Sashe 112
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta maimaita" Fadar shugaban asa?" Rusunawa ya sake yi yace" E ranki shi da A hankali ta mi a hannunta ta kar i wayar tana tunanin anya kuwa? Wa zai kirata a fadar nan ita kam? Wa ta sani a wurin? ora wayar tayi a kunne a nutse tace" Assalama alaikum." asa asa ta ji an ce" Gata ranki shi da e, ta amsa." Cikin sanyayyar muryar dattako aka ce" Assalama alaiki." Duburburcewa Saleema ta nemi yi daga zaunen nan ta furta" Wa... Amm, ina wuni." A nutse ta amsa da" Lafiya lau, gimbiya Saleemat." Shiru tayi tana rarraba idanu ta rasa me za ta ce, cikin kamilalliyar murya matar tace" A gafarceni, na kira kai tsaye, sunana Hajia Balaraba Seini, mun yi waya da anwata Mardiya, shine take fa a min ta je bata sameki gida ba, ko anwarki ne ba lafiya." Shiru tayi da alamar ta gama magana kenan, da sauri Saleema ta kalli ahalin nata ta dinga musu alama da yatsa cewa su yi shiru, a nutse ita ma duk da ana gane tayi kuka tace" Hakane ranki shi da anwata ce ba lafiya, amma yanzu jikin mahaifinmu ya fi tsananta kan nata." Cike da kulawa ta amsa mata da" Subhanallah! Me ya sameshi?" Danne kukanta tayi ta sadda kanta tace" Yankar jiki yayi ya fa i, kuma likitocin sun ce a kaishi babbar asibitin Niamey nan da sa'a takwas, idan ba haka ba zai iya shiga doguwar suma." Da nuna damuwa sosai tace "Subhanallah! Haka abun ke neman yin amari? To yanzu wane mataki kuka auka? Ko na ce me kuke shirin yi?" A lasabce Saleema tace "Ranki shi da e dole a jirgi ne za'a fitar dashi a kan lokaci, to kuma tsare tsaren da an tsauri ta yadd..." A nutse ta katseta da "Uhum! Na gane, karki damu gimbiya Saleema, ni dama na kira ne dan mu gaisa akan jikin anwarki..." Numfasawa tayi tace "Ba zai gagara ba, ku gama shirinku tsaf, akwai jiragen sojoji da suka fi sauri gurin bayar da taimakon gaggawa, nan da awa aya za'a auko mahaifinku in sha Allah." Tsaye Saleema ta mi e tana hawaye tace "Alhamdulillah, nagode ranki shi da e, ha a..." Da murmushi mai sauti ta katseta da "Ba wannan lokacin gimbiya, ke dai ku shirya tafiya kawai, sai anjima." Tana aje wayar ta sauke nauyayyar ajiyar zuciyanta koma ta zauna tana lumshe idanu, dafa kafa arta Safiya tayi tace "Ya dai?" A hankali ta bu e idanunta ta kalleta tace "Mama Hajia Balaraba ce, matar shugaban asarmu ta kirani." A mugun zabure Ardiya dake zaune dirshen a asa ta zaburo tsaye tana fa in "Da gaske? Hajia Balaraba fa?" Kallonta Saleema tayi da rashin gane me take nufi tace "E, aunty ita." Matsowa ta sake yi har tana neman ran wafawa durkushe tace "Ita ce ta kiraki? Dama kina da lambarta?" Da mamaki duk suka kalleta Saleema tace "E, ita dai ta kirani." "A ina kuka san juna?" Ta fa a tana dur usawa gaban Saleema dan ita mamakin abun ne ke neman gagara aukar hankalinta, Hajia Balarabar da ta ji Iklima ma dake matar gwamna na kukan ta kasa samun kusanci da ita, har ungiya da Hajia Balarabar ta bu e Iklima ke jagoranta sai ta hannun sakatariyarta suke magana, amma ita da Iklima baki da baki basu ta a magana ba. Ganin kamar Ardiya maganar wayar ce a gabanta yasa ta kalli Hadeeya dake tsaye tana ma Ardiyar wani kallo mai kama da harara yasa ta cewa "Hadeeya, Hajia ta ce nan da awa aya za ta turo mana da jirgin sojoji ya auki Abba..." Sai kula ta kalli Safiya da ita ma ke mamaki tace "Mama, ku fitar da wanda zasu tafi tare da Abba." Hadeeya ce tayi saurin cewa "Aunty ba gaki ba, ku je tare mana." A sanyaye ta girgiza kai tana murmushi tace "Hadeeya ba zan iya ba, kuma kinga ma nan in da na zo babu izininshi, Ummi ce ta ce na zo za ta fa a mishi dan bana samunshi a waya." Safiya ce tace "Gaskiya ne, ba ma za kunje ba ku, ni zan je tare da shi, a can kuma ba zamu rasa mai taimaka mana ba, tunda Yayan mahaifinku a can yake dama." Karaf! Ardiya tace "A'a ni zanje, zan tafi tare da shi." Kallonta sukayi kafin Safiya tace "Hamdeeyar fa dake kwance?" Murmushi tayi tace "Ba gaki ba? Ke ma ai uwarta ce, nasan zaki kula da ita." Jinjina kai Safiya tayi tace "Hakane, shikenan to Allah ya bashi lafiya." Wayar Saleema ce tayi ara yar aramar, tana dubawa ta ga Abdus-samad ne, da sauri ta mi e irin na masu ciki take takawa da sauri ta nufi hanyar sauka daga matakalar, Ardiya na ganin haka ta ja Hadeeya gefe tana mata ra a tace" Tsakani da Allah kina ganin gaskiya ta fa a Hajia Balaraba ce ta kirata?" Da mamaki Hadeeya