Sashe 101
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga rayuwar da ta shafi mijinta." Ajiyar zuciya Saleema ta sauke tace" Aunty, na san da haka nima kuma na san zai iya yi min komai idan na nema, sai dai ku gane inda matsalar take, aunty bana da hurumin shiga abinda ya shafi mulkinsa, wannan hukunci ne da ya zartar bai kamata ni ko wani nawa ba mu masa katsalandan a ciki, yin haka fa kai tsaye shine cin hancin da yake lalata mana al'umma..." Numfasawa tayi tace" Aunty ba wai ba zan iya yi ma Hadeeya wannan alfarmar bane, zan fi kowa farin ciki a ce tana gidan mijinta kuma cikin farin ciki, sai dai gaskiya ba zan nemi alfarma a gurinsa wacce na san idan ya min ita to zai sa idarsa tare da tauye kansa saboda jin naiyina dana ahalina ya mana ita ba, kuyi ha uri aunty idan na ata muku rai." asan idanu ta fara aika mata harara kafin ta saki murmushin ya e tace" Kin gane ata? Ba wai kai tsaye za ki masa maganar ba, ke fa mace ce mai kissa da walisa, idan kika so lamarin nan ta wayar idanunki kawai za ki aika masa da sa on abinda kike so ya isar miki, kuma fa ba wani babban laifi suka aikata ba, fa a ne tsakanin mata su kuma suka shiga dan rabasu." ara ri e hannunta tayi gam-gam tace" Dan Allah Saleema ki taimaka kinji kisa baki, kuma ke ma ai gimbiya ce kin isa yanke hukunci a masarautar nan." Fuskarta ba yabo ba fallasa tace" Hakane aunty, amma fa ina da damar hukunci ne akan abinda nake da hurumi, ba wai yanke hukunci akan hukuncin sarkina ba, idan ni ce na yanke hukunci da fari zai iya yankewa a karo na biyu saboda ya isa ta kowane fanni, sarki ne shi kuma shugabana ne shi, amma ni kam ban da wannan damar gaskiya, kuyi ha uri aunty." asan idanu ta sake hararenta sannan ta mi e tsaye tace" Shikenan, na san ai da ciki aya kuka fito da kin sa an saki mijinta, da kuma ni na haifeki da ban isa na zauna a nan ina miki magiya amma ki kasa saurarta ba, nagode." Da kallo ta bita har ta fice a akin sannan ta girgiza kai dan ta san dama ba zasu fahimceta ba bare har su mata shaidar arziki, saidai akan haka ba fa za ta ta a shiga hurumin da ba nata ba gaskiya, shi kanshi ba zai ji da i ba idan ta yi, idan kuma ya zo ya musu kafiya to ribar me suka ci, sun zubar da mutumcinsu sannan basu samu biyan bu ata ba? Ba riba kenan. Tun aurenta za ta iya cewa yau ka ai ta kasance cikin walwala saboda sakewar da tayi a gidansu, tayi farin ciki tare da mahaifiyarta da aninta, dan Ardiya fita tayi daga gidan haka ma Hadeeya, hakan yasa gidan ya musu da i ba kadan ba. Sai dai duk da haka kewar mutumin nan ta addabeta, hakan yasa duk sanda ya samu sarari to suna ma ale a waya, sai dai kuma rabin wayar tasu fa ansu ne suke orawa, dan kiran farko ma da ya mata tana auka cewa tayi "Uhum! Rashina na wasu mintuna har ya sa ka fara kirana ne?" Sai kawai ya buga kai ga kasa yace shi fa sam ya kirata ne dan ya tambayeta ko zai samu abinci daga wajenta? Yanzu ma da ya kirata cewa tayi dan fa yana shine ta aga, tund aya ce ba aunar ta yake ba me ye kuma na kiranta a kai a kai? Shi ma ya ce dan Ummi ta ce ya dinga kiranta ne shiyasa ya ke kira. Haka dai har dare ya mata a gidan bayan ya nutsu ya shirya ya zo aukarta. Saida ta shigo motar kafin ta lura da kayan dake jikinshi, waro idanu tayi ta aga murya tace "Wai da kayan nan ka fito daga gida?" Tsareta yayi da idanu yace "E, me ye?" Rumgume hannaye tace "Ba komai, ina mamaki dai ne." Murmusawa yayi ya tayr da motar suka bar gida, kallonta ya sake yi bayan sunyi nisa yace "Matanmu, zamu iya zuwa cin abinci? Yunwa fa nake ji, kuma kinga yau haka kika manta dani gaba aya." Da sauri ta kalleshi tace "A'a gaskiya, ni ban ta a zuwa cin abinci ba wani wuri, kuma ma ko zan je ba da wannan babbar rigar ba." Kallonta yayi yace "Ban gane ba? Ba dai nufinki sai kin cireta ba?" aga masa gira tayi alamar e, girgiza kai yayi yace "A'a wallahi." Ci gaba sukayi da tafiya ba jimawa ya faka motar a gidan abinci na Rosario kasancewar sun fi kusa da nan, bai fita a motar ba sai ma wayarshi da ya shiga daddanawa kamar ya manta a inda suke, ita kuma tana kallon motocin dake laye a wurin da alama su ma suna cikin gidan cin abincin. Mutum biyu ta ga sun fito daga gidan cin abincin auke da runfar nan ta kakkauran leda mai kwalliya, a kusa da inda ake faka motocin taga sun aje suna arin yi mata masauki, a nutse suka kafa ginshi anta har runfar ta tashi