← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 116

Sashe 113

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kika kira." Da kulawa Saleema tace "Aunty jikin nashi da sau i dai ko?" A sanyaye tace "To da sau Daga angarenta tace "Shikenan aunty, to akwai ku i hannunku ne na siyan maganin?" e baki tayi tace "To, da dai zan je ne idan ma basu isa ba ko bashi ne su biyo mu kafin a samu, kinsan mahaifinki ba aje ku i masu yawa yake a gida ba, dam..." Jin za ta kawo mata wasu dogayen maganganun da ita ba su ne a gabanta ba yasa ta cewa "Ba damuwa aunty, zan aika yanzu a tura muku ta Amana sai ku cire ku siyi maganin." Da fara'a sosai ta amsa da "To shikenan ar albarka, Allah ya saka da alkairi." A sanyaye Saleema tace "Aunty dan Allah idan Abba ya tashi ki bani shi a waya." "To in sha Allah." Ta fa a tana kauda kanta daga dubansu, suna gama maganar wayar Hadeeya ta kira, ba jimawa ta aga cike da fa a da masifa tace "Yanzu Hadeeya ni zaki rainawa hankali, ki ce za ki turo mana ku i amma shiru har yanzu." Cike da rashin taunawa tace "To ya zanyi dan Allah? Nima shine na ce ya bani kuma sai hanya hanya yake min, yanzu nan da yar na amshi jaka goma a hannunshi, gata nan zan tura muku amma har kin yi gajen ha uri." Da mamaki Ardiya tace "Jaka goma?" "E." Ta fa a ita ma a dake, wawan tsaki tayi tana fita a akin kafin tace "Allah ya tsinewa jaka goma Hadeeya, ke dan buru'ubaki kin san nawa yarinyar nan Saleema ta turo ranar da muka zo garin nan? Jaka ari biyu da hamsin fa, a hakane yanzu na ce mata bamu da ku i ta ce za ta sake aiko mana, to ita ta fi ku sanin hanyar kar an kudi ne a hannun namiji? Ko abun cikin bujen da take aga masa ne ya fi naku mahimlanci?" A hassale Hadeeya tace" Kinga Momma ni gaskiya kar ki sake ata min rai, ta ya zaki ha amu da Saleema? Ita tana sana'arta kuma mijinta ma zai iya mata fiye da haka, mu kuma fa?" Cike da masifa tace" Yanzu kun ga anfanin nema kenan? Can da ina matsa muku kar ku biyewa maza su dakusar daku a gida ai baku yarda ba, shikenan to ki ri e banzar jaka gomarki ba sai kin turo ba." Tana gama fa a ta kashe wayar ranta a ace sosai game da sha'anin yaran nata, haka fa tunda safe Hameeda ta ce ta turo ku i a je a auko, cike da isa da asaita da jin na ta an ma sun taimakawa mahaifinsu ta tura an Yayan mijin nasu ya je ya auko dan ta ji da in yayatawa Hameeda ce ta turo, abun takaici yana zuwa ya mi a mata jaka talatin, da fari ta auka yaron ne ya so cutarta shiyasa ta kira Hameedar ta tambayeta, e, shine abida ta fa a mata kenan dai ita ta turo haka din, shine yanzu ita waccen za ta ce wai jaka goma? Goma aniyarta, ita da goman ma... Ke ni ki ban goman, haba! Almubazzara kawai. *09:20 na dare* ewa Alhaji Rabilu yayi yace "To Yusuf ni zan wuce gida, sai da safe idan na dawo." Cikin taushin murya Alhaji Yusuf yace "Yaya, ka jira ka an mana Ardiya ta dawo sai ka tafi, ka ga ma lokacin shan maganina ya yi." Kallon agogon hannunshi yayi yace "To ai dare ne ke yi, gashi kuma ban san a ina ta aje magungunan ba ni da na baka." Juyawa yayi gefenshi yace " azu dai na ga ta sakasu a waccen drower, ban sani ba ko suna ciki har yanzu." Zagayawa yayi zai duba yana fa in "Ban da ma abun Ardiya, ke da kike jinya ina ke ina fita wai gidan awarki, mtssss!" Murmushi yayi mai ciwo tare da takaicin da ya san sanda aka yanke shawarar ha oshi da ita ma shi kam da ya ce a'a ya gode. Ledar pharmacie ya auko tare da zazzage magungunan yace" Wane a ciki ne za ka sha yan..." Sai kuma ya auke takardun recit na ku i da ta aje a cikin ledar ya ri e da hannu aya, guda biyu ya nuna mishi ya alla ya bashi sannan ya mi o masa ruwa, zaune yayi kan kujera yana duba takardun ba wai da wata manufar ba, murmushi yayi tare da lankwashe takardun ya auki ledar maganin ya mayar dasu ciki. Hira suka an fara ta awa sama sama, kamar daga sama an Alhaji Rabilu ya shigo akin, duk kallonshi sukayi a tare inda mahaifinshi da mamaki yace "Kai kuma yanzu a wannan lokacin? Ya ma aka yi suka barka ka shigo? Bayan lokacin rufe asibitin ya yi." Wayarshi dake hannunshi ya mi o ma mahaifin na shi yace "Ce musu nayi kira ne na gaggawa daga fada kuma wanda za'a ba wayar yana ciki, Abba aunty Saleema ce ke son magana da kai." Duba wayar ya yi ya ga yanzu ne kira ke shigowa, agawa yayi tare da sallama cike da