Sashe 77
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace "To su *wanene* kenan?" *Da* wani mugun sauri wayar hannunta ta su uce mata ba tare da saninta ba sanda mutane hu un dake tsaye kan mutanen dake zaune akan tabarmi suka cera da wani irin ki a na sautin sarewar daya kara e gidan a anin lokaci, busa ce irin ta gidan sarki mai mara awa, busa suke kamar masu son tashin dabbobin dake bacci. Bata damu da wayar ba haka ta sake zura kanta tana hangen masu busar, da gudu Gaishata ta taso tana fa in "Busar me a ke?" Matsa mata tayi suka le a ta tagar, daga sama sama suka fara jin abun kafin ya fara shigo unan kawunansu har suka fara fahimtar abinsa san- iran nan yake aga murya da iya arfinshi yana fa in "Masha Allahu, Alhamdulillah, Allah ya kawomu lokaci ya riskemu, a wannan rana ta asabar da ta shiga tarihin masarautar mara awa, aure ya auru tsakanin an sarki jikan sarki mahaifi ga sarki in sha Allah *sarki Abdus-samad Abdallah Wazir* uban marayu, gatan marar uwa, babanmu mai share kukanmu, Allah ya ja zamanin sabon sarki mai gadon mai mara awa, tare da * ar baiwa* yarinya mai ashin arzi i wacce ba ta duniyar sanda aka yi rabon tsiya, wato *sabuwar gimbiyarmu* uwa mabada mama amarya ga sarkinmu mai adalci *Haleematus-sadiya Yusuf Jiji*, aure ya auru akan sadaki ka an domin samun albarkar aure." Muguwar sarawa kanta yayi, ba ta da hawan jini a iya saninta, amma dai yau ta tabbatar ya kamata a nan takedan kuwa jiri ne ya ebeta ya kifar a asa har ta kaiwa Gaishata karon da ita ma tayi tangal tangal za ta fa i, da sauri Gaishata ta dur usa tana kiran sunanta, idanunta a bu e kuma tana yabtawa saidai kamar ba ta hayyacinta ba, tallabota Gaishata tayi ta tashi zaune suna kallon juna. Har yau ba'a daina busar sarewar nan ba, inda hayaniya ta aru har suke iya jiyo maganganun maza a falonsu, tagumi Gaishata ta buga ta jingina a bango tace "Wai me hakan yake nufi? Anya kuwa gaskiya ne?" Wuri aya ta kafe da idanuwa tana kallo, sam bata hayyacinta bare ta san me take, a da ile tace "Gaskiya ne, gaskiya ne muka ji!" Kallonta Gaishata tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Yanzu kenan duk wahalarmu ta tashi a banza? Ta auri wanda ya shallake tunaninmu kenan?" ufule Ardiya tace "Haka ya nuna, na ce haka ya nuna." Zunbur ta tashi tsaye tana matse fuskarta saboda jikinta da yaji ya auki ciwon fa uwar nan da tayi a asa, sa hanzari ta kama hanyar fita a falon hankali tashe, da sauri Gaishata ta bi bayanta har tana sakin gyalenta asa. A falon suka samu wasu daga cikin dangin mijin nasu suna ma Safiya barka wacce ita kanta zulumin hakan ne yasa ta bin kowa da idanu kawai, ita ma kamar a mafarki ta ji ana shelantawa arta Saleema ta auri sarki, sarki? Ba fa an sarki a ka ce ba, sarki gaba aya? Wuri Ardiya ta samu ta zauna saboda juyowa kanta da sukayi suna mata barka, murmushi nan ta saki mai kama da kuka gaya ta amsa da "Uhum! Barkanmu." Shigowar Alhaji Yusuf ta saka ta zuba masa idanu da takaici kamar ta sha i wuyanshi ta kashe, yo ita zai yaudara haka? Ita zai ma rufa-rufa a rayuwar nan? Babbar rigarshi ya sa a bakinshi har kunne ya arasa inda Safiya take, cikin ra a yace" Uwar Hajia, yanzu an daina hushin? arki fa yanzu *gimbiyar mara awa* ce." Maganar nan ce ta sakata fashewa da kuka tare da tashi zunbur ta juya ta kalli gabas a daidai inda Ardiya da Gaishata ke zaune, sujadar godiya ta yi ga Allah tana yi tana kuka kafin ta aga hannayenta sama tace" Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah Alhamdulillah, nagode maka da wannan babbar ni'ima, Allah nagode maka da ka nunawa ma iya da mahassada arshensu." Kamo kafa unta Alhaji Yusuf yayi yana murmushi, Ardiya dake kallon Safiya idanunta a tsatsaye tamkar na mayyar da aka kama, wani gumi ya shiga wanke mata fuska tana kallon Safiyar kamar wacce aka firgita, cikin ra a Alhaji Yusuf ya kalli Safiyar yace" Yanzu fa ar babbar mace ce, ki gana da ita na arshe, da sallah isha'i masu tafiya da ita zasu zo." Kallon Ardiya yayi yace" Madame, dan Allah ki kula da komai, zan sa a kawo muku nama da za'ayi girki na musamman saboda ba i masu zuwa, mu zamu wuce fada ne yanzu dan kai gaisuwa ga sarki, kinsan yanzu aka yi na in." ufule, a hassale, rai ace, cike da guguwar hassada da yashi ta rarako idanu tace" Ni ce m..." Sai kuma tayi shiru saboda duk mutanen falon uta suka kalla, bata so kuma a gane bata jin da in lamarin nan ba, dan haka ta yale kawai ta sadda kanta har ya fita a falon tare da takewar bayan an uwanshi. ______________ A matu ar rikice