tsaf, da sauri suka koma gidan abinci aya na auke da kujeru biyu farare aya na auke da teburin shima fari ar na roba, suna komawa ciki mace aya da namiji aya suka fito da farantai a hannayensu suka awata wurin da abinci da abun sha, a daidai lokacin manager wurin ya fito kai tsaye motarsu ya tunkaro. Fita yayi daga motar bayan sun yi musabaha taga suna magana kafin ya koma ciki shi kuma ya zagayo ya bu e mata ta fito. Yanayi mai da i tare da wanda zuciya ke so, hakn yasa duka fuskokinsu auke suke da asaitaccen murmushi dake kwantar da hankalin junansu, sake kallonshi tayi a karo na adadi tana murmushin daya fito da ha oran makarta tace "Nagode *mijina*." Ba tare da murmushi ya bar fuskarshi ba yace "Ba komai matanmu, kin cancanta ai, ya kamata ke ma kisan kina aure, ba kullum a takure a fadar masarauta ba da kuma alkyabba." Wani farrr tayi da idanu tace "Gaskiya kam, na ji da i sosai." A haka suka kammala cin abincinsu ba hayaniya kuma babu hasken fitila cike da nisha i kafin su bar nan su koma gida. Kwana biyu kenan amma har yanzu bai sake tada mata maganar da Abbanta ya mishi ba kuma ba ta ji labarin ya sakesu ba, dan haka ta ba maganar baya kawai, shi kuma ya yi shiru ne kwana biyu ya ga ko za ta masa maganar, amma kuma sai ya ji shiru hakan yasa shi ara girmama lamarinta, har yau da yake zaune gaban mahaifiyarshi cike da ladabi yace "Ummina, kin san da yarinyar nan ar aljanna ce ko?" Duk da ta gane da wa yake, amma sai ta share ta kalleshi tace "Wace yarinya kenan Babana?" asa yayi da kanshi yace "Ummi wace yarinya kuwa face wacce ta kafa mana tarihi." Da sauri tace "Ohhh! Saleema wai? Ai sosai ma, shiyasa na za a maka ita." A sanyaye yace "Ummina, me kika sani game da ita? Ina so na tambayeta amma kunya ke hanani." Da mamaki ta kalleshi tace "Kunya kuma? Akan me?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Sai nake ganin kamar ba za ta ji da i ba idan na tambayeta labarin rayuwarta." Murmushi tayi tare da ci gaba da damun furarta tace "Ban san abu dayawa a kanta ba, saidai bayan zuwanta nan muna hira sosai, a nan ne na san abunda na sani a rayuwarta ta baya, Saleema dai ta taso a gidan..." A ta aice ta bashi labarin rayuwarta har zuwa wayarsu da Saleema ta arshe wacce take fa a mata mahaifinta zai mata auren dole, dalilin da yasa kenan suka shirya da yayanta da kuma an uwan mahaifinshi aka nema mishi aurenta a oye saboda kada masu hana ruwa gudu su shiga lamarin. Sake kallonta yayi ya saka hannayenshi biyu ya fara matsa mata afafunta wanda ya jima bai mata haka ba sai Saleema ce ke yi yace "Ummina, amma dai kinsan wallahi Allah ne ya ceceni ya wanke yarinyar nan ya bani, yanzu fa da ta auri waccen na farkon da aka saka musu rana?" Sai kawai a zuciyarshi ya ayyana "Rabona." Dariya tayi tace "Ai dan tana taka ce shiyasa ma lamarin ya wargaje." A hankali ya ci gaba da matsa mata afafun ita kula tana damunta yace "Ummina, ranar ma fa haka na sameta ta gama yanka wai ita inki take yi, Ummi ba kya ganin ya kamata muyi wani abu game da burin nan nata?" Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace "Nima na yi tunanin haka, amma kasan gidan nan da kuma matsayinka, zai sa a yi ta ananan maganganu, shiyasa ma ban maka maganar ba, ni dai karatu ne dama na ke cewa zan fa a maka ina so mu fara da ita." Shi ma fuskarta ya kalla yace "Ummi makaranta za ki kaimin iyali?" Murmushi tayi tare da hararenshi tace "Tun farkon zuwanta gidan nan fa na fa a maka, ina so ta dinga koya min karatu." Murmushi yayi ya sadda kanshi yace "Ba damuwa Ummi, za'ayi, za'ayi komai da kike so, kawai ki mana addu'a, amma bai kamata mu bari burinta ya ruguje ba." Zumar dake gefenta cikin kwalba ta auka ta tsiyaya a cikin furar sannan ta auki gorar dake auke da kakkaurar madarar ta zuba sannan ya juya ta mi o masa, kar a yayi tare da gyara zama ya aje tasar gabanshi sosai ya fara sha da bismillah. Lumshe idanu yayi yana murmushi yace "Ummi, wato a duk duniya har yanzu ban samu wacen ta kaiki iya damun fura ba." Murmushi tayi tace "Har * ar Baiwa*?" Zuba mata idanu yayi kamar da mamakin ya take son ureshi haka? Sai kuma yayi murmushi, hakan yasa ta dungure mishi kai ta yale da dariya tace "Ja'irin yaro, wato na kamaka?" Dariya yayi ya sunkuyar da kai yace "Ummi, da na gama shan furar nan gyara afafu za ki yi na kwanta na yi bacci, na jima ban samu haka ba ina so kuma