← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 116

Sashe 73

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kalleta ba tace "Kinga ba dan Mu'az ya riga *Lukman* fara soyayya da ke ba, ai da na masa hanyar aurenki." A fakaice suke son nuna mata kamar soyayyar da sukayi da Mu'az da kuma rabuwarsu ne ya kawo mata jinkirin, a ganinsu an sanshi shiyasa kowa ya guje mata saboda ana ganin kamar ragowarsa ce, tayi kuka na an lokaci sai kuma ta sake mi a al'amuranta ga mai kowa mai komai. *Ahalin Jiji* Saida ta zauna asa kafin tace "Ina kwana Abba." Saida ya kawar da kanshi sannan ya amsa da "Lafiya." Jiki a sanyaye ta mi e za ta fita a akin, da harara Ardiya ta bita ta ta e baki ta ayyana "Za'a tsufa a haka." Har za ta fita Safiya ta turo Ahmad gaba tace "Je ki da shi ina zuwa." Dawowa tayi Safiya na kallon fuskarta wacce a yanzu ta saba gani mai tattare da damuwa babu walwala ko aya, kama hannun Ahmad tayi yana rigimar sai ya je wajen Abbansu ya kar i waya, hannu ya tara masa hakan yasa ta sakeshi ya tafi, aukarshi yayi ya ora a cinya Saleema kuma ta arasa fita, da satar kallo ya bita ganin Saleema gabanshi haka na matu aga masa hankali, ba wai dan tana da shekara *Ashirin da biyu* bane ba aure, a'a yadda annenta sukayi suka barta ne ya fi damunshi, kuma ita ba aiki ba sannan ba karatu ba, gata ita kuma da manyan asusuwa, hakan yasa a yanzu dai ita da Ardiya da Mahaifiyarta ba ka banbance a da iyayenta, kafa a da kafa a suke. Kallonsu yayi tare da maida hankalinshi kansu yace "Maganar Hadeeya ce dama, jiya sun zo nan ita da mijinta suna rigima, ita ta dage dole sai ta mori karatunta ta hanyar yin aikin gwamnati, shi kuma ya ce baya bu ata, amma za ta iya za ar duk sana'ar da taga zata iya shi zai bata jarin, ta nuna sam bata so, shine na ce su bani lokaci zanyi shawara, ya kuke gani?" Wani kallo Ardiya ta masa sama da asa cike da ganin ya antasu tace" Yanzu matsalar gidan auren ata ka kasa a farantin gida kowa ya kwashi kasonshi?" Sai kuma ta kalli Safiya cike da izgili tace" Ka jira ta fara aurar da ta ta ar mana, sannan ne za ta fahimci girman ha in da Zeid in ke neman takewa." Malalacin murmushi Safiya tayi ba tare da ta kalleta ba tace" Kamar dama jira kike a yi magana ki fa i abinda kika fa a, ina ga bani na ce ya nemi shawarata, dan haka za ku iya ji da matsalarku, ban da lokacin wannan hayaniyar." urawa tayi za ta mi e yace" Ban gama magana ba, sannan kada wacce ta sake canza mana maudu'i." Cike da masifa Ardiya tace" Nima ba lokacinku nake da ba, ar da tayi kwantai zan zauna ata lokacina a kanta? Alhamdulillah ana biyu suna gidan mazajensu kuma sune asa da ita, ita kuma fa? Hahahahaha!" Ta kece da wata dariya tace" Ita ba matar gida ba, ita ba matar waje ba, ba aikin fari bare na ba i sai zaman ak..." ufule da mugun hanzari ya mi e tare da yo wa kanta ya aga hannu kamar zai kifeta da mari, sai kuma ya dakata cak yana kallonta, a hassale yace" Kin ci albarkaci abu aya, amma kada ki sake aibata min Juyawa yayi yana kallon Ahmad dake wasarshi da waya yace" Ku tashi ku bani wuri." ewa duk sukayi suna hararar juna, suna fita falonsu Safiya ta kalleta tace" Aure nufi ne na Allah, sannan lokaci ne da shi tamkar rayuwa, ke baki isa ki hanata aure ba idan lokacinta yayi..." yasta yatsunta tayi tace" Kuma ina mai tabbatar miki za ki sha mamakin wannan jinkirin na ta, dan ina ji a jikina alkairi zai zama in sha Allah." Cike da izgilanci da rashin sanin gaibu ta bushe da dariya tana tafa hannaye tace" To madadin mamakin da zan sha ki ce min zata *auri sarkin garin nan mana*, kinga sai na kasance cikin wanda zasu dur usa gaishe da gimbiya... Hahahahahaha, wayyo Allah cikina." arashe da wata dariyar tare da barin Safiya a tsaye, saida ta shige wasu hawaye masu zafi suka kwaranyo mata, sosai taji zafin maganar ta Ardiya, gashi kuma Saleema ko saurayin ba ta da bare ta sa ran sanin wanda zai iya kasancewa mijinta, ita fa rashin aurenta yanzu bai dameta ba, to nawa ne ma shekara ashirin da biyu? A al'adar hausa ne sai a ga yarinya ta jima, amma ko anan larabawa wannan ba wani abu bane, hasalima idan baki kai talatin ko ka an ga asa da haka ba kamar ma baki isa auren bane, sai wacce Allah ya so da rahama ne za ta yi shi da ashirin da sama... Addu'a ce ba zata daina yi mata ba, sannan ga tauyeta da akayi wajen hanata fita, idan fitar ta zma dole kuma sai ya ce su tafi tare ko kuma ya ce ta tafi da Ahmad, sam