← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 116

Sashe 52

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafa arshi yace "Abokina, me ye matsalar?" A hankali numfashinshi ya fara sauyawa alamar bacci na son aukarshi, dan haka ba wanda ya ce komai har saida suka tabbatar baccin ya aukeshi, cike da damuwa Alhaji Auwal yace "Me yake damunshi? Kin ji fa Alhaji Yusuf ne ya dawo dashi gidan nan." Duk kallonshi sukayi kafin Hajia Rabi tace "To me ya sameshi?" Ba tare da tauna harshenta ba Gaishata tace "Wata ila sihirin da mayyar nan ta mishi ne ya sakeshi." A tare kowa dake wurin suka kalleta, da mamaki da kuma yanayi na acin rai Alhaji yace "Kamar ya? Kina lafiya kuwa?" e baki tayi ta auke kanta ta mayar kan Nafissa da shigowarta kenan da yanayi na tashin hankali jin an ce Mu'az baya da lafiya, cike da antawa da wula anci ta yatsina fuskarta tana kallon Nafissa tace "Malama lafiyar shigo mana nan?" Sai kuma ta nuna mata ofa a sanyaye tace "Dallah fice a nan kinji." Jiki a sanyaye Nafissa ta juya za ta fita, kallonta Hajia Rabi tayi tace "Ya za ki yi haka kema? Ita ma yanzu ai ar gida ce." auke kai tayi dan ba za ta yarda ta fa a mata maganar da tayi kama da rashin kunya ba a gaban Alhaji, arasa fita Nafissa tayi ba tare da hakan ya dameta ba, dan in da sabo ta saba, a kwanakin nan da tayi matsayin suruka a gidan, babu wani abu da mahaifiyar mijinta ta mata da zai nuna mata za ta so ta, haka shi ma mijin abinda take fuskanta kenan a wajenshi, tsangwama, duka, hantara da kyara ga wula anci. Saida ta fita ya kalli Mu'awwaz da ke tsaye hannayenshi har e yace "Bi bayan matarka." Saida ya kalli mahaifin nashi ya wani jijjiga kai irin an takurashi fa kafin ya juya ya fita da tunanin a kan Nafissa zai huce. Yana fita ya kalleta da yanayin zafi da garga i yace "Kinga Gaishata, ina rabaki da shiga shirgin yarinyar nan, ita fa matar anki ce, ta ya zaki siyawa kanki raini a wurinta? Tunda kin ce ke ba da sonki aka aureta ba kuma ba kya aunarta, to ki zuba mata idanu mana ki kallesu, a ganinki dan kina hore masa a kunne a kanta bayn sun ke e zai zuba mata idanu ne? Ke yake mayarwa shashasha wallahi." Bata kulashi ba dan gaskiya bata san wula ancin nan da yake mata yanzu, ta kula ba sonta yake ba yanzu sai dai burin tozartata a gaban al'umma, dan haka da ya ga bata tankashi ba sai ya fice a akin ya barsu, Hajia Rabi ma da matsalar anta ce a gabanta da sauri ta bi bayanshi dan arasa jin abinda ya sameshi a can *12:44* na dare ya farka da ambaton Allah a bakinshi, idanunshi da jikinshi sunyi mugun nauyi, da yar ya tashi zaune yana murza dyarshi da ta bugu sosai, lumshe idanu ya sake yi yana tuna abinda ya faru, tun daga kalamanta na farko ya dinga tunawa har kalominta da suka matu ar tsayar da bugun zuciyarshi saboda tashin hankali da firgicin sababi, bai ta a jin imauta ba irin ta yau, bai ta a fuskantar halin ha'ula'i na rayuwa ba sai jiya, maganganun nan na Saleema na arshe da ta ce _"Na ji zan biya bashin, zan biya amma ba anmu ba, dan Allah ka dakata haka."_ Sun matu ar gigita tunaninshi. Jawo hannunshi yayi dake kan eyarshi har ya sauko kan dokin wuyanshi, mugun nauyin da jikinshi yayi ne yasa shi sake komawa ya kwanta yana kallon sama, maganganun sosai suke masa yawo a kai, hakan yasa shi saka duka hannayenshi biyu ya dake kunnuwanshi yana rintse idanu sosai, ya jima a wannan yanayin har hawaye suka fara wanke masa kyakyawar fuskarsa, ba abinda yake iya furtawa sai "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallahu wani'imal wakil!" Su yake maimaitawa har saida dare ya sake tsalawa, kukan da ya ci idanu a rufe ne ya jawo bacci ya sake figarshi ba tare da ya shiga ba. Ko awa aya baiyi ba a baccin nan ya farka a mugun tsorace tare da sakin ara, sai kuma yaui saurin kama bakinshi ganin lallai abinda ya gani a bacci ne ya ganshi ba'a zahiri ba, sam mantawa yayi da ciwon da jikinshi ke masa, firgigit ya sauko daga kan gadon duk ya rikice ya kalli kanshi a madubi yana duddduba jikinshi, sai kuma ya kalli fuskarshi, lallai abinda ka kwanta da tunaninshi ya kan iya zuwa maka a mafarki, gashi an gajeran baccinshi duk ya dameshi da munanan mafarkai. Juyawa yayi da sauri ya fita akin ba tare da ya duba lokaci ba bare ya san arfe nawa, saida ya fito falon daga yadda ya ga shiru ya tabbatar dare ya tsala, sai dai masifar da yake ciki ba zata barshi yayi ha urin zuwa safe ba. akin mahifiyarshi ya arasa yana bubbugawa, ya jima a tsaye kafin ya ji daga ciki tace "Waye?" "Mu'az ne, ni ne Mama." Ya fa a a agauce, da mamaki ta fara kiciniyar bu ofar tana fa in "Mu'az, lafiya yanzu cikin dare?" Tana bu ewa ta kalleshi sosai tace "Jikin ne ya motsa?" Kama hannunta yayi ya maida ita cikin akin hankali tashe tya zaunar da ita bakin gado, kallonshi take da yanayi na tsoro da mamaki, ba tarz daya dami da kallon da take masa ba yace "Mama, tambayarki nake so na yi, dan Allah Mama ki bani amsa karki oye min komai." Girgiza masa kai tayi tace "Tambaya kuma Mu'az? Me zai hana ka bari har da safe to?" A ru e yace "A'a Mama ba zai yiwu ba, Mama rayuwata tana cikin garari wallahi, idan baki bani amsar nan ba zan kasa samun nutsuwa ne." Irin kallo na tsanake ta mishi sannan tace "Ina jinka." aya hannun nata ya kamo yana ta murzawa yace "Mama, da gaske ne zina bashi ce? Idan ka yi da an wasu sai an yi da na ka kaima?" ance idanu tayi alamar mamaki sai kuma tace "Me yasa ka tambaya Mu'az?" Girgiza kai yayi da alamar rashin gaskiya yace "Ba komai, kawai na tambaya ne." Numfashi ta sauke tana kallon fuskarshi da kallo na tuhuma kafin tace "Haka dai aka cewa, kuma a yadda lamarin ke wakana, hakane, bashi ce." Da sauri ya saki hannayenta ya dafe goshinshi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Zunbur ya mi e tsaye ba tare da kuma waiwaye ba ya fice a falon, har mi ewa tayi tana kiran sunanshi amma bai ko juyo ba yadda ka san ma ba dashi take ba, yana fita ofar falon ya bu e bai zame ko ina ba sai angaren Papi, dake dattijon a yanzu ba wani abu daya rage masa da ke masa da i face yayi tsaye a cikin dare sa'ilin da kowa ke bacci shi yana ganawa da ubangiji, Mu'az na buga ofar sau aya ya ji kuma ya salamce dan tunanin farko da ya zo mishi shine wani ba lafiya, saidai yana zuwa bai bu e ba kai tsaye saida ya fara tambayar waye? Da sauri ya bu e jin muryar Mu'az a yanayin da bai ta a ji ba tunda yake a rayuwa. Kallon juna suke kamar wa anda suka rasa bakunan magana ko yaren da zasu fahimci junansu da shi, a karon farko Papi ya numfasa yace "Ina jinka?" Gyara zama Mu'az yayi idanunshi a kakkafe kan dattijon sunyi jajir ga wala data cikasu yace "Papi, da gaske zina bashi ce?" Tar! Tar! Ya kuma dasa mishi idanu yana kallo, ya auki kusan minti biyu a haka kafin ya saddta kanshi asa ya ci gaba da jan carbin hannunshi, a alla sai da ya ja kusan rabin zagaye na talatin da uku kafin ya sake agowa ya kalleshi, cikin dakakkiyar murya yace "Hakane, lafiya?" Jiki a sanyaye ya tashi tsaye yana kallon gaba aya akin, sai kuma ya dur ushe asa ya rarrafa ya matsa kusan Papi ya kama afafunshi, ora goshinshi yayi a kan gwiwar Papi ya fashe da kukan da gabadaya daga zuciyarshi ya fito, cikin kukan mai tsuma zuciya da saka zuciyar mai sauraro karyewa shima ya fashe da kuka yace "Papi na ha ura, na ha ura da ita har abada, ba zan zama silar lalacewar rayuwarta ba, Papi idan na bari ita ko zuri'arta wannan fantin ya shafesu, ban zama adali ba, sannan na zama mai saka alkairi da sharri, Papi ka fa a musu na ha ura, wallahi na barta saboda Allahana." Lumshe idanu Papi yayi ya ja wani dogon numfashi, wata ila wannan shine dalilin tsananta bugawar irjinshi tun safiyar yau, tunda Mu'az in ya tambayeshi kan zina ya san akwai wani abu a asa, dan haka bai yi mamaki ba, saidai jin ya ce ya ha ura ne yasa shi dafa kafa arshi yace "Wacece ka ha ura da ita? Ban gane ba." agowa yayi ya kalleshi yace "Papi Saleema, na ha ura da son aurenta, ba zan gyara kaina sannan ita na cuta mata ba, Papi kai ma ka sani tsakani da Allah ban cancanci Saleema ba, sam ban dace da ita ba." Girgiza masa kai yayi yace "Kada ka yi saurin yanke hukunci, ka tuba ga Allah a kurakurenka na baya, Allah mai gafara ne kuma mai jin ai, sannan Saleema shiriya ce a gareka, kada ka bari wannan damar ta wuceka." Cike da damuwa da shashe ar kuka yace "Papi shine matsalar ai, ta ya ita tana anfanata ta kowane fanni, ni na rasa da me zan saka mata sai na saka zuciyarta ta ani amon zina, Papi ka kusan me ta fa a min yyyyau..." arashe da sake fashewa da kuka, bubbuga irjinshi ya shiga yi yana fa in" Papi Saleema fa ke cexa ita ta yarda za ta biya bashin dana auka, Papi ta ya zan yarda haka ta faru? Saleema!" Sake ora kanshi yayi a afarshi yana kuka, a tausashe Papi ya sake cewa" Kar kayi haka Mu'az, Saleema alkairi ce gareka da gidan nan baki aya, idan ka fasa aurenta ba lallai ka samu mai nagarta kamar ta ba." Da sauri ya ago yace" Dama kuma hakane ya dace da ni, Papi ban san fa adadin matan
Chapter 52 · 0% Book details