uwar-gidan tsaka ta zazzaro idanunta tana kallon kanta a madubin da wayar dake kunnenta tace " an-galadima wannan wane irin abu ne? Me ye haka? Ya za'ayi na i ba wanda ya sani sai kawai mu ji busar sarewar dake nuna mara awa tayi sabon sarki?" A matu ar gigice ya cire rawanin kanshi ya jefar cikin tashin hankali yace "Ranki shi da e ba iya na i akayi ba, harda fa aure aka aura masa, aure? Abdus-samad in?" Ita ma maimaitawa tayi a razane da "Aure? Abdus-samad in? Amma ta ya haka... Wai kai kana ina duk haka ta faru?" Wawan tsaki yayi sai kuma ya dafe gaban goshinshi dake sara mishi yace "Ranki shi da e me ye abunyi yanzu? Ni fa malamin nan ya tabbatar min da babu ta yadda Abdus-samad zai yarda ya auri wata mace, ta ya yanzu za'a aura masa aure da wata? Wacece ma ita?" A dake ta amsa da "Ni zan gano wacece ita, kai ka koma wajen malam ka sanar dashi abinda ke faruwa, idan zai yiwu kar ta shigo gidan, idan kuma har ta shigo to kar ta rayu, kuma a yi aiki da ilimi yadda babu wanda zai zargi mutuwar daga wani mahaluki ne." Jinjina kai yayi a sanyaye yace" Angama ranki shi da Cike da siga ta mugunta ta sake sanyaya muryarta sosai tace" angaladima, kada ka yi sanya kan lamarin nan, mu fara ji da yarinyar da har aikinmu baiyi tasiri akanta ba wajen hanata amincewa aurensa, daga baya zan san ta inda zamu ullowa lamarin har mu cimma nasara, a wannan karan na maka al awarin zama sarki ko ta wane hali, dama na tsaya maka ne har aka baka ri waryar mulkin nan saboda ina so ka ri eshi na wani lokaci har sanda ana zasu kai munzalin, amma yanzu..." Ta kalli kanta a madubi sannan tace" Ka yi abinda na ce kawai." Jinjina kai yayi yace" Shikenan." Da haka sukayi sallama ta aje wayar tare da ara gyara jikinta ta auki babbar alkyabbarta ta saka sannan ta fita a akin baccin na ta. Abinda dama take gudu ne yake faruwa, dan kuwa mutane ta samu akin duk ba hayanuya suke ba, arara alamu suke nuna yanzu fa ta fisu matsayi kenan, tunda anta ne sarkin, gashi dai ta shigo amma hadimai ne suka iya gaisheta da wannan girman da take burin ganin ya ci gaba da wanzuwa har abada. Zaune tayi kusa da gimbiya Ramlat dake kar an gaisuwar matan liman da suka shigo, ba su gama gaisawa ba wata hadimar ta shigo da girmamawa ta zube asa tace "Ranki shi da e, yalla ai gwamna ne da tawagarsu suke neman iso dan tayaki murna, mai martaba ne ya basu damar haka." A sanyaye da sakin fuska tace "Ba matsala, za su iya shigowa." Jakadiyarta ta kalla hakan yasa ta mi ewa tana fadawa matan. Dake nan cewa su zo ta nan, ta wata hanyar ta fitar da su daga falon Gimbiyar na kallon wannan ikon Allah yadda aka maidata kamar hoto. Tana zaune suka shigo tana ganin irin gaisuwar da ake mata, sosai ta cika tamkar za ta fashe, sai dai tayi murmushin ya e kawai dan kar a ganeta, sai gashi sun kasa gaisawa a tsanake bare ta mata murna har ta san wacece yarinyar da ta kutso kai a daidai lokacin nan ta tayar musu da hankali, dole ta koma anga renta ba tare da sanin haka ba, saidai ta yi niyya za ta sani dan kuwa da ita za aje daukarta dan ta ga yanayin gidansu, idan wanda za'a ma barazana ne da ku i sai ta gani, idan kuma masu bu atar jan kunne ne sai ta ja musu su kuma su ja ma arsu. *A* hankali ya sauke sanyayyan numfashin da babu wanda ya san yayi saboda fuskarshi da aka rufe da na in farin rawani, sosai ya shiga damuwar al awuran da ya auka yanzun nan da nauyin jama'a da ya hau kanshi, shin zai iya saukewa? Shugabanci abu ne mai nauyi da kuma wuyar sha'ani, shin zai iya sauke ha in al'ummarshi? Ba ma wannan ba! Wani nauyin na daban da mahaifiyarshi ta jagoranta aka aura mishi, shima zai iya saukewa? Ta ya ma akayi baya jin wannan tashin hankalin kamar sauran lokuta idan za'a aura masa aure? Bai san komai ba game da yarinyar, fuskarta? Kamanninta? Sunanta kanshi bai sani ba har yanzu, abu aya daya sani shine *ita ta bashi magani*, hakan yasa a yanzun ya bata sunan *zam-zam*. _Aunty Safiya ga fa sunan._ Ya gaji da zaman nan jama'a a cikin manyan kayan, sai dai har yanzu ba i ke shigowa, a haka wai wan anda ke kusa ne da zasu iya zuwa, a bar maganar wanda zasu taso takanas dan tayashi murna da addu'a. A hankali ya sake lumshe idanu ya gya a kanshi tamkar yana masa ciwo ya amsa gaisuwar mataimakin gwamna yana jin yadda fadawan ke amsa masa da cewa "Sarki ya amsa, sarki na godiya." Wannan sha'ani ne mai wuyar gaske, abun ne ya zamar masa biyu, ba gaira ba dalili yana zamanshi Ummi ta sakashi tunanin wacece ita? Ya za ta kasance? Fari' cikinsa ko ba in cikinsa? Fatanshi