Sashe 62
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jakarta ta sake auka ta ciro wayarta za ta ci gaba da dannawa, tashi Saleema tayi jikinta duk a mace ta kama hanyar fita, tana daf da fita ta aga kai ta kalleta tace" Da na ce zan iya aikata miki komai, ina nufin komai, daga ciki har da salwantar da rayuka, ki kiyaye." Duk da a tsorace Saleema ta girgiza kai saida tace" Wa'iyazubillah! Da fari ina tunanin dalilin da gwamna zai sa ya ce yana sona, amma yanzu na fahimci dalilin, dole yana bu atar tsaftattaciyar soyayyar da ta nin aya a cikin tafarkin addinin islama. " Sai kuma ta saki murmushi tace" Idan Allah yayi shine mijina bana jin akwai mahalukin da ya isa ya dakatar da hakan, amma ki sa ranki a inuwa, matashi ma mai jini a jika ya nemi aurena yanzu zai yi wuya na amince masa bare babban mutum irin wannan, na barki lafiya." Tana fa a ta juya ta fice bata jira ta jie za ta ce ba dan ta ga fuskrta da yanayin mamaki, dan batayi tsammani za ta fa a mata haka ba, amma dai ta ji sanyi sanyi da ta ji alamu na nuna mata cewa ba lallai ta yarda da bu atar da mijin na su ya zo mata da ita ba. *A gurguje*: a gajiye suka dawo gida sukayi wanka tarz da saka kayan bacci suka kwanta, kallonta Safiya tayi tace "Yau dai ki je akinku mana, mahaifinki mita yake wai ina rabaki da an uwanki." Kallonta tayi daga kwance tace "Mama yau kuma? Yaushe rabona da kwana akin? Kayana fa duk suna nan." Tashi tayi zaune ta kalli mahaifiyarta da kyau ganin yadda take gurgurar goro saboda zuciyarta dake tashi, a tsanake ta shiga fa a mata abinda ya faru jiya tsakaninta da gwamna da kula haukan da matarsa ta mata. Da mamakin wannan lamari Safiya tace" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Iklimar? Da wayonta?" e baki Saleema tayi tace" Mama ba wannan ba, ni fa ba son mijinta na ke ba, ta ma daina wahalar da kanta a kaina, dan bai min ba." Kallonta tayi da mamaki tace" Kina nufin ba kya sonshi?" aga kai tayi alamar e, numfashi ta sauke tace" Kin fa awa Abbanki?" an tsorace tace" Mama, shine nake tunanin kar Abba ya zo bai ji da i, ki masa bayani da kanki." Jinjina kai tayi tace" Shikenan, zan fa amasa." Murmushi tayi tace" Yawwa Mama." Komawa tayi ta kwanta tana fa in" Mama yau dai kar ki tasheni fitsari, dan ban sha ruwa ba." Harara ta dalla mata tace" Ai tashin da kike min ne na tsana a rayuwa, a ce idan kina son zuwa akin sai kin tasheni na rakaki? Shiyasa idan na farka kafin ki tasheni ni nake tashinki." Dariya kawai Saleema ke yalawa tana fa in" To Mama cikin daren sai na je ni ka ai? Gwara ina ganin mutum a kusana ya fi." e baki tayi tace" Na ga mijin da zai juri wannan shiriritar, namijin ne yana bacci zai tashi dan rakaki fitsari?" Murmushin gefen la a tayi ta kalleta tace" Zai yi mama, zan sameshi, mai ha uri tamkar Yaya Mu'az." Kallonta tayi tace" Da alama dai Mu'az in nan ba zaki manta da shi ba duk da abinda ya miki." A sanyaye tace" Mama ta ya zan manta lokaci aya? Da sannu zan manta da shi da suk wani abu da ya koyar da ni shi." Da sauri ta gyara kwanciyarta tace" Yawwa Mama, kuma kin gani, jiya hirarmu da gwamna saida na aru da wani abu dangane da shekarun Nana Aisha (R. A), yana da ilimi, ga dattako, ga kirki kuma kyakyawa kamar ba tsoho ba." arashe tana fashewa da dariya, duka Safiya ta kai mata tana fa in" Ke rufe min baki, marar kunya kawai." Dariya ta dinga yi har ta ji bacci na son aukarta, zaune tayi tsakiyar gadon ta aga hannayenta ta shiga karanta addu'o'inta na tsarin jiki kafin ta shafe jikinta ta kalli mamanta tace" Mama cin goron ya isa, ki kurkure bakinki sannan ki ui addu'a mu kwanta." "To." Ta fa a tana mi ewa ta shiga ban aki, dan da wuya darzn da zai zo ya shu e Saleema ba ta tunatar da ita addu' a kafin ta kwanta ba, ko da kuwa a akin mahaifinta za ta kwana ranar, dan haka ar ta zamar mata tamkar awa sannan abokiyar hira da shawara, kuma tana jin da in yadda ita kanta ta auketa awa. Wannan karan dai ya goyi da bayan ra'ayin nata ari bisa ari, tunda Safiya ta shaida masa yadda sukayi da matar gwamnar ya ji gaskiya shi ma hankalinshi bai kwanta ba, dan gaskiya abinda zai ta a masa lafiyar a baya son shi ko kusa, da haka ya saka Alhaji Auwal gaba wajen yi wa gwamnan bayani yadda zai fahimta, kuma ba su oye masa komai ba, da haka dai suka rufe babinshi can