← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 116

Sashe 44

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shashashan kallon ya watsa mishi yace" Na auka kai ka fa a min ka samu sabuwar ar shilar da za ta rage maka zafi." Cike da rashin gaskiya yace" Hakane na fa a, amma kafin na fa son Saleema ne, yanzu babu wannan tunanin a raina game da ita, ka yarda dani abokina." Iska Zeid ya huro daga bakinshi yace" Ba maganar yarda tsakanina da kai Mu'az, yanzu fa a min me yasa ka kirani?" A take yace" Ha uri nake so ka bata, ka fa a mata wallahi ba abinda take tunani bane, kuma yanzu ma haka na ma Hadeeya kashedi za ta fita harkata." Da wani kallon tuhuma ya kalleshi yace" Za ka daina kiranta kenan?" Matse fuska yayi yace" Ni fa dama ba ni ke kiranta ba, ita ke yawan takura min da kira." "Sai ka ke agawa ko? Duk da kasan maganar aure ce tsakaninka da Yayarta." Ya fa a yana kallonshi, da alamar saranda ya aga hannaye yace "Na ji kuma na auki laifina, amma dan Allah ka je ka bata ha uri komai ya wuce." Girgiza masa kai yayi yace "Mu'az ba zaka iya da rigimar yarinyar nan ba, ka san matsalar auran mace ar islamiyya?" ura mishi idanu Mu'az yayi da alama arin bayani yake nema, orawa yayi da "Haka za ta dinga gwara maka kai kamar wani anta, su fa irin yaran nan komai a gurinsu ba daidai ba ne, kowane motsinka sai ta nuna maka ai ba kyau Allah ya hana, kaza haramun ne kaza haramun ne, ga takurar tsiya da na cin sababi musamman kan abinda ya shafi addini, ka ga ka auri] ar islamiyyar nan? Wallahi ka daina baccin asuba kenan saboda saita tilasta maka bin jam'i, ga su da ganin kowa an wuta, haka kawai za ta ga komai ba daidai ka ke yi sai yadda take yi ne daidai." Tsaf! Ya zuba masa idanu har ya gama maganarsa, numfasawa Mu'az yayi yana murmushi yace" Gaba da gabanta, duk lalacewata ka fini iskancewa, tunda ni ina son na daina duk abinda na ke, hakanne ma ya sa na ke son auren wacce take da ilimin addini, maganar tashi sallah asuba kuma ai tun zuwanta gidanmu ta koya min, yanzu haka daga waccen ranar da ta je zuwa yanzu ban ta a rasa jam'i a kowace sallah ba." Kallonshi yayi sosai yace" *Zeidul-Abidin*, mun samu rayuwar nan ba da wayo ko dabararmu ba, kar mu yi saken zuwa lahira babu guzuri, dan hakan shine asara ma fi girma da zamu tafka, mutuwar nan dai ba sallama take wa mutum ba, sannan ba ta turo sa on kar ta kwana, to idan dai mutuwa za ta zo mana bagatatan a halin da muke ciki yanzu, da wane ido zamu kalli ubangijinmu, wanda Saleema ta fa a min cewa kowane yaro yana zuwa duniya ne da al awarin da ya auko tsakaninshi da ubangiji kan ba zai ta a ha ashi da kowa ba, sannan zai bauta masa iya iyawarsa, ka ga haka...?" Ya fa a yana nuna masa dun ulallen hannunshi na dama sannan yace" Ta ce min dalilin da yasa kowane jariri ke zuwa da dun ulallen hannu kenan, wannan al awarin da ya auko ma mahaliccinsa, amma awanni ka an, kwana ka an sai ka samu jaririn da bai san waye shi ba ya saki hannunsa saboda kawai ya sha i iskar duniya, da haka zai ci gaba da mantawa da wannan al awarin, abinda zai sa ka tuawa kuma shine zama a gaban masu ilimin da zasu sake tunatar da kai wannan al awarin, idan har muka bi ta son zuciyarmu Zeid, ina ga ba anfanin zamanmu muna amsa sunan musulmi, kawai mu koma maguzanci zai fi dacewa da mu." Shi ma Zeid zuba mishi idanu yayi har saida ya gama, dan gaskiya abinda ya fa a gaskiya ne kuma ya ratsa zuciyarsa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da murmusawa yace "Gaskiya nima ar islamiyyar nan zan nema, gashi lokaci aya har ta mayar da kai sheikh Mu'az." Harara ya watsa mishi yace "Kai fa an iskane." Shi ma hararanshi yayi yace "Na kaika ne?" Girgiza kai yayi yace "Na ji yanzu zan shiga har ciki na bata ha uri, amma Mu'az dan Allah dan girman Alla kaaa fita harkar anwarta." Cike da tabbaci yace "Na daina wallahi, kuma ba zan sake kulata ba." Jinjina kai yayi yacce "Allah yasa, dan gaskiya ni tsoro ka ke bani, kuma tunda ka fa a min tsarinka a kansu na ji dama hankalina bai kwanta ba, dole dama a samu irin haka." Cike da jin haushi yace "Na ce na daina ko? Ni dai yanzu ka shiryani da ita dan Allah." e murfin motar yayi ya fita ya tunkari shiga gidan, haka ya dinga kutsa an mata da samarin da har yanzu ra ashewa ce a gabansu har saida ya isa ofar shiga babban falon ya dakata, su Ardiya dake zaune nan wajen ya gaishe da su a mutumce suka