ta kalleta tace" Kina ganin arya za ta yi? Ita fa ke musu inki tare da anwarta Mardiya." Rarako idanu tayi tace" Tsakani da Allah? inki fa? Yanzu tun daga can suke turowa har nan?" Wani kallo Hadeeya ta mata tace" Momma, ke baki san wacece Saleema ba a yanzu ko? Ba ki san irin alfarmar da inkin nan ke mata ba ko? Zaki gani to a gaba." Jinjina kai Ardiya ta dinga yi tana tunanin inki fa? inki? Anya kuwa? To indai hakane ko inkin za ta zubawa Hamdeeya ku i ta koya? Kai wace Hamdeeya kuma yanzu da ba ta san ma za ta rayu ba, ko dai ita za ta koya da kanta? Da wannan tunanin har ta tafi gida dan shiryawa da kuma auko abinda zasu bu ata a tafiyar tasu. *Alhamdulillah.* 02/07/2022 10:42 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _59_ *Kwanansu biyu* da tafiya yau, Safiya na zaune tana yankawa Hamdeeya lemu ta kalleta cike da tausayawa, ta rame fuskarta duk ta fa a sai farin fatt tamkar bata da jini, ajiyar zuciya ta sauke cikin nutsuwa da jan yaro a jiki tace "Autar mata, zamu iya yin magana dake?" A hankali ta kalli Safiya da idanunta da sukayi fari sosai ta aga mata kai alamar e, ci gaba tayi da yanka lemun tana orawa a faranti arami tace "Hamdeeya, me ya kaiki aikata wannan kuskuren? Garin yaya haka ta faru? Shin kuwa kinsan ke in macece mai daraja? Sannan shekarunki basu kai aukar wannan wa i'ar ba, sannan me yasa ba ki yi duba da an uwanki ba? Har suka shiga gidan majazansu ba wacce haka ta faru da ita." Juyar da kanta tayi tana kallon tagar dake kusa da gadon da take kwance a kai ba ta da alamar za ta yi magana, cikin nutsiwa Safiya ta ora da " addararki ce, bawa kuma baya wuce addararsa mai kyau ko marar kyau, ki tuba zuwa ga Allah zai yafe miki idan ya so, sannan ki guji sake aikata irin laifin da kika aikata, Hamdeeya alfasha ba kyau ga namiji ma bare mace, muninta ya fi fitowa arara idan mace ta aikata ta, kinga har yanzu ke yarinya ce, kina da damar sake rayuwarki ki kuma ingantata..." Numfasawa tayi tace" Kinga yanzu dalilin abinda kika aikata mahaifinki na kwance, Alhamdulillah tunda jikinshi an ce da sauki sosai, ki misalta da a ce fa uwar da mahaifinki yayi fa uwa ce ta har abada, da ya za ki yi? Ga laifin zina, ga laifin kisan kai, sannan ga laifin zama silar rasuwar mahaifinki...sannan mu ma da mun kalleki da laifin da ke kika zama silar zubewar bangon da muke jingina.." Wani irin kuka Hamdeeya ta fashe da shi tare da juyowa da sauri ta ora kanta a cinyar Safiya, hakan yasa Safiya aje farantin da wu ar ta shiga dadda ata amma kuma ita ma kukan take, cikin kuka Hamdeeya ta fara fa in" Aunty ya zanyi? Abba ne duk arina sai ya nuna banyi ba saboda ban zo ta fari ba, wata rana da aka bamu sakamo na sake zuwa ta uku sai na ke ta kuka na fa awa malaminmu cewa Abbana zai min fa a, shine shi kuma malamin ya ce zai taimaka min amma sai na bashi hadin kai, ni aunty ban san komai ba a lokacin haka ya dinga min wasu abubuwa har ranar da ya min mai zafi, shine ya ce kar na fa awa kowa." Girgiza kai Safiya ta dinga yi tace" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Wannan wace irin boko ce? Bokon da za ta salwantar da mutumcin anmu?" Girgiza kai ta sake tace" Amma ya akayi kika zubar da cikin nan? Mamanki bata gane bane?" Girgiza kai tayi tana shashe a tace" Ba ta gane ba, nima ban san ina da ba shine ya dinga min wasu tambayoyi har ya gane, shine ranar a makaranta ya bani magani ya ce na sha, tunda na sha na ji bana jin dadin jikina har na zo gida." Hankalinta ne ya ara tashi, zuciyarta ta tunbatsa da acin rai, tabbas yau da gaban Ardiya take da sai ta kifeta da mari ba ko shakka, dan babu ta yadda za'a yi ta yarda ita uwa ce alhalin arta na auke da ciki ta kasa ganewa, ba wannan ne abun damuwar ba yadda ta dage ita za ta tafi tare da mijinsu alhalin arta na bu atar kulawarta, amma ba ta damu ba haka ta kwasa ta bisu saboda wani dalili na ta, dan ita ta san ba haka kawai za ta yarda ta tafi ba tunda ta ji tana ta ma Saleema wasu tambayoyi game da Hajia Balaraba. _______________ Da sauri ta aga wayar tana washe baki da cewa "Hajiar Abbanta, kina lafiya?" Daga wajen Saleema ta amsa da "Lafiya lau Aunty, ya jikin Abba?" Saida ta kalli Alhaji Yusuf dake kwance yana kallon aya angaren suna magana asa asa da Yayanshi sannan tace "Mai jiki gashi nan dai, yanzu haka ma saida aka ara rubuta mana takrdar siyan magani, zan ma fita in siyo ne