← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 116

Sashe 61

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya dawo ya kawo mata maganin, kuma har akin su Saleema ya shiga ya kai mata, abunda ya tsayawa Nafissa a rai shine ruwa sa ya sa Saleema ta kawo masa ya bata da kanshi kafin ya tafi, ita kanta Saleema saida tayi mamaki dan tunda ta ha a aurensu baya kulata, maganarshi da ita marar da i ko kuma gatse, amma yau sai ta ga hada tausasa mata yake har suka gaisa irin gaisuwa sosai. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:50 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _34_ Biki ya yi biki in ji mawa i sarkin wa a, an yi hidima sosai mata ma su aji kowace ta nuna ta ta bajintar da wayewa, daga arshe dai dare na yi masu niyya suka shirya dan raka amarya akinta, Saleema ma ba'a barta a baya ba ta rufa musu baya dan rakiyar anwarta akin mijinta tana mai mata faran farin ciki da zaman lafiya, duk da dai wannan biki da aka yi ta ga abubuwan al'ajabi, a ciki kuwa har da yanzun da suke kan raka Hadeeya gidanta, kwalliyar da aka mata ta ban mamaki yasa aka hanata yin ko da walla na ba in cikin rabuwa da iyayenta, tana ji tana gani anwarta ta fita a gidan ba alamar jimami ko ba in ciki bare damuwa na za ta tafi ta riski wata sabuwar rayuwar. _(Kwalliyar da ake ma amarenmu yanzu har da kunya take gushe mana, dan wannan kwalliyar take hana amarya zubar da hawaye dan kar ta ace, wanda a al'adance mun saba ganin amarya na kuka, muna yara har hakan ya kan zama abun alfaharinmu mu ga amarya na kuka za'a kaita akin miji, amma ban da amaren yanzu, ari ma suke fuskarsu ta fito da kyau wajen aukar su hoto dan kar a ga muninsu, a cikin hotunan amarya guda goma bakwai idanunta na kallon camera ne, Allah ka shirya mana zuri'armu)_ Tunda Mu'az ya samu labari a wurin wani abokinsu cewa ai har da Saleema a gidan amarya ya tarkato duk abinda yake ya zo nan, duk inda ta gilma a ofar gidan Hadeeya yana biye da ita sai dai bai yarda ta ganshi ba yana la e, ba komai ya sa shi zuwa ba sai sanin akwai abokansu dayawa ire-irenshi, dan haka ba ya fatan a sapu wanda zai tunkareta da ko da maganar banza a wurin, dan haka yake tsaye kan duka wani motsinta har saida ya ga an fara mayar da mutane gida, saida ya ga motar wanda ta shiga tare da wa anda suka shiga motar ya samu nutsuwa ka ai ya bar ofar gidan shi ma. *A can* kuma sanda gidan yayi shiru sai ma'aikata dake ta gyaran gidan da wanke wanke, lokacin Ardiya da Gaishata suka shige aki tare da Hajia Iklima da ita fa duk ku in nan na su take ganin ta fi su, ji take kamar a auye take a gidan nan, ta matsu ta tafi gida ta huta, amma Ardiya ta ri eta wai za su yi magana mai mahimmanci, yanzu haka fuskarta a yatsine take tana ta ma akin na Ardiya da ko a asar waje sai haka kallon wani kurkuku, ba dan nata akin ya di na Ardiya ba sai dan son nuna matsayinta ya fi na su. Ardiya da ta maida hankalinta garesu gaba aya ne tace "Hajia, kin san me na gani kuwa yau a gidan nan?" Fuska a gatsine ta girgiza kai kawai alamar a'a, orawa tayi da "Hajia, wallahi da idanuna da kuannuwana na ji yalla ai yana fa awa wannan banzar ba auyar yarinyar wai yana sonta kula zai aureta, yau na ga abun mamaki." Da rashin fahimta Hajia Iklima tace "Ban gane, wane yalla an?" Gaishata da ta samu labarin tun zuwanta ne tace "Mijinki mana, Alhaji Nasir, ni ai abun hauka ya so sa ni." ura musu idanu tayi tace "Ban gane ba? Wace yarinya ya ke so?" Ardiya ce tace " ar kishiyata mana, wannan marar ajin Saleema." Wani mugun kallo ta aiki musu tace "Mijin na wa?" Sai kuma ta feso iska a bakinta ta tashi tsaye ta auki jakarta tace "Sai anjima." Da sauri duk suka tashi tsaye Ardiya na fa in "Wallahi ranki shi da e ba arya muke fa a miki ba, ni da idanuna na gansu, da safe sanda ya shigo nan ina masa godiya na abun arzi i da ya turo mana, sai mahaifinta ya ce ita ma wai ana son ganinta, na yi mamaki sosai shine na la e dan na ji me ke faruwa, qhine na ji yana cewa yana sonta da aure har ma ya bata katinshi ta kirashi." Gyara tsayuwa tayi cike da jin kai tace" Kun gane, bana ha a komai da mijina a rayuwata, kada ku jazawa yarinya bala'in da kafatanin danginta zasu shaida ta ja rigima da ni, idan kun san da wasa kuke tun wuri ki daina, dan ku kanku zan iya aje mutumcinku