dattako, da ladabi Saleema ta amsa suka gaisa sosai, kallonshi Alhaji Yusuf yayi da ya ji yace" Muna fa godiya sosai ata da ari, Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya baki masu miki kema." A sanyaye ta amsa da" Ameen Abba, dama ina ta son magana da Abba ne naji jikinsu, amma aunty ta ce har yanzu jikin dai, shiyasa nake so muyi magana da kai na ji ko dai za'a fitar da shi ne waje." Da mamaki ka an a fuskarshi yace" Jikinshi da sau i sosai ata, ba bu atar ki aga hankalinki, mu dama muke tsammanin saki a kowane lokaci, jininsa kawai ke hawa yana sauka." Cike da ladabi ta sake cewa" Abba to an siyo magungunan na azu ne?" Yanzu kam mamaki ne sosai a fuskarshi yace" Magunguna kuma? Wasu sabi aka runuta?" Ya tambaya yana tsare Alhaji Yusuf da idanu da shima yake kallonshi, ba tare da sanin komai ba tace" E Abba, azu ai munyi waya da aunty ta ce an rubuta magani sa ta je ta siyo shine na turo ku in." A sanyaye ya girgiza kai yace" Gaskiya ban san da wannan maganar ba, kuma tunda suka zo nan ni ke siyo magani, idan ba ni ba to cikin an uwanki ne, bana jin ko ruwa mun ba Ardiya damar siyowa." Kai tsaye ta fahimci me auntynta ta aikata, dan kar a kalleta da laifin yasa Saleema fa in" Ohhh! Ayya, Abba na tuna ba fa aunty ba ce, su Mama ne mukayi waya dasu akan jikin Hamdeeya, amma... Abba?" Murmushi yayi irin na babba da yaron in nan dan shi ya gane komai tunda har ya ga zahiri sannan yace" Na'am." A shagwa e tace" Abba ku bani Abba mu gaisa dan Allah, ni gani nake kawai wayo kuke mana kuna cewa lafiyarsa alau..." Dariya yayi yace" To shikenan gashi, na san idan kin ji muryarshi za ki yarda ko?" Tsittt! Sukayi sai sauraren numfashin juna kafin daga bisani tace" Abba ya jikinka?" A sanyaye ya amsa da" Da sau i Hajiata." Shiru ne ya ara biyo baya sai kuma tace" Allah ya baka lafiya Abba." "Ameen." Ya fa a yana sakin murmushi tare da mikawa Yayan nashi wayar shi kuma ya ora a kunne yace "Yanzu hankalinki ya kwanta?" "Ummm!" Ta fa a kamar mai son fashewa da kuka, sai kuma ta sake taisa muryarta tace "Abba ku kula da shi, duk abinda ake bu ata ku sanar mana." Cike da aunar yarinyar da kuma tausaya mata yace "In sha Allah Hajiata, ki kula da kanki kema, Allah ya miki albarka." "Ameen." Ta fa a tana kashe wayar kuka na kwace mata tana jin ina ma Abbanta ne ke saka mata albarkar nan? Ganin ya kar i wayarshi yasa ya fita yana cewa uban "Abba sai ka zo." Saida ya ga ficewarshi sannan ya kalli Alhaji Yusuf yace "Ka godewa Allah Yusuf, Allah ya baka a mace tamkar namiji dubu, wallahi ka yi sa'a a rayuwarka, yarinyar da ka tauye ta hanyoyi da dama, amma sai amon muryarta ya ke fitowa ta inda ba'a yi tsammani ba, ba wai dan Safiya tana ar uwarmu ba, amma ni dai gaskiya na fi ganin girmamawa ta a ga ubansu a idanun yarinyar nan, tana da hankali na jajirtaccen namiji, tana da hangen nesa irin na namiji mai shekaru, tana da sanin takamata na maza goma, Yusuf, ka godewa Allah wallahi, dan ba arya Allah ya maka babbar baiwa a rayuwarka." Gyara zama yayi tare da kawar da kanshi daga kallon da Alhaji Yusuf in ke masa yace" Gaskiya nake fa a maka, duba ka ga fa ta kasa yarda da abinda muke fa a mata a kanka, burinta shine ta ji muryarka ka ai hankalinta ya kwanta, ga irin awainiyar da take ta yi a kanka duk da kuwa cutarta ake, amma dake akan *mahaifinta* ne ta ji ta gani, kuma ta gane hakan a yanzu amma sai ta ke so ta rufe maganar kawai saboda ita ba wannan ne gabanta ba." Sunkuyowa yayi ya ora gwiwoyinshi a cinyoyinshi yana kallon an uwan nashi da yke fa in " awainiya? Su da suke can ni ina nan? Ta ya ya?" Murmushi yayi yace "Kwana biyu ka ai ka yi a nan, amma yanzu na ga recit na ku in da ta turo guda biyu dan a siya maka magani saa da jaka ari uku da hamsin, ba ma wannan ne abun dubawar ba, ta dalilinta fa aka mana alfarmar da aka kawoka nan a asa da lokacin shigarka ha ari, wallahi ba dan ita ba mu dai nan duk yadda zamuyi sai ka kai wannan lokacin ko ka wuce." ewa yayi tsaye tare da matsawa ya an dafa kafa arshi yace" Ni zan tafi gaskiya, dan ba zan iya jiran matarkan nan ba, idan ta dawo ka gaisheta." Juyawa yayi ya wuce yana fa in" Allah ara sau Da kallo ya bishi har saida ya fice a akin kafin ya sauke ajiyar zuciya yana sake nutsuwa sosai dan auna abubuwan da ya fa a
Chapter 113 · 0% Book details