Sashe 5
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fad'a tana wucewa abun ta, da kallo suka bita har ta shige d'akin, jim kad'an ta fito daga d'akin da jakarta da ta b'oye a cikin hijabi ta nufi hanyar fita, Safiya ce ta kalleta tace "Ina za ki je kuma ?" Littafin makarantar ta ta nuna tace "Mama wajen Khairat zan je ta koya min lissafin nan." Harara ta wurga mata tace "Kuma shine sai yanzu da safiya za ki je musu ? Ki..." Da sauri Alhaji Yusuf ya katseta da fad'in "Karatu fa ta ce za ta je, ki barta ta tafi." Kallon Saleema ya yi yace "Uwata ta kaina, je ki kin ji sai kin dawo." Ai da sauri ta wuce kamar za ta daka da gudu saboda farin ciki. Tana fita ba ta zame ko ina ba sai gidan Hafsatu, kayan da ta nuna mata yasa Hafsatu mamaki da ta tabbatar mata ita tayi duk da na yara ne, da mamaki ta sake kallonta tace "Amma ta ya kika d'inkasu?" Cike da jin dad'in an yaba mata tace "Idan Mamanmu suka je karb'an d'inkinsu ne wajen tela sai na hau na yi." Da fara'a a fuskar Hafsatu tace "Da gaske?" Jinjina kai tayi alamar e, ita ma jinjina kan tayi tave "Masha Allah, kinga kam da Abbanki zai siya miki tela cikin sauri za ki iya d'inki." Kallon fuskarta tayi tace "To amma za ki dinga koya min?" "Sosai ma." Ta fad'a tana jinjina kai, dariya tayi tace "To zan fad'a masa." *Ko* da ta dawo ta samu Mamanta d'aki take fad'a mata "Mama, aunty Hafsatu ta ce wai na fad'a ma Abba ya siya min tela za ta koya min d'inki." Da mamaki Safiya ta kalleta tace "To, ke kuma yaushe kukayi haka?" Cike da shagwab'a tace "Yanzu ai na biya can." Kallon tuhuma ta mata tace "Kin tabbata karatu kika je ?" Jim ta yi tana kallonta da tunanin kar dai ta fad'a mata ta hanata ko ta fad'awa Abbanta, sai kawai ta d'aga kai alamar e tare da fad'in "Allah ko Mama." Jinjina kai tayi tace "Ni dai ba zan fad'a masa wannan shirmen ba, ki bari har ki fara koyon d'inkin tukuna, idan kika iya sai a siya miki." Takwaf takwaf tayi da fuska tace "Amma Mama ai dama cewa ta yi idan na je can na koyo na dawo gida sai na dinga aiki da telata, ta hakane zan fi sauk'in zama *mad'inkiya*." Girgiza kai Safiya tayi tace "Saleema, abun da mahaifinki ya ke so ki zama daban, abin da ke kike so daban." Sake girgiza kai tayi tace "Allah ya zab'a miki ma fi alkairi." Dariya Saleema tayi cike da yarinta tace "Mama idan na iya d'inki kinga faba sai kun kai ba, ni da kaina zan muku ke da aunty da su Hadeeya." Murmushi kawai tayi a ganinta shirmen Saleema ne kawai. *Bayan Wata uku* Duk girman farfajiyar gidan nan ta su cike yake da maza da mata, abun mamakin kuma yanda mata da mazan ke cakud'e wuri d'aya, kafatanin taron babu macen da ke d'auke da babban gyale bare hijab, dukansu shiga ce ta alfarma dake nuna matsayin kowace da kuma rayuwar da take ciki, kusan kowace riga da siket ne jikinta ta sagala mayafinta a kafad'a, mai d'an dama dama a cikinsu ce za ta d'orashi duka kafad'un biyu, inda fuskokinsu ke d'auke da rantsatsiyar kwalliyar da suka biya mak'odan kud'i aka cab'a musu ita, wasunsu ma har da zubo da gashi suke ya kwanta har kan wuyansu wanda aka kashe ma kud'i, jaka da takalmi masu sababin tsini kuma suka ce ja bani waje. Ba wannan ne abun tsaya wa a kalla ba sai yanda gurin ba zaka gane ina matar wane ko waccen ba, saboda bariki da wayewa ya sa kowane namiji ya saki matarsa a wani wurin yana gaisawa da abokai da kuma matan abokan, inda su ma matan ke gaisawa da abokan mazan da kuma matansu. Takon tafiyarta yasa dayawa daga cikin taron juyawa suna kallon mai tahowa, Ardayi ce cikin tsadaddar shiga wacce ta dace da yanayinta, kalarta da kuma jikinta, wanda hakan yasa ta sake haska wurin gwanin birgewa, iya d'an kwalin dake d'aure a kanta ne kawai, duk rabin wuyan rigar nan a waje yake yayin da siket d'in ya matse jikinta sosai, komai na jikinta ya bayyana ya fito mata da surarta. Alhaji Yusuf dake tsaye kusan abokanshi yana kallonta, murmushi kawai a saki ganin yanda abokanshi ke kallonta alamu ne na ta birge sai abun ya sa ya ji dad'i da jin cewa lallai ya yanko wulak'anci wannan wurin, duk da 'yar k'ibar dake gareta amma ba za ka ganta ka ce ita ta haifi su Hadeeya ba saboda iya d'aukar wanka. Saleema na gefe zaune akan kujerar k'arfe mai zaman mutum biyu, daga nan take hangen irin bidirin da ake inda hankalinta ya fi karkata kan irin d'inkunan dake jikin mata, duk da k'arancin shekarunta amma tana mamakin yanda mahaifinta ya fi ba wa wannan rayuwa