← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 116

Sashe 31

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta fita Hadeeya tace "Aunty Saleema ko na baki wayata sai ki saka layin a ciki?" Ba tare da damuwar komai ba ko jin ta yi asarar abu mai tsada ba tace "To ki bani ita duka mana, ke sai ki ri e wannan." A tare suka rakata da idanu a waje Hadeeya har da safe irji tace "Da gaske auntyna? Kin bar min ita duka?" Yatsina fuska tayi tace "To me ye a ciki? Waya ce, dau ar duniya, kina ar uwata na kasa bar miki ita." Da gudu Hadeeya ta sauko a gadon tana fa in "Yeeeeeeee! Auntyna nagode, nagode sosai." Rumgumeta ta yi Hameeda da ba ta ji da in haka ba tunda ba ita aka bar ma ba kauda kai tayi tana aramin tsaki. agowa tayi suka kalli juna Hadeeya ta sake sumbatar kuncin Saleema tace "Nagode auntyna." Murmushi Saleema tayi ta an shafa kuncinta tace "Da ina da irin wayar nan guda dubu, to da na dinga baki ko dan na ji sunan aunty a bakinki tare da ganin auna a tattare dake zuwa gareni, amma hakan ma nagode ma Allah." Cike da kunya Hadeeya ta sunkuyar da kai tace "Ai daga yau aunty zan dinga cewa." Murmushi kawai tayi ta tara mata hannu tace " auko min wayar?" Juyowa tayi ta auki wayar a kan gado ta bata, yo ita fa dama tun ranar ta gama tura komai dake wayarta zuwa wannan wayar saboda ko jiya ta fita da ita ta dinga hura hanci ita a dole wayarta ce, kuma ta tura komai ne saboda sanin da ta ma Saleema ba mai damuwa da irin wannan abubuwan ba ce, a niyyarta da duk sanda za ta fita ta dinga ara tana fita, sai gashi ar aljana kuma *ba auyar* auntynta da ba ta san da in duniya ba ta mallaka mata wayar gaba aya. Tana fitowa daga akin sukayi kici is da mahaifinta ya dawo aukar wani sa o, a ladabce tace "Abba sannu da zuwa." A ta aice ya amsa "Sannu, ina Mamanki?" Nuna masa akinta tayi tace "Tana ciki." Jinjina kai yayi har zai wuce sai kuma yace "Ki gyara min akina, idan kin idar akwai naman talo-talo na nan an kawo ki yi girki da shi, zuwa rana zan turo a auka." Farin cikin sakata aiki da mahaifinta yayi yasa ta sakin wani basaraken murmushi na jin da i, har ya an wuce sai kuma ya juyo ya kalli fuskar, mamakin murmushin me take? Sai kuma ya juya ya ci gaba da tafiya da tunanin me yasa bai ga hushi a fuskarta ba kamar yanda yake gani a fuskar Ardiya idan ya saka aiki musamman idan ta dawo daga aiki ne ko za ta tafi sai ta ga duk ya takura mata kamar yana neman mayar da ita baya ne, saida ya kai farfajiyar gidan ya saki murmushi saboda tuna ai haka mahaifiyarta take ita ma, ba ranar aikinta ba amma kullum cikin hidima take da shi, to idan bai so Safiya ba wa zai so? Bai ta a cewa ta yi ta nuna ba ta so ko ta ji ba da i ba, da ya ce yi to kawai take cewa sannan ya samu abun akan lokaci. Saleema kuma tqabar farin ciki yasa ta aje wayoyin a nan falo ta shige akin mahaifinta ta shiga gyaran ko ina a tsanake, ganin ta jima ba ta shigo bane yasa mahaifiyarta fitowa, wayoyin ta auka da ta gani a kan kujera sannan ta shiga akin na shi a nan ta sameta, ba ta kama mata ba sai ma bata wuri da ta yi ta ci gaba da aikinta, har ta kammala ta koma madafa, da taimakon mai aiki da mahifiyarta dake zaune ta gama wannan girki lokacin tafiyarta makaranta ya yi, dan arfe 02:00 za'a fara saboda aliban na da an yawa, gashi kuma har karfe 03:04 ta na gidan. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:48 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _20_ A gaggauce ta shirya cikin doguwar rigar da Alhaji Auwal ya siya mata da kuma hijabinta pink wanda ya ona ka an, takalman nan ta sako ta auro ni ab ta fito, a falo ta samu Mamanta zaune tana cin salade, arasowa tayi a ladabce tace "Mama na shirya, zan tafi." Cike da nutsuwa ta cire hannunta a salade in ta kalleta tace "To Hajia, a dawo lafiya, Allah bada sa'a, Allah ya taimaka." "Ameen Mama." Ta fa a sai kuma ta yi shiru a nutse tace "Mama, ki yi ha uri." Da mamaki tace "Akan me kuma?" A marairaice tace "Mama zan gabatar da al'amari mai girma da ya shafi rayuwata, amma kuma ke ko Abba ba kwa wajen, haka ma babu aya daga cikin dangina." Murmushi tayi tace "To ai Lubna za ta je, wata ila ma har ta rigaki isa." Turo baki tayi gaba tace "Ni dai Mama ki yi ha uri." ar dariya tayi tace "Saleema, kin kai adamin da ko kin koma wajen ubangiji zai tsayar dake ya tambayeki wajiban da suka hau kanki, indai akan wannan ne