← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 116

Sashe 91

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zancenshi, to ya sani ba komai na bashi ba face wuta, ni kuma ban san gaibu ba ina yanke hukunci ne da abin daya bayyana gareni."_, ka sani ranka shi da e akwai ranar tsayuwa, ranar da zamuyi shekara dubu hamsin a tsaye ba tare da Ubangijinmu ya ce mana uffan ba, ranar da za'a kusanto da rana izuwa unan kawunanmu tana tafasa mana walwa tamkar talgen tuwo, ranar da za'a taramu daga an adam na farko har zuwa na arshe, ranar da za'a tara annabawa na farkonsu da na arshensu, ranar da mala'iku zasu zagaye aljanu, aljanu kuma su zagayemu, a wannan ranar adalci ne ziryan, ranar da hatta dabbar da ta soki ar uwarta da aho sai an tsayar da su an musu hisabi, ranar da nauyin aikinmu ne yake yin sama, sharrinmu kuma ke yin asa sa anin sikelin duniya da nauyin ke yin asa, yalla ai..." Numfasawa tayi tace" Ka sani a wannan ranar babu wani sarki, babu hadimai, babu bayi bare dogarai, babu wa annan masu maka kirarin da kurentaka, a wannan lokacin da kowa ke ta kanshi, a ba zai taimaki ubanshi da komai ba, duk soyayya dake tsakanin uwa da anta ba zata anfanesu da komai ba, ranar da aka fa a mana tsabar masifar dake cikinta uwa za ta saka hannu ta jawo an dake cikinta ta fito da shi sannan ta jefar da shi shima yayi ta kansa, a wannan ranar ne ubangijin duka talikai, mamallakin ranar sakamako zai ce da kowa *yau mulki na waye*?... " Murmushi ta saki ta tsurawa fuskarsa idanu wanda suka riki a sukayi ja tace" Babu wani mahalukin da zai iya amsa wannan tambayar, Allah da kanshi zai ce *mulki nawa ne ni ka ai*..." Hawayen da suka an gangaro mata a kumatu ne yasa yatsarshi ya share mata, shi kanshi tsoratarwar da ta mishi ta sakashi kukan zuci, idanunshi sun ka a ya ara jin tsoron ubangijinshi, ha a wannan ita ce matar da ta dace dashi, wacce za ta dinga tunasar da shi waye shi ma karan kanshi. A jikinshi ya rumgumeta sosai yana fitar da numfashi, ita kuma shashe ar kuka take yi har ya an dinga bubbuga bayanta yace "Nagode zam-zam." agowa tayi ta kalleshi tace "Ka tafi, an kusa tayar da sallah." Babbar rigarshi ya gyara yana kallonta yace "Zam-zam, wa ya kamata na yi abota da shi a fada? Kowa sadda kanshi yayi idan ina wurin." o hannunshi tayi tace "Wanda zai fa a maka gaskiya komai acinta, wanda zai fa a maka halin da al'ummarka take ciki, to shi ne ya dace ya zama abokinka." A sanyaye yace "Gaskiya ne, nagode zam-zam." Murmushi ta masa shi kuma ya fita zuwa masallaci, ita ma nata angaren ta nufa dan gabatar da sallah, tana idawa kuma ta auki makullin madafa ta shiga dan ora girkin dare. *Tana* cikin aikin gimbiya Kubra ta shigo madafar, da ladabi Saleema dake yanka albasa a saman katako ta juyo tace "Barka da shigowa ranki shi da arewa madafar kallo tayi kafin ta kalli Saleema tana yatsina fuska tace "Uhum! Me kike ne?" Da fara'a tace "Girki." Matsawa gimbiya Kubra tayi kusanta tana kallon aikin da take tace "Me yasa za ki za i raba kawunanmu?" an kallonta Saleema tayi sai kuma maida dubanta kan aikin da take tace "Ba raba kawunanku zan yi ba." "To me kike yi yanzu haka da kika raba abincinmu da mai martaba?" Ta fa a tana tsareta da idanu, sai kuma ta kauda kanta tace "Ko kuma dai dan yana sarki ne sh..." Da sauri Saleema tace "A'a ranki shi da e, ni na yi hakane saboda aure nake a gidan nan, a ganina kamar bai kyautu a ce ba wani abun da zai ha ani da shi na daga hidima ba." Da wani kallo ta bita tace "Ba kina zuwa turakarsa ba?" Ita ma wani kallo ta jefeta da shi da yasa ta ji kamar matar bata da kunya, hakan yasa ta auke kanta tana murmushin mugunta tace "Ni me nake yi a turakar? Ai yalla ai ne ke arin, shiyasa na fi so na ciyar da shi daga ingantattun kayan masarufin da yake da bu ata a jikinshi dan arin lafiya." Wata muguwar harara ta watsa mata gyara tsayuwa cike da takaici tace "Kinga yarinya, mu nan ba ma haka, ki dakatar da wannan munafurcin na ki, daga gobe za'a ci gaba da girki tamkar yadda kika samu ana yi, sannan ki maida makulli a hannun Shamsu, shi zai ci gaba da sa kula da komai." Tana gama fa a ta juya ta fita a madafar, da kallo ta bita kafin ta ta e baki ta ci gaba da aikinta ba tare da jin wai za ta aikata abinda gimbiya Kubra ta fa a ba. *Washe gari* da safe a madarar dake angarenshi ta girka masa abun kari har ya fita, na rana kuma a madafar waje tayi, lokacin gimbiya Kubra ta sakankance cewa