amsa, dake bata san shi ba ko da ya tambayeta Saleema ta kalleshi daga sama har asa, a ranta ta ayyana "Kaiii!" A ganinta me ye tsakaninshi da Saleema, irin shaddar dake jikinshi mai aramin inki, gashi kyakyawa dukda duhun fatarshi, abu ga dogo ga iya aukar wanka, sai kawai ta sakar masa murmushi tace "Ko dai kaine surikin na mu?" Cike da kunya ya girgiza kai yace "A'a, ni abokin Mu'az ne, na zo bata sa o ne." e fuska tayi ta galla masa guntuwar harara ta asan idanu ta nuna masa tace "Shiga tana ciki." Shiga yayi da mamakin ita kuma matar nan me ke damunta? Ta ya za'a ce ba ta san Mu'az ba da maganar dake tsakaninsu da Saleema? Sa'ar da ya ci ta ha ewa da Hamdeeya ya saka ta kirawo masa Saleema dake akinsu kwance, sai dai ta daina kuka yanzu saboda bata son Mamanta ta fahimci wani abu. Hijab inta ta sako dan bata san ko wanene ba, hasalima ba'a ta a mata irin wannan kiran ba, a falon ta same shi zaune kan kujera duk da ana shige da fice tsakanin falon da akin Ardiya, kujerar nesa da shi ta zauna tana an sakin fuskarta saboda ta sanshi lokacin bikin Mu'awwaz sun ha u, cike da girmama juna suka gaisa kafin ya fara da abinda ya kawoshi, cikin nutsuwa ya gyara zamanshi yace "Saleema, abokina ya fa a min abinda ya faru azun, ya shiga damuwa sosai da tashin hankali, har yanzu yana waje bai bar nan ba, shine na ce bari na zo na baki ha uri, sannan na fa a miki ba abinda kike tunani bane, ba komai tsakaninshi da anwarki sai mutumci da girmamawa, ina fatan za ki fahimceni sannan ki yafe masa?" Da mamaki da kuma shanye damuwarta tace" To! Na fa a masa ina hushi da shi ne? Ni ai ban auka da zafi haka ba, kuma ya min bayani na fahimta, ba komai." Da kallon tuhuma ya bita yace" Kin tabbata ba komai?" Da tabbaci tace" Na tabbata, har zuciyata nake fa a maka haka." Da sigar zolaya yace" Kenan yanzu zai iya turowa mu aura muku aure mu huta da irin wannan ananen matsalolin?" Cike da kunya ta sinne kanta ta rufe fuska da hijabi, murmushi yayi cike da jin yarinyar ta birgeshi saboda kunya ya sake cewa "Kenan baki ha ura ba har yanzu?" Da sauri ta girgiza kai tace "A'a wallahi na ha ura." ewa yayi tsaye yace "To indai hakane mu je yana jiranki a waje." Zaro idanu tayi tace "Yanzu kuma?" Da mamaki yace "E, me ye to?" Shiru tayi tana tunani a ranta, katseta yayi da fa in "In dai ba ki je ba zan sameshi na fa a masa kin i ha ura ya zo da kanshi har akin ya sameki." Da sauri ta mi e tsaye tana fa in "To shikenan zan je." Gaba ya yi ita kuma tana binshi a baya har suka fita daga gidan, yana ganinsu ya fito da zumu i yana washe mata baki, saida ya araso ta tsaya ya ara gyara tsayuwarshi yace "Babyyy, kin yafe min?" Sadda kanta tayi asa ba ta ce komai ba, sake matsowa yayi daf da ita ya marairaice yace "Matata, ki yafewa mijinki mana, ba zan ara ba." Cikin kunya ta ago ta kalleshi tace "Ni fa dama ba hushi na yi ba." a fuskarta yayi yace "In dai hakane to ki min murmushi ko na ji sanyi a raina." Numfashi ta sauke kafin ta an murmusa, dafe irjinshi yayi yana kallonta yace "Na ji da i Baby, kuma dan Allah kada ki ara irin hushin nan dani, zan iya mutuwa fa." ar dariya kawai tayi ba tace komai ba, a hankali ya dinga jan ta da hira tana an amsa mishi sama sama, dan a takure take jinta duba da basu ta a tsayawa a nan ba, sai take ganin duk wanda ya wyce kallonsu yake, sun kai minti sha biyar kafin ya mata sallama zuciyarshi fes na farin cikin ba zata kwana da acin ranshi ba ya bar gidan. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:49 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _27_ an nesa da shi ta zauna kanta a asa tana jin yana rufe jaridar dake gabanshi, gilashin dake idanunshi ya cire ya aje kafin ya sake maida hankalinshi kanta yace "Ina jinki?" Saida ta ara sinne kai tana arfafa kanta cikin nutsuwa tace "Abba, dama...da...dama ina zan fara koyon inki ne, dan Allah Abba ka barni na fara?" ura mata idanu yayi na tsawon lokaci, sai kuma ya numfasa tare da mi ewa ya auki makullenshi da wayarshi ya nufi hanyar ficewa a akin yana fa in "Bana son sake jin maganar inkin nan a bakinki, idan ba haka zan ata miki rai fiye da tunaninki." Da sauri ta juya ta bishi da kallo ta ofar baya da zai fita tace "Abba dan Allah?" Cak! Ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, ance idanu yayi ya nunota da yatsa yace "Saleema rainani kikayi kenan? Dan kinga
Chapter 44 · 0% Book details