karki damu, ki je Allah ya tsare." "Ameen Mama." Ta fa a da fara'a tare da wucewa tana fa in "Sai na dawo." Da fara'a ta bita da kallo tace "A dawo lafiya." Tana zuwa mai gadi ya mi e yana fa in "Hajiar Alhaji fita za'a yi ne?" Ba yabo ba fallasa ta amsa da "E, ba jimawa zan yi ba." *Filin Makaranta* alibai biyu sukayi karatu sai Saleema, kamar yanda kowane alibi na za ar abin da yake son karantawa ne, haka ita ma ta za i in bayani akan girma da darajar iyaye, gaba aya a harshen larabci ne rubutun, tunda ta fara da mu addima malaminsu ya yi sa e yana fatan kar a samu matsala, dan a ganinshi yadda aka bata takardar a urarren lokaci ba lallai ta haddace inda yake da bu ata ba. Amma abun mamaki, sai ga Saleema na karanta takardar nan tamkar balarabiyar da ta sauko daga jirgi kai tsaye ta zarto wurin taron, irin yadda muryarta ke fita da arfi, ga wani sanyi da nutsuwa a cikin muryar ha e da rawar da muryar ke yi na kukan da take na rashin sabo sai ya hakan ya ara ma muryar armashi. Tsaye malamin ya mi e daga kujerarshi jin tana ci gaba da karanta har wajen da ba ya tsammanin ta kai can wajen da ya rubuta. _(Babbar nasarar an adam a rayuwar nan ita ce ya rayu da iyayenshi da kyautatawa, idan har suka shu e ba sa farin ciki da kai, ha a ka yi asarar da kwatankwacinta tamkar rasa iyalinka da duk abin da ka mallaka ne lokaci aya, babu wanda zai gane girman asarar sai mai kyakyawan ahali da manyan kadarori.)_ Ci gaba take yi ba alamar dakatawa, a hankali ya kai hannunshi saman goshinshi har yayi nasarar tunku e hularshi ya mayar da ita baya, bai san sanda sakakken bakinshi ba ya furta masa "Tabarakallahu ahsanul khali in, masha Allah, lahauka wala- uwwata illa billah!" Duk hayaniyar da ta kara e wurin ta dandazon mutane, a hankali ta fara ragewa har aka yi shiru baki aya sai us kawai kake ji yana tashi daga asa, malaman da aka orawa alhakin kiran sunayen alibai da kuma dakatar dasu, tsagwaron larabcin da take yi yasa su mantawa da aikinsu, ba wai yadda take futar da harufan bane abun mamaki, a'a yanda take karantawa babu takarda a hannunta alamar haddaceshi tayi, da kuma sauri-saurin da take yi da ya nuna ya zauna mata a kaine sosai, hakan shi ya fi basu mamaki, a ganinsu ko wata aya daya wuce take haddar nan, iya abin da za ta iya yi kenan. Duk sanda ta ambaci "Ya ku mutane ku ji tsoron Allah, sannan ka da ku ha ashi da kowa, sannan ku kyautatawa iyayenku..." Jinin kowa sai ya sake hauhawa ya tsuma, mafi aksarin mutanen wurin ba sa jin me ake fa a a harshen na larabci, amma daga yadda take yawan anbaton sunan Allah ya tabbatar musu abu mai matu ar mahimmanci ne, a hankali sai aikun mutane suka fara aukar karatunta a wayoyinsu wanda abu ya shiga ransu matu a, duk da akwai masu auka na musamman da makarantar ta tanada har ma da aukar hoto mai motsi, amma hakan bai wadatar ba. Sai da ta kai shafi na biyu sannan aka dakatar da ita tare da mata godiya kamar yanda aka ma sauran, daga ita alibai biyu ne sukayi karatu aka tashi bayan an kira kowane alibi an bashi kyauta, babban abun da ya birge Saleema shine yadda babban limami kuma malamin da yana aya daga cikin malaman da take matu auna da aiki da fatawar da suka bayar ta manyan malamai gabata shine ya bata kyauta. Daga nan suka rabu da Aunty Lubna dan basu son su tafi gidan tare mahaifinta ya yi tunanin wani abun, da sauri ta auki hanyar komawa gida dan magriba ta gabato sosai. A lokacin da kowa ke ta hada-hadar gabatar da sallah, lokacin Saleema ta shigo gidan bayan ta oye duka hannayenta cikin hijabinta sakamakon kyautar littatafai da littafi mai tsarki da take auke da su da kuma envelope in da babban malamin nan ya ora mata a kai da ba ta san me ye ko nawa ne a ciki ba? Tan shigowa farfajiyar ta sake rage saurin tafiyarta sakamakon ganin mahaifinta tsaye a daidai ofar shiga falonsu, ha iyar fuskarshi da kuma hannunshi mai ri e da labceciyar wayar lantarki suka nusar da ita lallai akwai matsala babba. Cak! Ta tsaya tana kallonshi daga nan da idanunta da ke cikin ni ab har sun tara ruwa, da hannu ya mata alama tare da fa in "Zo, zo nan." A hankali ta laluba hannunta ta cire ni in da tunanin ko idan ya ga fuskarta zai ji tausayinta, kamar wacce wai ya fashe a a ciki ta fara takawa zuwa gareshi tana ci gaba da takwaf takwaf da fuskarta. Ikon Allah kafin ta isa gareshi wayarshi tayi ruri, rai
Chapter 31 · 0% Book details