mahimmanci fiye da komai, ita dai a kan idonta ta ga ya kashe kud'in da suka ba million baya a kan abinda za'a tarbi bak'in nan kawai saboda su tayashi murna na girma da ya k'ara samu a wajen aikinshi kasancewarshi malamin kud'i, a iya saninta ita dai ba ta tab'a ganin wata bajinta da mahaifinta ya yi ba ga addininshi da zai nuna ya na kishin addinin na sa, dama dama ma idan azumi ya zo, a masallacin dake jikin gidan na su ya kan sa wa ana fitar da abun bud'a baki ga mabuk'ata, sai kuma abun sahur idan aka fara sallah tahajjud, wannan ne za ta iya cewa aikin alkairin dazata iya shaida mahaifinta na yi. Maida kallonta tayi kan Hadeeya da ta shirya ko ta ce mahaifiyarsu ta shiryata cikin wata arniyar rigar kanti iya gwiwoyin Hadeeyar, ta yi kyau sosai dan ka rantse ma yar turawa ce, sai dai a ganin Saleema kamar ba ta dace ba, sam gani take yi shigar ba ta birgeta ba. A hankali ta sadda kanta kan takardarta fara tas sannan ta fara zana wuyan rigar da ta ga Mamanta ta saka d'azu ita ma da za ta zo wajen taron, dan wuyan ya burgeta sosai hakan yasa ta tsurawa rigar ido ta gama hardaceta a kan ta kafin Safiyar ta saka. Kiran da aka masa a waya yasa shi d'agawa ya na d'an matsawa daga wurin ya amsa da "Ina jinka Abdul, ka zo ne ?" Jim ya yi alamar ya na sauraren me maganar kafin yace "Ok ina zuwa." Hanyar fita ya nufa yana fad'awa mai gadi "Bud'e k'ofa akwai wanda zai shigo." Bud'e k'ofar mai gadi ya yi ya fita har k'ofar gidan yana dubawa, cikin wata tsadaddiyar mota bak'on ya fito tare da matarshi da ita ma ta gaji da had'uwa, gaisawa sukayi sosai kafin ya musu alama da su wuce gaba, suna shiga shi ma ya bi bayansu da niyyar shigewa muryar Hafsatu ta dakatar da shi daga niyyar shigewar tana fad'in "Ina wuni Abban Saleema." Juyowa ya yi yana ganinta ganin dai ya d'an shaidata wasu lokuta Safiya na kai mata d'inki yasa shi d'an sakin fuskarshi ya amsa da "Lafiya lau, ina wuni ?" "Lafiya lau, ina Saleema ?" Ta fad'a da fara'arta, ba yabo ba fallasa ya amsa da "Ta na ciki." Murmushi ta yi tace "Saleema kenan, akwai k'ok'ari wallahi, idan ta yi wani abun ba za ka ce yarinya ce ba, shiyasa ma na ce ta fad'a maka a siya mata telarta, dan hakan zai fi kawo mata sauk'i." Da mamaki da kuma rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ya gyara tsayuwarsa yace" Tela kuma?" Ba tare da tunanin komai ba tace" E, idan aka siya mata mai aiki da lantarki ma za ta fi gaskiya." Har yanzu dai da mamakin ya sake cewa" Dama ta na koyon d'inki ne?" D'an shiru ta yi sai kuma tace" E, ta yiwu ka manta dai, ai kusan wata uku kenan da ta fara zuwa, dan ma ba na koya mata wasu abubuwan saboda k'arancin shekarunta." Wani kallo ya mata lokacin da idonshi suka fara yin launin ja na b'acin rai dan jin yaudara da ha'intarshi da Saleema da kuma mahaifiyarta sukayi, wato idan ya fahimta duk lokacin da Saleema ta ce mishi za tatafi karatu can ne ta ke zuwa? Jinjina kai kawai ya yi ya shige bayan ya furta "Nagode." Ya na shiga inda ya hangi Saleema zaune ita kad'ai ta dasa kanta k'asa ta na zana abu a takarda ya nufa, ya na zuwa kam takardar ya fincika da k'arfi, hakan yasa rabi ta yage ta bi hannunshi rabi kuma a hannun Saleema da ta d'aga kanta tana kallonshi a tsorace. Kallon takardar ya yi ya ga ta zana sanfirin wuya, duk da bai gane komai ba amma ya fahimci dai abunda aka fad'a gaskiya ne dan ga shaida nan. Tsaye ta mik'e tana zazzare ido ta na kallonshi, tsareta ya yi da ido yace "Me ye wannan?" Rarraba ido ta fara yi na rashin gaskiya, kafin ta ce wani abu Safiya da ta hangesu ta kuma kula kamar ba lafiya ba ta taho tace "Lafiya Alhaji?" Rai b'ace ya kalleta yace "Me ye wannan?" Ya nuna mata takardar? Kallon rashin sani da fahimta ta ma takardar sai kuma ta girgiea kai tace "Ban sani ba, me ye wannan d'in?" Nuna kanshi yayi yace "Ni ma kike tambaya?" Sai kuma ya jinjina kai ya nunasu da yatsa yace "Ku jira a gama taron nan zan ji daku dukkanku." A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace "... *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:37 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _5_ A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace "Me kika masa kuma yanzu?" A raunane tace "Ba abun da na yi, irin wannan zanen ne fa nake yi." Ta fad'a tana nuna wuyan rigar Safiya, tab'e baki Safiya ta yi tace "Kin tabbata?" Jinjina kai tayi tare da cewa "Allah ko." Jinjina kai tayi tace "Shikenan."