ta ji abinda ta fa a ne da ta ga da safe bata shiga ba, amma yanzu da aka kai mata labarin tana madafar tana aiki sai ta garzayo ta zo gurin gimbiya Ramlat ta kawo mata orafin. Ajiyar zuciya gimbiya Ramlat ta sauke ta kalleta da kyau a tsanake tace "Ina ga da mun ba wa lamarin nan baya, gidan mijinta ne tana da damar da za ta yi duk abinda ta ga dama, yi masa girkin da kanta ba laifi bane, sai dai..." Numfasawa tayi tace "Zan saka mata idanu na gane nufinta, idan har udurin na mai kyau bane, zan auki mataki da kai." Da yanayin rashin jin da i maganganun gimbiya Ramlat in ta kalleta a kausashe duk da a sanyaye take kallonta tace "Kenan ba za ki iya dakatar da haka ba har sai kin yi bincike? Ni a ganina wannan raba kawunan ahalinmu ne, ta ya za ta raba abincinshi da an uwanshi da kuma mu iyayenshi?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da ora afa aya kan aya tace "Duk da ya zama sarki, bamu cire rai da sake zaunawa da shi mu ci abinci tare ba, amma da wannan tsarin nata sai komai ya bayyana cewa ya ara yin nesa damu kenan." Murmushi gimbiya Ramlat tayi ta sauke numfashi tace "Shikenan, zan mata magana a dakatar... *idan da yiwuwar hakan*." uru ta sake ura mata idanu da mamaki da haushi, sai kawai ta li e bakinta ta shiga arin tashi tsaye, kallonta ta dinga yi ita ma da murmushi a fuskarta tana ayyana "Ni za'a kawowa zancen banza ba? Mijinta ne ai, tana da hurumi." Har ta fice daga akin bata daina kallonta ba kadin ta kawar da kai tana ta e baki. Gyara zamanta tayi sam a ranta ba ta da niyyar wai tuntu ar Saleema akan maganar nan, sai dai a yi duk wacce za ayi, amma kam an yi wal iya ta ga kowa kuma ba zata sake bari a cuceta ba bare anta. *Alhamdulillah.* 26/06/2022 22:53 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _49_ Ganin har *kwana uku* yau da ta samu gimbiya Ramlat da maganar amma ba wani hwan asawa da ta yi yasa ta nemi gabatar da aikinta ko ta wane hali duk da kuwa irin cikas in da Saleema ta kawo mata dalilin raba wannan girki da ta yi. Shigowarshi kenan aramin falon dake kusa da fada dan hutawa kamar yadda aka saba, ma fi yawan lokuta idan shari'a ta yi zafi ne ake shigowa dan hutawa kafin a ci gaba, dogarin dake gadin ofar ne ya shigo yana rusunawa har asa yace "Allah ya taimaki farin sarki mai farar zuciya da farar aniya, sa o ne daga gimbiya uwar marayu mai talakawa." Daga ofar da ya nuna ya fahimci wanda ya kawo sa on yana waje kenan, dan haka ya masa alama da hannu a ta aice yace "Uhum!" Da sauri ya fita ya wangale ofar akin, jim ka an ya sake shigowa da kyakyawan tiri a hannunshi, yana zuwa ya aje gabanshi sannan ya mi e yace "A huta lafiya ranka shi da Saida ya fice sannan ya kalli farantin, murmusawa yayi a kan la anshi tare da saka hannu ya fara warware rawanin dake kanshi dan ya samu damar shan iska, saida ya warware duka ya aje gefe sannan ya kai hannu kan jug in ta kwalba tare da aukar kofin ya fara tsiyaya kakkaurar madarar da ke da sanyi. Dake shi ubangiji idan har ya maka talala a rayuwar akwai ranar in dillanci, akwai lokacin da zai nuna maka komai yana faruwa ne a yadda ya tsaranshi, hakane ta faru yanzu ma, *kiran* Saleema ne ya sa shi dakatawa daga zuba madarar ya gyara zamanshi ya jingina a kujerar, aukar wayar yayi yana kallon kofin dake hannunshi a sanyaye ya furta " *Uwar gidana*." Da murmushi a fuskar Saleema daga inda take ta amsa da "Barka da rana yalla ai." ar ajiyar zuciya ya sauke yace " *Matanmu*, me kike yi yanzu?" Saida ta waina idanunta tace "Umm! Na gama wasa yanzu haka." Wara idanunshi yayi sosai yace "Wasan me? *baby*?" A shagwa e tace "Ina yi wa ar tsanata inki ne." "Subhanallah." Ya fa a da mamaki sosai sannan ya sake fa in "Kina son abokin wasa ne?" A ladabce tace "Um!" Murmushi ya saki tare da ora afarshi kan aya yace "Kin samu, ba dai abokin wasa ba?" Numfashi ya sauke kafin yace "Wato Gimbiyata, na ga alama kin sha u da Ummina matu a, tunda gashi har ta zayyana miki komai a kaina." Da mamakin rashin fahimtarsa tace "Komai a kanka? Ban gane ba?" Kofin hannunshi ya matso kusa da bakinshi yana murmushi yace "Ma'ana kinsan duk wani motsina, tunda gashi daga shigowata hutun da bai gaza minti talatin ba, har kin aiko min da abun sha." Murmushi ta saki tare da mirginawa ta gyara kwanciyarta, da fara'a a fuskarta tace "To ai..." Sai kuma ta tuna wani abu, ita dai bata aika masa komai ba, ya kenan zai ce ita? Tashi tayi zaune
Chapter 91 · 0% Book details