kamar dai bai yarda da Saleemar ba, ita kuma ta so yin magana amma magabatanta sun nuna mata rashin yin shi ya fi alkairi, ta zuba masa idanu ta ga iya gudun ruwansa. A farfajiyar gidan ta zauna kusa da fanfon da wasu lokuta ma ota ke shigowa iban ruwa, a nutse sosai take sauraren ro on da Gimbiya ke sake yi mata karo na uku kenan tun ha uwarsu, da za uwa da son jin me ye matsalar matar tace "Ranki shi da e, ba wai zan shiga hurumin da ba nawa ba, amma zan so sanin matsalarku dan ta zama a ddu'ata ta musamman, tabbas Allah ya fimu sanin abinda ke oye a zu atanmu, sannan yana amsa addu'a idan muka ro e da ya biya mana bu atunmu na alkairi. Ranki shi da e, wata ila abinda kuka nema a wajen ubangiji ba alkairi bane, shiyasa bai baku ba har yanzu ko kuma ya musanya muku shi da wani abun da yake alkairi a gareku, wata ika kun san abinda ya baku in ko kuma baku fahimta ba, misali lafiya, ita ka ai da Allah baku ma alkairi ce kuma ya cancanci ku gode masa, duba da wasu suna kwance suna kashe zunzurutun ku i dan a sama musu wannan lafiyar da Allah ya bamu a kyauta." Cikin tausashiyar muryar kuka tace" ata, ai lafiyar ce take neman yi mana wasa, yarima Abdus-samad a sukurkurce bana gane kansa, kinga dai ana son na ashi a matsayin sarkin mara awa, amma abun ya gagara, sau uku ana daf da na i sai ya gigice, ayan tunda ya bar garin bai kuma dawowa ba saida ya shekara biyu..." Sautin kukanta ne yasa Saleema tashi tsaye tana jin ba da i sosai sannan ta ora da" Ba mulkin nan ya fi damuna da ake son lalata min rayuwar yaro akan shi ba, sai yadda aka hanasa sakewa yayi aure kamar kowa, yana son yin auren kuma Allah ya hore mana abun yin auren ko da guda hu u ce a lokaci aya, amma da za'a mishi maganar aure aramin mahaukaci yake dawo ya nemi illata kanshi ko yayi ikrarin ruguza wacce za'a aura masa in, wasu matan ma da kansu suke cewa basa son shi... Na rasa wannan wace irin jarabawa ce, mun yi addu'a, munyi sadaka mun yi aikin Hajd da azumi da tawasuli a gurin Allah akan lamarin nan, amma har yanzu shiru kike ji tamkar... Astagfirullah! Saleema yanzu haka Abdus-samad shekararshi talatin da biyar, amma ko auren fari baiyi ba anenshi har ya haifi yara biyu, annensa mata kuma ba'a ma magana." Kukan matar shi yafi tsuma zuciyarta har ta fashe da kuka ita ma, sai gashi suna kokawa ba mai rarrashi wani, dan Saleema har ta fara hango kanta idan fa ita da ke mace t kwashe shekarun nan ba aure? Ya za ta yi? Sun fi minti uku suna kuka kafin Saleema ta fara sassautawa tana shan majina cikin dakusashiyar murya tace "Ranki shi da e, kuyi ha uri, ku sani duk abun daya faru da bawa addararsa ce, ita kuma addarar nan an rubuta tun kafin halittar kowa, *al alamin* daya rubuta addarar tamu, da *allon kiyayewa* da aka rubuta addarar tamu, malamai kansu sun yi sa ani kan wanene aka fara halitta, wannan ya nuna girman da addara take da shi da kuma anfaninta ga an adam, addara jarabawa ce, ita kuma jarabawa sai mai imani ka ai Allah yake jarabta dan a gwada arfin imaninmu, a Al ur'ani ma Allah ya fa a cewa dan kun ce kunyi imani sai mu barku hakanan ba jarabawa? Kenan rayuwar mumini cike da jarabawa masu da i da akasin haka." Numfasawa tayi tace" Ranki shi da e, Allah maji ro on bayinsa ne, ku ro eshi da magiya da kuka a lokacin da kowa ke bacci, akwai tabbaci addu'arku ta kar u a wannan lokacin, sannan kuyi ta da ya inin lallai yana jin ku kuma zai amsa muku, shi da kansa ne ya fa a a Al ur'ani, _Idan bayina suka tambayeka game dani to ni ina kusa dasu, ina amsa ro on mai ro o yayin da ya ro eni, ya ce ku ro eni sannan kuyi imani dani domin su shiryu._, ranki shi da e ku saka ya ininku akan ubangijinku, ya fi ku sanin me ke damunku, wata ila kuma jinkirin da zai zama alkairi a gareku ya muku, ina fatan Allah ya warware muku wannan matsalolin na ku, sannan zan sake magana da malaminmu su ci gaba da sakaku a addu'a, in sha Allah komai zai yi daidai, sannan nima..." Shirun da tayi yasa Hajia Ramlat data kasa kunne tana sauraren yarinyar jikinta har tsuma yake tsigar jikinta na tashi tace" Ina jinki Saleema, ci gaba, hakan na sama min nutsuwa da jin addu'ata ta kar u a wajen ubangijina, kamar yadda kika fa a tayiwu an jinkirta mana ne saboda za'a bamu babban rabo ko ba'a nan ba, wata ila a gobe kiyama." Da murmushi a fuskarta ta sadda kanta, kunya take ji ta fa a mata wasu addu'o'i ta ce a dinga karanta masa a zam-zam,
Chapter 73 · 0% Book details