Sashe 16
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana kallonta, arara tsoro ya bayyana a matashiyar kamar za ta arta a guje, saida ta samu tabbacin yarinyar da ta gani jiya ce sannan ta shiga are lata kallo daga sama zuwa asa. Bayan abubuwan nan da ita ma Allah ya hore mata guda biyu, wata cikakken irji da mazaunai ba ta ga wani abu da yarinyar ke da shi da za ta birge Mu'awwaz da ake ikrarin na da tsantseni da yami ba, numfashi kawai ta sauke da ta tuna wa'azizzika da take saurare da suke magana kan mata da miji, ita kam ta san akwai wani babban tasiri da magana- isu dake da tasiri a jikin namiji wanda a jikin mace ka ai ake samunsu, dan abun ya girmi tunani ka ga ma'aurata sun yi fa a baja-baja da rana, amma da dare ya yi su sulhunta kansu, musamman ma namiji da shi ya fi fara neman sulhun. Ko shakka ba ta yi cewa wannan yarinyar ma Allah ka ai ya san *BAIWAR* da ke tattare da ita da ya sa har ta auki hankalin Mu'awwaz, yaro walisa, ga kyau ga nasaba ga ku i da ilimi. Lura da kamar ta na tsoron Saleema ya sa ta sakin murmushi tace "Me ye sunanki?" Da sauri ta ago ta kalleta ido har sun cika da walla tace "Hajia dan Allah ki yi ha uri, ka da ki tona min asiri, wallahi ba laifina ba ne." Cike da raha Saleema tace "Sunanki fa kawai na tambaya, amsa ce mai sau Marairaicewa tayi tace " *Nafissa*." Kallon tsanake ta mata tace "Nafissa, ba ki san cewa ke mace ba ce? Abinda ki ka aikata jiya zai iya zama silar rugujewar duka zuri'arki, wannan abun da ki ka bashi ba tare da aure ba, shi in dai shi ne mutumcinki da za ki yi tutiya da shi, me ya sa kika bayar da shi a arha haka?" Sunkuyar da kai ta fara yi cike da nadamar rayuwarta da kuma dana-sani, cikin kukan da ba shi da anfani a yanzun tace"... *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:38 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _12_ Cikin kukan da ba ya da anfani yanzun tace "Ni ma ba'a son raina ba ne, iyayenmu sun rasu kuma ina da annai guda uku duka mata, sai na yi aiki sannan in ciyar da su, shi ne sanda na fara aiki a gidan nan Alhaji Mu'awwaz ya ce zai bani aikin da zai linka min abin da za'a biyani, na auka wani aikin ne ashe dam...ashe wai..." Lumshe ido Saleema ta yi tana sauke numfashi kamar wacce ta sha wahala, cikin matsanancin kuka Nafissa ta ci gaba da cewa" Tun daga lokacin ya ke min barazana da kar na sake kowa ya ji abin da ke faruwa, duk da ina biyan bu atuna da na an uwana da ku in da yake bani, amma dai ina jin ba da i sosai kan abin da muke aikatawa." Kallonta Saleema tayi da mamaki tace" Dakata! Dakata! Na ji kina cewa daga lokacin, kina nufin ba jiya ne ya fara faruwa ba?" agowa tayi ta kalleta tace" Ko ka an, wata uku kenan yanzu da hakan yake faruwa." Da tsabar mamaki Saleema ta rufe bakinta da tafin hannu tace" Wata uku? Ki na sakar masa jikinki kamar wanda ya biya sadakinki?" auke hannun tayi ta kawar da kanta, cikin kuka Nafissa tace" Hajia ina cikin wani hali ne, anwata da take bi min ta fara fita ban san ina take zuwa ba, hakan ya aga min hankali da na ta a ganinta a tasha tare da wata awarta da kula irin karan motocin nan, sai na ke jin da duka mu taru mu lalace, gwara a ce ni ka ai abun ya shafa, shiyasa na ci gaba da biye masa ya na bani isassun ku in da na ke musu duk abun da su ke so, kuma rabin abin da na samu kishiyar Mamanmu ta ke wacewa." Juyowa Saleema tayi ta fuskanceta tace" Wai tsaya! Dama ba ku ka ai ku ke rayuwa ba?" Girgiza kai tayi tace" A'a, tare da kishiyar Mamanmu mu ke, mahaifinmu ya rasu shekara aya da ta wuce, tun daga lokacin rayuwa ta sake mana zafi, matar Babanmu da anta gallaza mana kawai suke, gidan da muke ciki ma a rabon gado su aka ba wa, yanzu haka muna zaune gidan ne muna biyan ku in hayar akin da mu ke ciki." Cikin jin haushi da takaici Saleema ta an daki teburi in gabanta tace" She aniyar mata." Kallon Nafissa ta yi tace" To amma ba ku da wasu an uwana?" Cike da jimami ta an murmusa tace "Akwai, amma rashin sa'armu shi ne, mun zo a lokacin da ake wasa da zumunci, kowa na shi kawai ya sani, kafin rasuwar mahaifina har aurena aka tsayar, amma da ya rasu kuma matarshi da anta suka handame an abun