← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 116

Sashe 15

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kenan za ta fita Hameeda da ta fi damuwa da abinda ta ga Saleema na yi tace "Ina za ki je?" Juyowa ta yi ta kalleta tace "Gida, sai kun zo." Da mamaki Saleema tace "Gida kuma? Abba fa cewa ya yi..." Cike da raini Hadeeya tace "Ki barta ta tafi mana, ai ta san Abba ya fa a mana zai turo a aukemu bayan kwana biyu, shi ne dan ta rainashi za ta ce za ta tafi yanzu." Dogon tsaki ta ja ta maida hankalinta ga abinda take, Hameeda kuma ci gaba da kallonta tayi har saida ta fita a falon, tana sauka asa Hajia Rabi na fitowa daga madafa, dama kuma ta shiga ne dan orawa Alhaji abinda ya bu ata, ta samu abun kari an gama shiryawa amma ba ta ga Saleema ba, fitowarta dan ta duba akinsu ne sai kuma suka ha Cike da kulawa da kuma fara'a a fuska tace "Yawwa Saleema, na duba ciki ai ban ganki ba, ashe har kin gama girkin? Kai gaskiya Saleema kin yi ari, dama haka kika iya girki?" Hijabin da ta jawo tana ara goge fuskarta yasa Hajia Rabi ganin jakar dake hannunta, da mamaki ta matso kusanta tana fa in" A'a! Saleema ina za ki je da jaka kuma?" Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya da sha iyar murya tace" Mama gida nake so na tafi, ina kewar Mamana ne... " Da sauri ta ri o hannun Hajia tana ci gaba da fa in" Dan Allah Mama kar ki hanani tafiya, ina so na ga Mamana ne." Sosai Hajia ta shiga mamaki da kuma zuba mata ido tana nazarinta da kuma son gano gaskiyar kalamanta, cike da kokonto tace" Saleema, wani abu aka miki ne a gidan da ba ki ji da i ba?" Da sauri ta girgiza kai tace" A'a Mama, ba abinda aka min, nk dai kawai ki barni na tafi." Sakin hannunta tayi ta ara ri e jakarta ta an ra ata tace" Nagode Mama, sai anj..." ota Hajia tayi tace" A'a Saleema, ba zan barki ki tafi ba, ko dai ki fa a min abinda aka miki? Ko kuma na kira Alhaji na fa a masa." Kamar za ta dur usa asa ta shiga gurfanawa tana fa in" Mama, Mama kar ki fa a mana dan Allah, Mamata na ke ji kamar tana cikin wani hali, ki barni na je na duba idan na sameta lafiya sai na dawo." "Ina za ki je?" Alhaji Auwal ya fa a daga bayansu yana fitowa, tare suka kalleshi sai da Saleema ta sauke arfan numfashi, saida ya araso gabansu ya tsaya yana kallon Saleema yace "Ina na ke jin kina cewa za ki tafi?" Tsareshi tayi da ido ta girgiza kai alamar ba komai, kallon Hajia ya yi yace "Me yake faruwa?" Kallon Saleema tayi sannan ta kalleshi tace "Wai gida za ta tafi, na tambayeta me aka mata ta ce ba komai." Kallon Saleema ya yi da ke ta fi i-fi i da ido yace "Me aka miki?" A raunane tace "Ba komai Abba, dama ke war Mama na yi." Wani kallo ya watsa mata kafin yace "Je ki aaje jakar, ba haka mukayi da Abbanki ba, idan kuma kin dage za ki tafi sai na kira na fa a masa." Da sauri tace "A'a Dan Allah, kaa yi ha uri Abba na fasa tafiyar." Hanyar akin ta kama sai kuma ta juyo tace "Amma Abba Mu'a..." Sai kuma ta ga kamar bai kyautu ta fa a musu ba, dan haka ta juya da sauri kawai ta barsu nan tsaye suna binta da kallo har ta shige sannan su ka bar wurin. *Bayan minti 20* Hamdeeya ce ta shigo da sauri akin tace "Saleema wai in ji Abba ki zo." Kallonta tayi kamar ta ce ba za ta zo ba, dan ta fi jin nutsuwa a zaman akin, amma sai ta jinjina kai tace "Ina zuwa." Da gudu Hamdeeya ta fita kafin ta mi e jiki a sanyaye ta auki hijabinta akan riga da siket in da ta saka yanzu bayan ta yi wanka, cikin nutsuwa da dattako ta shiga taka matakalar, ba ta aga kai ta kalli inda ta ji mutanen suke ba, sai dai daga yanda take ji akwai ido sosai dake yawo a jikinta, bata kuma tantance su waye a wurin ba. Saida ta gama sauka sannan ta aga kanta dan ta san inda za ta dosa, fahimtar Alhaji Auwal ya na kan teburin cin abinci ya sa ta nufa can in, tun kafin ta arasa yace "Yawwa zauna." Kanta a sunkuye kamar wacce ta aikata abun kunya ta ja kujerar da ta kula ba kowa a kai ta zauna, hannayenta da suka fito waje sanadiyar hijab in ta mai hannu ta ora akan teburin ta na wasa da yatsunta cike da kunya da ladabi. Hajia Rabi da ke kallonta cike da birgewa da aunar yarinyar tace "Saleema, ki saki jikinki kin ji, ki ci abinci." Sai lokacin ta aga kanta dan kallon Hajiar, sai dai a lokacin ta kula da wa anda ke