← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 116

Sashe 36

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

matsala bane, ba ga motata ba, me ye anfaninta idan ba zata mayar da Haleematu gida ba?" Sunkuyar da kai ta sake yi Abban ta kuma ya kalleta kafin ya kalleshi yace "E to yalla ai, da za ka dinga kiranta da Saleema zan fi ganewa, dake sunan mahaifiyata ne, kuma tun tana jaririya muke kiranya da Saleema..." Da alamar ban ha uri yace "Oh yi ha uri, ban sani bane ai, ina anfani da sunan da na ji ankirata da shine a makarantar nan." Kallon jami'in yayi dake gefensu yace "A mayar da su gida a motata, kuma a kunna musu jiniya tamkar yanda ake min, ina so ta isa gida da wuri ba tare da ta samu tsaiko ba." Da girmamawa ya amsa tare da fita dan shirye shiryen fita irin ta gwamnan kamar yanda ya bu ata, Alhaji Yusuf kuma da a yanzun ya an fara shinshino wata bu ata a dabam shinfi e akan fuskar gwamnan Saleema ya ma nuni da su tafi, dan gaskiya ba zai so ya nemi bu atar nan ba in har abin da yake tunani gaskiya ne, saboda Alhaji Auwal kamar uba ne gareshi bayan kasancewarshi mai gida ma. A hankali suka shiga takawa Saleema na baya alamar girmamawa, amma lokaci lokaci sai ya juyo ya an kalleta yana murmushi, har saida ya kaisu farfajiya wanda hakan ya ba jami'ai dayawa mamaki duba da duk wanda zai rako har nan to fa babban ba o ne na musamman sai kuma idan mahaifiyarsa ce ta zo gidan, to ita kam da kanshi ma yake bu e mata ofa ta shiga, idan yana da dama watarana ma da kanshi yake tu ata har gidanta. Mota aya ce a gaban motar da su Saleema ke ciki, sai aya a bayansu inda ta gaban ita ke da jiniyar da ke shaida gwamna ne a kan hanya tamkar wata motar aukar marasa lafiya. Izuwa yanzu kam ita kanta Saleema wani tunani take daban, tambayar kanta take duk akak me safiyar yau take ha uwa da manyan mutane? Da wannan suka isa gida nan ma suka tarda wata hidimar ta musamman, sai kawai Alhaji Yusuf ya sada ar ya bayar da tashi gudumawar ta hanyar sakawa a kawo lemuka baja-baja aka shiga shagali a gidan. amshi, amshi rahama ne mata, ku garzayo domin samun na ku wannan danda an na ku turaren na musamman mai abun al'ajabi akan farashi mai sau i, don samun na ki tuntu i wannan lambar 94-98-56-52.* *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:49 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _23_ Kiran da ya mata ne ya tasheta a baccin da ta samu na rana, tana agawa ta saisaita muryarta ta furta "Barka." Saida ya fara sakar mata murmushi kafin ya amsa "Babyta sarauniyar mata, an gama hushin da ni?" Kunya ce ta sakata rufe fuska da tafin hannu tace "Ka yi ha uri dan Allah, na san na ata maka rai, nima ba'a son raina bane." A nutse yace "Na sani Baby, idan ban miki uzuri a wannan halin ba wa zai miki? Shiyasa tun jiya na ara zage damtse wajen du ufa da addu'a dan Allah ya bani ke nan da sati aya ko biyu, ta hakane ka ai zan sama miki lafiya." Mamakin kalamanshi da rashin fahimtar inda suka dosa yasa ta fa in" Ban gane ba? Kana da magani ne dama? Kuma ai baka san me ke damuna ba." Murmushi ya mata mai sauti yace" Na sani mana, kowace mace ai da yanda zuwan na ta ba on ya ke..." Cike da kunya da yama tace" Kaiiiiii!" Sai kuma tace" Ni sai anjima, kuma idan irin wannan maganar za ka dinga min ba zan ara aga kiranka ba." Da sauri yace" Dakata Baby, shikenan to na daina daga yanzu." A shagwa e tace" Ka yi al awari?" Cike da tabbaci yace" Na yi al awari." Gyara zama tayi suka fara ta a hira, saidai duk da haka wani abun kam kunya yake bata idan ya fa a, saida agogon akin ta alamta mata bugawar arfe 03:30 sannan sukayi sallama dan yayi haramar gabatar da sallah dan ita ba sallah take ba. akin falo ta shiga ta kama ruwa tare da canza pad in ta, tana fitowa ta ji muryar Abbanta shi da amarya yana fa in "Kinga ni ban da wasu ku in da zan ara muku, shagali ne ke kika ga zaki iya, ban hanaku ba kuma nayi ari da na baku wannan ku in ma, idan dole sai kuyi ki ara a na ki sai kuyi." Cikin masifa ta ji muryar Ardiya na fa in "Dama na san ba aunarmu kake ba, ai azu da ka shigo ba'a tambayeka, amma haka ka cire ku i masu yawa ka bayar aka siyo lemu mai tsadar gaske aka dinga rabawa matsiyatan unguwa da dangi, shine