su arata shi da matarsa, idan ya ga dama ya auki mataki ko ya yaleta ruwansu. *Bayan Wata aya* Cikin sanyayyar murya aka furta "Jarumi ka fito?" Gabanta ne ya mugun fa i har ta rarako idanu tana kafe ofar ban akin da idanu, a haukace tace "Jarumin uban wa? Wacece ke? Me ya ha aki da mijina?" Dogon tsakin da ya kara e kunnuwanta budurwar ta saki tare da yanke kiran, a gigice ta kalli wayar sannan ta kalli ofar da aka bu o ta ban aki, kafin ya karaso gareta ta isa gunshi ta nuna masa wayar tace" Wace ar iskace ta kiraka a waya take kiranka da jarumi?" Cike da wofantarwa ya kar i wayar yana gyara towel inshi da hannu aya yace" Ban sani ba, me ya kaiki ta amin waya?" A haukace ta sake tarz gabanshi tace" Na ta in, wacece ke kiranka har cikin gida? Tukuna ma ina zaka je?" A fusace ya wanke fuskarta da marin da ya sakata kifawa kan gadon ta fashe da kuka mai sautin gaske, aje wayar yayi gefenta ya nunata da yatsa yace" Ke har kin isa ki tsareni kina min wannan tambayar iskancin? Ni nake aurenki ko ke kike aurena? Fita zan yi kuma baki isa ki hanani ba." Wajen kayanshi ya nufa ita kuma ta mi e da gudu ta fito a akin tana kuka, hakan yasa Hadeeya ta riga Zeid fita a gidan ta zo gidansu dan sanar wa da mahaifiyarta abinda ya mata. A ta aice kwananta biyu gidan, da gangan Zeid ya yi banza da ita bai waiwayeta ba, saida kwanan gidan shi ka ai ya gundireshi, kuma ba damar kawo wata dan mahaifinsa ya saka wanda zai saka masa idanu a kan hakan, dole ya jawo wani abokinshi suka zo biko. *Tunda* suka shigo Saleema ta basu wuri dan ta fahimci magana zasuyi, dan kwanan Hadeeya biyu a gidan ta lura da Ardiya da ke yawan fusata, dan ranar da Hadeeya ta zo ma sosai ta dinga jin bala'inta daga akinta inda kukan Hadeeya ya kara e gidan, gashi kuma Abbansu baya gari bare ya shiga mganar, dan haka Ardiya ita ce ta tarbesu madadin mahaifinsu. Cike da gajiyawa da surutun matar Zeid ya sunkuyar da kanshi yana ayyana "Jaraba, ba dai surutu ba." Abokin na shi kuma lalla ata yake shi ma har kansa ya fara ciwo, wai sai wani daddagewa take a kan me zai marar mata a? Jaka ce ta kai masa? To kar a sake? Kuma kada ya saki ya wula anta mata a ta hanyar ha ata da wasu a waje, da yar dai wannan mita ta mutu ta ce zasu iya tafiya gobe ta turata ta koma da masu rakata, da haka aka samu wannan wutar ta mutu. Sai dai abunda bata sani ba wannan ne Hadeeyar ta fa a da ya kai ga ta a lafiyar jikinta, amma kira a wayarsa na an mata ya fi a irga wanda take kamawa, baya ga lokacin tana amarya an matan da suka dinga zuwa da sunan danginsa ne, amma daga arshe ta gane basu da wata ala a ta jini kawar arya ce, ga matsalarshi ta cika daren sababi, wani lokaci yana shigowa sai sallah subah, ranar da ya zauna gidan kuma wuni cur yake da waya a hannu yana kakkauce mata, ko gilmawa ta zo yi ta bayanshi sai ya oye waya dan baya son ta ga abinda ya ke a wayar. *In dai da comment to da aiki.* *Alhamdulillah.* 13/06/2022 17:25 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _35_ Gaba aya hankalin Alhaji Yusuf ya koma kan wannan ciki na Safiya, tunda cikin ya wuce wata biyar suka sake du ufa da addu'a da kum sakawa ana tayasu, yanzu gashi cikin ikon ubangiji har ya shiga wata na bakwai, hakan ba aramin da i ya masa ba, yara an koma makaranta amma har yau bai ce komai game da komawar Saleema makaranta ba, dan haka ita ma ba ta ce za ta koma ba ta zuba masa idanu. Yanzu haka shirin aikin Hadj yake, dan haka ma yake ta kwatantawa Saleema cewa ta kula da Mamanta, kar ta bari ta yi aikin komai a gidan nan, Safiya tun tana jin da in hakan har ta fara tqarguwa, dan gani take kamar idanun kowa a kanta suke, saboda rawar afarshi tayi yawa, tamkar fa wanda bai ta a samun haihuwar ba yake yi, dan haka fatanta bai wuce Allah ya sauketa lafiya ba, dan kuwa ita ka ai ta san irin laukayin da take sha a kan wannan ciki, ko dan ta jima bata samu bane? Ko kuma dan yanzun ta fi sanin ciwon kanta da zafin jikinta? Ba kamar haihuwar Saleema da akayi da uruciya sosai ba, wanda hakanne ma yasa ita da ita tamkar awaye, bare ma da ita in ta zama marar jiki sosai, sai suka zama tamkar wasu an tsara. Kusan komai zai faru a rayuwa to da dalilin faruwarshi, Saleema ta ha ura da maganar inki tunda har ta sha dukan mutuwa a kan shi, dan haka ta tattara komai ta watsar