa bashi amsar da ta dace, sai kawai take ara zurfafa karatunta ta hanyar sanin Khairat in a waya shi ma ba kullum ba. *Juma'a 02:30* Hawayen da suka wanke mata fuska a anin lokaci yake kallo da mamaki, a tausashe kamar mai son rarrashinshi tace "Yalla ai kar ka min haka, ka fa amin wasa kake yi dan Allah, wallahi idan wasar nan taka tayi nisa zan iya rasa rayuwata, ka ce wasa kake min ka ji?" Lumshe idanunshi yayi daga cikin farin gilashinshi tas sannan ya bu e a kanta ya ora afarshi aya kan aya a tsanake yace" Ba wasa a maganar nan, saboda aurin auren ne na dawo yau in nan." A mugun razane ta mi e tsaye cikin tsawar da ta sakashi li e idanu tace" Me? Da gaske ne kenan? Lallai ma." Kallon uwar gidan tayi mata mai cike da nutsuwa da dattako a haukace tace mata" Wannan ni dama ba kishi nake da ita ba, amma me yasa ita ba tayi mamaki ba?" Fuskarshi ya fara ha ewa sannan yace" Saboda ita ta sani ne tunda na fara neman auren." Wani ihu tayi ta shiga juyawa a tsakiyar akin tana fa in" E fa, na gane komai, wato ni ce ar iska a gidan nan, ni ce ban da matsayi da mu amin da za'a fa amin ba, to ni a me ka aukeni?" Ta fa a tana tsaya wuri aya da kallonshi, a hankali ya sauke afarshi aya ya mi e tsaye, hakan yasa uwar gidan tasowa da sauri ta matso dan ita ta fita sanin waye shi, tsaf zai mata haukan da ya fi nata, dan kasancewar rigar dake jikinshi ba ita zata saka ka yi masa abinsa ka ga dama ba, tsaresu tayi da idanu jira take ta ga ya aga hannu zai gaura mata mari ta dakatar da shi, sai dai a sanyaye taga ya kalli Iklimar yace "Kina ji? Ki daina min ihu a kai bana so, aure ne an riga an aura min, ke baki isa kiyi komai ba, idan kuma kina ganin za ki tsorata tane kamar yadda kika tsorata Haleema, to bismillah." Zazzare idanu ta fara yi hatta zufa ta mata sharkaf, baya ga imuwar da take ciki har da sanin ita ta lalata auren shi da Saleema a yadda take gani kuma su Ardiya ke nuna mata, ashe ya sani shine bai ta a nuna mata ba? Juyawa yayi zai bar falon cikin gunjin kuka tace "Amma yalla ai shine za ka ha ani kishi da wata antacciyar yarinya, talaka ar talakawa? Ni wallahi yanzu na yarda ka saketa ka auro Saleemar ta fi min dama-dama, ko ba komai ita ma daga babban gida take, amma wannan ai..." Kawai ta fa i gurin ta kifa kanta a kujera tana gunjin kuka tamkar sa on rasuwar iyayenta aka fa a mata, girgiza kai yayi ya sa kai ya tafiyarsa dan shi gane yake hauka kawai take, yanzu ba ga ar uwarta nan ba da ta kwantar da hankali ta nuna masa tana tare da shi, da ita aka yi shawarar komai wanda hakan ya sake kankaro mata lodin mutumci a wajenshi, kuma a yanzun ji yake ko amaryar da yake zumu i sai ya sa a mata a kan uwargidansa, dan ba zai yarda wata ko wani su ba anta ranta ba. _Daga nan za mu jingene labarin gwamna da rayuwar gdansa, daga dai yadda ya faru yanzun kunsan za'a samu hargitse, akwai abubuwa a gabanmu dan haka zan rufe a yanzu, wata ila daga arshe na ta o mana su dan jin yadda aka arata, in sha Allah._ _______________ Tsaye take inda babban teburin da suke yanka kaya ke gabanta, hijabinta mai hannaye ta an tattara daga asa ta aureshi saboda yankan d zatayi, shigowar Mubarak tare da wani yasa Huzeifa saurin tasowa ya tare ofar shigar, daga Saleemar har su in kallonshi suke da tunanin wani abun ne ya sakashi yin haka. Mubarak ne yace "Yaya wucewa zamuyi, kayan nan nake son kammalawa." Juyowa yaui ya kalli Saleema da ta fara yanka rigar tamkar yadda ya ce ta yi, ha e fuska yayi sosai in nan murya a dake ba alamar wasa yace "Ke saki hijabinki." Kallonshi tayi sannan ta kalli hijabin sai kuma ta sake kallonshi tace "Yana hanani aiki da kyau ne, shiyasa na d..." Harara ya watso mata yace "Na ce ki saki." Turo baki tayi ta warware hijabin ta ci gaba da aikin gabanta, shi kuma ya kauce musu a hanyar suka shigo Mubarak na dariya da fa in "Idan ta yi wari ma ji wallahi." Kowa aikinshi yake ba mai ce ma wani ala inda Mubarak ya an kunna sauti a wayarshi, hakan ne ya hana shagon yin shiru dayawa, sai da ta yanka siket in ne ta kalleshi tace "Duba min ka ga girman nan ya yi?" Ba tare daya kalleta ba yace "Ki duba kayan matar suna nan kusa da ke." Yatsina baki tayi tace "Bana son kallo ne har na gama, na fi so idan na auna mutum sau aya to na gane yanayinshi." ago kai yayi ya kalleta ya dakata da inkin da yake yace "Allah ko?" aga masa gira tayi alamar e, hakan yasa shi sakar mata wani kallon da ta yi saurin kawar da dubanshi gareta, kallon Mubarak tayi ta ga shima aikin yake, dan haka ta kalli ayan dake zaune kan kujera yana yanka akan telar dake inkin aramar yarinya ne tace "Dan Allah Sani dan uba min ka gani, ai ka gane matar ko? So nake idan ya yi aka fa amin to nayi daidai kenan." "Uhum." Ya fa a yana tasowa, yana zuwa gefenta ya tsaya yana dubawa sai kuma ya kalli Huzeifa "Ai kayan Sa'adatu ne?" A hassale da bai san me ya sameshi ba yanzu idanunshi na kan kafa ar da Saleema da ta Sani da suke neman ha ewa yace "Ban sani ba, na ce ta duba kayan matar ta i, tun jiya da aka kawo kayan na ce ta rubuta kamar yadda muke ta i, ya zan mata? Rabu da ita ka ji." Nuna masa wajen zamanshi yayi yace "Je ka ci gaba da aikinka malam, barni da ita." Da mamaki da kuma ulluwa Saleema ta aje almakashin dan lokuta da dama yana yawan mata irin haka, kuma baya mata sai idan da maza a shagon, cike da sangarta da wauta tace "Shine zaka aga min