Sashe 58
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sha'awa, dayawa qai suka shiga tunanin dama haka take yarinyar nan? Amma take tauye kanta ta hanyar rufe jikinta ko ina, wasu kuma na ganin ashe da babban dalilin da yasa take rufe jikinta, dan kuwa ugunta ba iya fa i kawai gareshi ba har da kakkauran auwawun da suka isa wadatar mai kallonsu sake rinjayar ragamar idanun su ci gaba da kallonta. Daga cikin masu kallon nan har da Mu'az da yau dai Zeid da kanshi ya lalla oshi ya zo kamun nan, ya jima daga zaunen nan yana tsarkake zati da buwayar Allah, ya jima yana ambaton Allah aya, haka kuma ya jima yana godewa Allah da ya sa bai ta a ganin haka kafin yau ba, ya kuma yi godiya ga Allah da Saleema ta zama lai suturta jikinta, ba dan haka ba da bai san ina fitinar surarta za ta tsaya ba. Tunda ya waiga damanshi da hagunshi ya ga wasu mazan abinda yake kallo shi suke kallo, sai dokin zuciya ya sukwaneshi zuwa birnin kishi, sai yake ganin akan me dan ubanninsu zasu ura mata idanu su ma? Bai san me ya aikata ba, haka bai san me ya rinjayeshi ba kamar yadda bai san me hakan zai janyo ba, shi dai kawai ya ganshi ya mi e tsaye ya tunkareta, a lokacin da ta rusuna dan aje cake in a tebur in dake gaban Hadeeya da Zeid cikin shiga ta alfarma, hannunta kawai ya ji ya dam a wanda hakan yasa ta saurin sakin cake in har tebur in yayi ara uta kuma ta ago a tsorace tana kallon wanda ya ri eta da wannan iban karan mahaukaciyar. *Humra fara* *Humra ba *Sabulun gyaran fata* duka akwai ga mai bu ata. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:50 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _33_ Duk wurin tsit ya auka in banda wasu daga cikin an matan dake rawa wanda basu kula ba, amma hatta Hameeda da ta fi kowa gullisuwar rawa saida ta tsaya tana kallonsu, Ardiya da awata kuma wara idanu sukayi dan kallon ikon Allah, sa'a aya a lokacin Safiya na angaren mahaifinsu Saleema tana gyara wurin dan ita ce da aiki, wannan hidimar kuma ba za ta hanata kula da sashen mijinta ba. A zabure ta finciko hannunta sai dai ko alamar sakinta bai yi ba, jujjuyawa tayi gefe da gefe ta kalli yadda mutane ke kallonsu, kallon fuskarshi ta sake yi wanda duk firgicin da take ciki ta ga yau in ya mata kyau duk da ya ara ramewa, amma ya yi haske ga kuma manyan kayan da suka masa kyau, idanunta taf sukayi da walla ta marairaice yanayin da ta san yana bugashi a asa har ya safe mishi gwiyoyinshi, a hankali ta sake mitsika wuyan hannunta na ta dake jim cikin tattausa kuma faffa an hannunshi tare da sanyaya murya tamkar mai ra a tace "Yahyah, hannuna?" Lumshe idanu yayi a hankali ya fara sassauta mata ri on har ya saki gaba aya sai kuma ya matso daf da ita, shi fa sam ya manta da mutanen dake zagaye da su, dan haka cikin yanayin da shima ya san idan ya mata magana take saurarenshi har ta tausaya mishi, cike da kasala da gajiyawa ya karkace kai cikin muryar rarrashi yace "Baby, me yasa kika fito haka? Duba fa sai kallonki suke." Da sauri ta jaye hannunta daya saki ta mayar bayanta ta kalleshi da yanayi na acin rai tace "Sai me? Ina ruwanka dani to? Ka damu dani ne dama?" Juyawa tayi da sassarfa ta shiga takawa har ta fice a filin ta tunkari shiga falonsu, ashe yana biye da ita haka idanuwan mutane ma na biye da su da ma aukakin mamaki har da Zeid da ya ji kamar ya urma ihu daga zaune ya zundumuwa Mu'az in zagi saboda kare masa bayan Saleema da ya fara shagala da kallo har yana ayyana "Kutumar uban can! Dama haka ar islamiyyar nan take?" Amma saboda bu ulu sanin sai an kalli bayanta yasa Mu'az babakere da babbar rigarshi kamar mai gyarata yana sa awa a kafa a, hakan ya hana duk wani mai mugun nufi da kallon waf rasa damar sake ganin wannan al'ajabi. Saida ta zo daf da shi ya sake fa in "Babyyyy." Da sauri ta juyo dan bata tsammaci shine a bayanta, da mamakin rainin hankalinshi ta sake kallonshi cike da tsiwa tace "Me ye? Lafiya?" A raunane tamkar wanda ke tsoronta yace "Magan nake so muyi." "A kan me?" Ta fa a da kallon tuhuma, sai kuma tayi alamar kamar ta tuna da wani abu tace "Oho! Na tuna, kana so ka ka ce min na yi ha uri ne akan abinda ya faru? Sannan ka ce na yafe maka ko? To ba komai, kamar yadda ka ganni na jima da mantawa da komai, hasalima har na samu wani mijin." Shirin juyawa tayi za ta shige da sauri yace "Wallahi kina matsawa sai na ri ugunki a wurin nan." Take ta tsorata ta