da nake gani gefe na shuka muku ta'asar da bakuyi tsammani ba, kun gane?" Cike da jin da in zantukanta Gaishata tace" Ba wasa ba ce Hajia, wallahi gaskiya muke fa a miki." e fuska tayi sosai tana huci tace" Kenan shiyasa ranar ya gayyaceta har gidanmu? Na yi mamakin yadda ya kar i ba i a wannan lokacin kuma a gidanshi, abu ne da baya faruwa." Sai kuma ta kallesu tace" Me yasa kuka gaya min? Ba ku san zan iya aukan kowane irin mataki ba?" Murmushi Ardiya tayi tace" Mun sani, kuma dan ba ma so haka ta faru shiyasa muka sanar da ke, ki auki matakin da ya dace kawai." Wani malalacin murmushi tayi tace" Kinsan da zan iya komai a kan mijina?" Kallon juna sukayi Ardiya da Gaishata sai kuma Ardiya tace" Saleema yarinya ce mai tsoro da taka tsantsan, ina ga ma kashedi ya isheta ta fita harkar mijinki, musamman idan kika mata barazana da Mahaifiyarta." ufule, da sigar dabamci tace" Shikenan, zan ha u da ita gobe, zan fara ganin me ye take da shi da bana da, kafin na kora mata kashedin." Juyawa tayi rai ace ta fice a gidan Gaishata da Ardiya kuma suka fashe da dariya, Gaishata ce tace" Yar banzar yarinya, ba uta ta ha ani da al ai ba gashi nan har ta samu ciki tana shirin haifa min ba in jika, da yardar Allah ita ma ba za ta yi farin ciki a gidan aurenta b" Dariya Ardiua tayi ta koma ta zauna tace "Ta ma fara samun wanda ya dace tukuna, ta ya Hadeeya ta auri wanda ko Mu'az bai kai da komai ba, sannan na yarda Saleema ta auri gwamnan garin nan? Ba na fa awa Iklima bne dan ina sonta, dan ta aga hankalin kowa a fasa auren ya sa na yi haka, idan har ba ta samu mijin da bai kai Zeid ba to ba zan ta a hutawa ba." *Washe Gari* arfe *05:14* Saleema ta fito da sauri za su tafi wajen damu tare da Nafissa, sosai doguwar rigar ankon atamfar ta mata kyau duk da hijabi ta ora wanda musamman inkashi tayi saboda ranar, har ta kai farfajiyar inda Nafissa ke jiranta Ardiya dake tsaye suna magana ita da ar uwarta tace "Saleema." "Na'am." Ta fa a tana juyowa, nuna mata falon tayi tace "Je akina ki auki turarukan Hadeeya na nan a kan gado ki tafi da su." "To." Ta fa a da sauri ta dawo akin tana rataya jakarta arama akan kafa a, tana shiga akin mace biyar ta samu suna ta hira, a jumlace ta gaishesu da "Ina wuninku." Duk da wasu daga ciki sun gaisa tun sanda suka zo, amsawa sukayi asa asa har ta ra a ta nufi kan gadon. Wata kakkauran mata mai iba ce ta mi e tsaye tana fa in "Ku fito mu jira waje ko, Hajia Iklima amaryar gwamna Alhaji Nasir za ta yi magana da mai shirin aye gurbinta." Dammm! Gaban Saleema ya fadi tayi saurin kallon matar dake hakimce kan gado tana latsa wayarta, saida ta ji jikinta ya auki rawa dan ba ta san ita ce matarsa ba, aukar ledar da ta ga kwalaben turaruka tayi ta shiga jerin matan dake fita har da Gaishata dake dariya tana fa in "Amarya kuma uwar gida ba, ta gidan ma ya ta iya da ita?" Bushewa sukayi da dariya har da tafa hannu suka fice, matar nan mai iba ce ta juyo za ta rufe ofar ta ga Saleema bayansu tana shirin fita, da hannu aya ta hanka ota ta dawo akin tana fa in "Ba ki ji an ce za ta yi magana da ke ba ne?" Tangal-tangal tayi kamar za ta fa i kafin ta tsaya kan afafunta, a hankali ta juyo ta kalli Hajia Iklima da har yanzu kamar ba ta san me ke faruwa ba, gyara tsayuwarta tayi tana ta kallon matar tana jira ta ji me za ta ce mata. Saida ta yi niyya da kanta ta sa afarta da babu takalme ta turo kujerar robar dake gefenta sannan ta mata alama da hannunta mai waya alamar ta zauna, jiki a sanyaye ta ja kujerar ta zauna tare da ora ledar turarukan a cinyoyinta tana ci gaba da kallonta. Numfashi ta sauke tare da aukar jakarta mai kyau da tsadar gaske ta saka wayarta a ciki sannan ta maida hankalinta kan Saleema, a nutse cike da aji da yatsina fuska tace "Saleema ko? Gundarin ba i ba kame-kame ba, ina so ki sani ni ba tsararki ba ce da zaki dinga kula min mijina, ban sani ba ko uwargina kika sani shiyasa kike tunanin kin isa ha a shinfi a da mijina, to ki sani ni ba lusarar mace ba ce, ki fita a harkar mijina, a hakan ma dan ina ganin darajar Ardiya ne yasa na miki kashedin nan, ba dan haka ba zan iya aikata komai a kanki kuma ba za'a san ni nayi ba bare wani ya aga maganar, kin fahimta?" Gyara zamanta tayi ta nuna mata ofa tce" Za ki iya tafiya."
Chapter 61 · 0% Book details