da ya bari a duniya, haka ina ji ina gani aka fasa aurena." Cike da takaici Saleema tace" Saboda me wai?" Kallon fuskar Saleema tayi tace" Saboda babu wanda zai min kayan aki, iyayen wanda zan aura kuma su ka ce sam ba za'a yi haka da sj ba, wai shi ne zai min kayan kenan? Ba dan dukanmu muna so ba suka soke aure, yanzu ma har ya yi aurenshi.." arasa fa a ta na wasu hawayen, cike da tausayawa Saleema tace" Kun yi karatu ne?" Jinjina kai tay tace" E, amma ni shekara aya kenanda na daina, saboda fafutukar da na ke ba za ta barni na yi karatu, a alla wannan gida na uku ne nake aiki, kafin shi kuma na yi wanki da daka, har sarrafa awara na dinga yi na mutane ma su siyarwa, sannan na yi aikin wanke-wanke a ashin mai siyar da abinci, sannan na yi aiki a gidan wata Hajia da ita ma take siyar da abinci, muna tayata girki tana ba mu abinci da ku i, na ji da in aikina sosai a gidan duk da ba wasu ku i na ke samu ba, sai dai akwai maza da ke shigowa gidan siyan abinci, tun a nan na ke fuskantar farmakin maza, sai kawai na ha ura da aikin dan na tsira da mutumcina, ashe Allah ya rubuta ba a can zan rabu da shi ba sai a nan." Da sauri ta kalli Saleema da ta ji shashe ar kuka, ai kam hawaye ta ga tana yi sosai, da sauri ta matso kusanta ta dafa kafa arta tace" Hajia ki yi ha uri kin ji, ni dai dan Allah ki rufa min asiri kar ki fa a ma kowa, na miki al awarin ba zan sake amincewa da shi ba." Cikin kuka mai ban tausayi Saleema ke fa in" Mu na rayuwa a babban gida cikin farin ciki, za mu ci abinci da safe, sannan mu nemi abun ta awa idan rana ta yi, idan aka jima za mu ci abincin rana, zuwa yamma ka an mu sake cin wani abun dan marmari ko sha'awa, idan dare ya yi mu ci na dare, wasu lokuta mu kan ci abinci kala uku ko biyu, baya ga kayan da in da mahaifinmu zai siya mana, ban ta a bu a wurin ajiyar mahaifiyata ban samu kayan walam da ma uashe ba, ban san me ye yunwa ba a rayuwata... Ashe wasu na can suna fafutuka da abin da za su ci? Ashe wasu yara marayu na can na neman abin da za su rayu da shi? Ta ya na yi wannan kuskuren? Ta ya?" Wani matsanancin kuka ta fashe da shi ta zube asa, hankali tashe Nafissa ta tsuguna ta na bata ha uri, sai Saleema ta bata tausayi sosai da jin cewa lallai wannan ta musamman ce a cikin ahalin nan, wai kukan nan a kan damuwarta ne? Kuka sosai Saleema ke yi kamar ranta zai fita har saida Nafissa ta tuna da muhimmin abu da take ta yi saurin fa in "Hajia dan Allah ki daina kukan nan, kar ma su gidan su zo su auka wank abu na miki su koreni, dama tun jiya ya ce kar na sake zuwa, amma saboda ba ya so a zargeshi ya ce na zo yau, amma daga yau ba zan sake dawowa gidan nan ba, ni yanzu zan je na kaiwa Alhaji maganinshi lokacin shan shi ya yi." A hankali Saleema ta ago kanta ta kalleta tace" Ba za ki daina aiki ba, za ki ci gaba da zuwa kamar kullum, Mu'awwaz kuma zai biya a kan abin da ya aikata, na miki al awarin wato mi ki ancinki." ewa sukayi a tare Nafissa na kallonta tace" A'a Hajia, kar ki sa kanki a ha ari saboda ni, ki barshi shi da Allahn da ya halicceshi, ba ni ka ai ya wa haka ba bare na fi kowa jin zafi, tun kafin ya fara nemana na ta a kamashi da wata anwar Mamansa a akinshi, hakan halinshi ne, idan ki ka matsa za ki iya rasa na ki mutumcin ke ma." Wani murmushi ta yi tace" Bai isa ba, Allah ne ya ce "Wanda ya dogara da shi to ya isheshi." Ta ya wani aramin alhaki kamar Mu'awwaz zai cutar da mu yanda ya ke so kuma ya kasa girban abin da ya shuka? Ba zai yiwu ba." Jinjina kai Nafissa ta yi cike da jin aunar matashiyar lokaci aya tace" Hajia zan tafi na kai wa Alhaji maganinshi, zan dawo yanzu." Da mamaki ta kalleta tace" Dama Alhaji bai da lafiya ne?" Da sauri tace" A'a ba wannan Alhajin ba, mahaifin mai gidan." Waro ido Saleema tayi tace" mahaifin mai gidan? Dama a gidan nan ya ke? Ko wane gidan ki ke zuwa kullum kai masa magani?" Girgiza kai ta yi tana fara'a tace" A'a, a nan bayan gidan yake." Jinjina kai Saleema tayi duk a tunaninta gidan tsohon a nan unguwar yake bayan gidan Alhaji Auwal, dan haka ma ta gyara fuskarta tace" Muje na rakaki." Jinjina kai tayi ta bu a wata drower ta auki magunan sannan suka fita a madafar