yanzu shagalin da Hadeeya za ta ha awa awayenta na murnar samun jarabawa sai ka ce baka da ku Hannaye ya zuba aljihu yace" Abinda zan iya yi kenan, in ya miki kiyi, in baki so ki bani ku i akwai abunda zan iya yi da su da wannan mahimmanci." Tsaki ta ja masa tare da cewa" Da inta dai ita wacce ake hura mana hanci dalilin bata da kwalin da Hadeeya take da." Wani malalacin murmushi yayi yace" Hazalika ita ma Hadeeyar ba ta da abin da *gimbiya* take da." Zaro idanu tayi da mamaki tace" Gimbiya kuma? Ta da a...?" Hannu ya aga da niyyar kifa mata mari, saidai ba abi'arsa bace duka mace, hakan yasa ya dakata ganin ta tsorata har ta rintse idanu, jinjina kai yayi yace" Ba ta da ilimin boko, amma tana da ilimin da kowane namiji ke neman samu a matar da zai yi rayuwa da ita, a halin da ake ciki yanzu zamu iya yin kafa a da kafa a da Saleema wajen arzi i, dan yanzu haka akwai takardar caki (check) na ku i da bansan adadinsu ba a hannuna kuma na ta, baya ga sar i masu darajar da ke baki ta a sakawa ba ajiye a drower mahaifiyarta, dan haka ki iya bakinki akan uwata wallahi sai in ata miki rai." Ficewa yayi ya barta nan tsaye, Saleema dake ban akin saida ta ji Ardiya ta bar wurin ka ai ta fito zuciyarta fess da tunanin dama haka Abbanta ke sonta? A kanta ne zai atawa Ardiya rai? Lallai yau rana ce ta musamman a gareta. ______________ Kamar zai yi kuka cikin tsananin acin rai ya kalleta yace "Mama, wallahi ba zan aureta ba sai dai ya kasheni, duba fa a kanta ne ya hanani ku i ya hanani zuwa kamfani, ni yanzu ko sisi ban da a jikina, a hakane zai min auren bayan ya ha ani da talauci." Ita ma ranta nata a ace saboda ita ta ma fishi jin haushin Alhaji Auwal din ha e da Saleema da take ganin duk ita ta ja musu wannan bala'i tace" Kai in za ka yi abin da ya ce ka yi, idan ba ka yi wallahi zai iya cireka a cikin anshi, gabanka dai ranar ba irin ba ar maganar da bai fa a min ba, ya kake so na yi? So ka ke ya sake ni saboda auren na ka?" Turo baki yayi ya sake ura mata idanu da suka mishi jajir saboda yau bai samu ya busa abin da ya saka kanshi ba yace" Ni ba haka nake so ba, kawai ki masa magana ya sake min aljihuna, haba dan Allah." Ajiyar zuciya ta sauke tace" Matsala ce ta ku i ko?" Kamar zai ha eta da ranta ya hayayya o yana fa in" E mana, na fa a miki ko sisi ban da, ya barni ko kamfanin na je amma ya Da sauri ta arasa gaban madubi ta auki aramar jakarta ta ciro ku i ta zo ta mi a mishi tace" Kar i, dan Allah Mu'awwaz ka kwantar da hankali, kar ka ce za ka matsawa mahaifin nan naka, ka yi abinda ya ke so ka ji, idan an aura maka ita dole ai ba za'a tilastaka zama da ita da farin ciki ba, ka ana mata ku arta har sai ta gudu da afafunta." Wani huci yayi yace" Mama ni ba na so ko numfashi na ha a da ita ne, ta ya ma za'a aura min ar aikin gidan nan? Wannan ai zubar da aji ne." A sanyaye ta sake cewa" Ka yi ha uri kai dai, ka ga fa ko ba komai mahaifinka zai yarda ka masa biyayya, hakan zai sa ya sakar maka duk harkokinka na da, amma ka ga ni ba zan ji da i ba a ce Mu'az ne ka ai ke kula da gidan gonarsa da kuma kamfaninsa ba, dan shalelena." Figar ku in yayi a hannunta yace" Shikenan to na ji." Bai jira komai ba ya fice a akin dan hanzarta samo abinda zai washe masa walwarsa. Ganin haka ta auki wayarta dake bakin gado ta kira Ardiya dan ta tambayeta wai da gaske ne an saka ranar Mu'az da Saleema? In kuwa gaske ne za su ga anci wallahi, dan babu ta yadda Saleema za ta ha anta aure da mai aikin gidanta sannan uta ta shigo gidan a matsayin sarakuwa, sam ba zai yiwu ba sai dai in bayan ranta. ______________ Irin takaicin da ya riski kanshi a ciki baya jin ya ta a samun kanshi a ciki sai yau, tunda ya shigo shagon ma ya kaisa aiwatar da komai, gashi yana tsananin farin ciki a asan zuciyarshi na samun nasarar jarabawarshi, babban abun farin cikin shine ya fi sauran alibai haza a a lakarantarsu, sai dai ba in cikin Sharhasila ya dame farin cikinshi ya shanye. Kifa kanshi yayi a telar da ya hau da sunan inki amma bai yi komai ba, abun daa yke tunani shine ta ya Sharhasila za ta masa haka? Kwana hu u ya rage bikinsu kawai ya samu labarin wai ta yi fa a da wasu an mata har an rufesu a magar ama, me yake damunta?
Chapter 36 · 0% Book details