wurin, Alhaji Auwal ne da amaryarshi, sai Hamdeeya da ita Hajiar da kuma wannan *kuren*, ba ta yarda ta ha a ido da shi ba dan jikinta ya bata kallonta yake, a hankali ta ja farantin gabanta ta auki cokalin ta fara tsakurar abincin. A sace ta kalli Hamdeeya cikin ra a tace "Ina su Hadeeya?" Nuna mata wani akin ta yi dake nan asa tace "Suna akin Yaya Mu'awwaz." Wani irin fa uwar gaba ta ji ya ziyarceta, da sauri ta walalo ido tace "Me suke yi?" e baki ta yi tace "Ni ma ban sani ba." aga idonta tayi da niyyar kallon Alhaji Auwal, sai kuma idonta suka sauka cikin na Mu'az da ya rumgume hannaye ya na kallon duk wani motsinta, shi da ma saboda ita ya tsaya wurin ba dan ya ci abinci ba, wani irin kallo ne ya ke mata ya na jin shi dai kawai birgeshi ta yi lokaci aya ba dan kyanta ko nasabarta ba. Suna ha a ido ya sakar mata murmushi cike da tsokana yace "Za ki ci abincin? Ko na ura miki?" an waro ido tayi da mamakin rashin kunyarshi, sai kuma ta auke kai ta sake kallon Alhaji za ta nemi izininshi, kafin ta yi magana Mu'az ya sake fa in "Abba." "Na'am." Ya fa a yana maida kallonshi ga gareshi, Mu'az kuma Saleema ya urawa ido ba tare da yanayi na wasa a tare da shi ba yace "Na ce ko ka yi wa arka miji ne?" Shi da Hajia Rabi tare suka saki murmushi suna kallon Saleema, inda amarya ta yatsina fuska ta kalli Mu'az in ta na ganin me ye na wannan tambayar? Sam a ganinta bai ma kamata a ce Mu'az ya yi wannan tunanin akan wannan yarinyar ba, dan ta na da labarin rashin iliminta da wayewarta, yatsina baki tayi tana kallon Alhajin da yake fa in "A'a, me ya sa ka tambaya aboki? Ko dai ar ta wa ta sace tsoka ma fi mahimlanci ne a jikinka?" Wata ar dariya yayi ya sunkuyar da kai sai kuma ya ago yace "Ni dai Abba idan ba ka mata miji ba, to ku taimaka min kar na ara zama tuzuru a gidan nan, idan shekarar nan ta wyce ban yi aure ba gallabarku zan yi." Saleema da ta yi mutuwar zaune da ido kawai ta ke binshi kamar wani sabuwar halitta ne ta gani, Alhaji Auwal kuma dariya kawai ya ke sai Hajia Rabi da ta an dakeshi a kafa a tace" Marar kunya kawai, me za ka yi to?" Saleema ya kalla ido cikin ido ba tare da shayin komai ba yace" Ba zan bari ta zama ta kowa ba, zan mayar da ita *mallakina* ko ba ta so." Yanzu kam da ke ranta ya gama aci na takaicin bawan Allahn nan, zabura ta yi ta mi e da sauri ta nufi hanyar madafa, dan gani take idan sama za ta hau za ta jima ba ta kai ba, da kallo duk suka bita har ta acewa ganinsu, cike da izgili da raini amarya ta kalli Mu'az tace "Wannan yarinyar fa ba ajinka ba ce, ba ta da ilimi sannan ga ta auye, ka nemi dai-dai da kai mana." Kallonta yayi irin kallon nan na nidai ban saka bakinki ba, sannan ki min shiru ko ki ji ba da i, ya mata wannan garga in da ido ne dan kar ta hassala shi ya fa a mata magana Abbanshi ya ce ya rainata, dan haka yake so ta masa shiru kawai. Fahimtar kallon yasa ta auke kai ta na sake yatsina baki da tunanin "Ita ina ma za ta yarda Mu'awwaz ya auko mata ajawo irin yarinyar can?" Da haka ma ta yanke shawarar tunkarar lahaifiyar yarinyar da maganar, dan ta san su in amare na musamman ne, idan suka yanke hukuncin to mazan za su ce ya yanku ne kawai. Alhaji Auwal da farin cikin hakan ya kamashi kallon Mu'az ya yi yace" Karka damu aboki, indai da gaske kake ka shirya za mu je wajen mahaifinta sai mu nemo aurenta." Cikin jin da i Mu'az ya ba wa mahaifin na shi hannu suka tafa yana fa in" Yawwa aboki, na ji da i, idan mukayi sa'a ma ya amince nan kawai za ta zauna sai dai na mata lefe da gado." Dungure masa kai Hajia Rabi tayi tace" She ani, wato ba za ka bata damar sallama da iyayenta ba kenan?" Sosa eya yayi yace" Wane sallama kuma Mama bayan ga waya? Ta je daga bayan idan ta gama jego." e baki Hajia tayi da mamaki da kuma kunyar maganar sa, Alhaji Auwal na dariya yace" Abokina da alama yanzu kam ar manuniya ta fara azalzalarka ka yi aure ko?" Bushewa sukayi da dariya shi da Mu'az sai Hajia Rabi da ta mi e tana fa in" Allah ya shiryaku shirin addinin musulunci." *Saleema* kuma na shiga madafa ta samu mai aikin nan tana wanke-wanke, a hankali ta rage saurin da ta shigo da shi na bala'i da gwaramar da bawan can ke ha a mata da bata san dalili ba ta fara takawa har zuwa kusa da ita
Chapter 15 · 0% Book details