zazzaro idanu sai kuma ta kya e fuska ta turo baki, da yanayin rashin wasa ya shiga arewa fuskarta kallo yace "Kin samu wani mijin? Ya kaini? Ko ya fini? To ina miki barka, ni magana nake so muyi da ke akan anwarki Hadeeya." Duk da ta tausasa muryarta amma da yanayin jin haushi tace "Uhum! Ita kake so yanzu ko? To ai abokinka ya rigaka, ka ha ura kawai, dama Allah bai addara zaka zama suruki a wannan gidan ba." Maganarta sosai ta basho dariya, amma sai ya murmusa yace "Ba akan wannan ba, akan mijin da za ta aura ne?" Cike da rashin damuwa tace "Ka ga, shi in dai amininka ne da baka da kamarshi, haka ka fa alin lokutan baya, dan haka ni dai yanzu banda wannan lokacin." Har ta juya sai kuma ta juyo da sauri ta ha e hannayenta alamar ro o tace "Yalla ai Mu'az, nagode da karamcin da ka nuna min, ina maka godiya abisa ruguza min zuciya, nagode so...sa..i." Maganarta ta arshe ta sakashi lumshe idanu dan cikin rawar murya tayi maganar alamar kuka na son wace mata, da kallo ya bi bayanta har ta acewa ganinshi, a sai ance ya juya tare da kama hanyar fita dan komai ya fice masa a rai ba zai iya ci gaba da zama wurin ba. Sosai jama'a suka taru dan shaida wannan aurin aure, duk rashin son sakewa na Saleema dole ta fita suna ta kai da kawo matsayinta na ar gidan kuma Yaya ga amarya Hadeeya, wanda dayawa daga cikin abokanan wasa dangin mahaifinta ke tsokanarta ita bata yi auren ba har anwarta ta rigata, hakan bai dameta sai dai ta murmusa dan bata san yadda ake yi da an uba ba a wannan fannin. Hayaniya ce ta sake kaurewa sanda aka tabbatar aure ya auru, dan kuwa maza na ta shigowa suna wa iyayen amaryar barka da wannan arzi Ardiya na zaune salon uwar amarya kenan, tabbas ba arya ta kece raini a xikin shigarta ta dakakkiyar shaddar zuma da uwar sar ar dake wuyanta tanfatsetsiya, Alhaji Yusuf ne ya shigo yana ta faman sa a rigarshi, bai arasa saboda matan dake wurin ya kalleta yace "Hajajj, ki zo Yalla ai ne ya shigo ki masa godiya na awainiyar da aka yi." Ko da ta ji haka ta san gwamna yake nufi, mi ewa tayi da fara'a da tunanin wani arzi in ne ki kiranta, ba dan haka ba ta san zai yi wuya a ce ya shigo a irin wannan lokacin da ta san yana tare da masu tsaronshi saboda cunkuson da aka samu. Daf da zata isa inda Alhaji Yusuf ke tsaye yana jiran ta shigo ta ofar falonshi dan ya rufe Saleema ta fito daga akin Mamanta duk ta rumgumo lamukan da take ta rabawa mutane, dakatawa yaui daga shirin rufe ofar yace "Hajia." Da sauri ta kalli inda ya kirata in dan ta san da ita yake ta amsa da "Na'am." Da kai ya mata alama yace "Ki zo ana son ganinki." Da sauri ta jinjina kai alamar to tare da aube lemukan kan kujera ta kalli aya a cikin awayen Ardiya tace "Aunty Dan Allah ku rabama na kusanku ne basu samu ba." Da kallo kawai matar ta bita dan ita ar mijin Ardiya mamaki take bata, Ardiya kuma juyowa tayi tana kallon Saleema har ta araso, mamakinta wa ke son ganinta kuma? Bayan gwamnan akwai wani a akin ne? Har ya rufe ofar bata daina mamaki da kuma tunanin nan ba. Yadda falon ke shiru sai sanyayyan sanyin ac dake hurowa da wani fitinannen amshin turaren *Pattern* da ke dukan hancin duk wanda ya kusanto falon saboda yadda ya gauraye wurin, a sanyaye suka shiga takawa da nutsuwa da kuma sallama a bakunansu, jami'i aya ne a tsaye a gefenshi, inda yake zaune cikin wata dan areriyar shadda fara sol sai yalli take wacce ta sake fito da yarintarshi a fili. Ga mamakin Ardiya inda Saleema take ta ga ya kalla yana murmushi da kuma amsa sallamar da sukayi, hakan yasa har saida ta sake juyawa ta ga wai Saleemar ce a nan ko kuwa? Wuri suka samu suka zauna Saleema na rufe afafunta da dogon hijabinta, kanta na sadde asa tana jin yadda matar Babanta dake ganin ita ce mace ta farko da ta sani wajen aji da shan amshi amma tana ta kwasar gaisuwa ka rantse ar maro a ce, jin haka ya tabbatar mata lallai kyautar da ya mata mai yawa ce wacce tafi yadda ta nunawa Mamanta. Duk sai da ta gama godiyarta tas a ta aice ya amsa da "Ba komai, yi wa kaine, nima nagode." Wannan amsar da ya bata yasa Alhaji Yusuf mi ewa ya kalli Ardiyar yace "Muje ko, dama zasu auki hanyar tafiya Niamey ne, shine na ce ya kamata su shigo dan ki masa godiya." Murmushi ta saki ta mi e tana fa in "Ai ko ka kyauta Alhaji, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare." Sake amsawa yayi da "Ameen." Daga haka bai sake cewa komai ba, ita