Sashe 11
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hadeeya ma mi ewa sukayi suka ce "Mu je mu shirya kar mu tsayar da Yaya." Su uku ne suka nufi akin su dan shiryawa, Saleema kuma da ta kalli Alhaji Auwal ne tace "Abba, ya na ga yanzu gidan babu yara?" Murmushi ya yi ya saki kallon amarya yace "To ai yaran da kika sani su ne suka girma yanzu, ga Mu'awwaz nan kin gani ya zama saurayi, ga Ummee, Safwan ne kawai kuma ya na asar waje karatu." Jinjina kai tayi kawai ta an tsakurar abincin ta na jin duk ba da i sai ita ka ai yanzu a cikin iyayen, fitowar su Hameeda yasa ta juya dan ganin da wace shigar aka fito? " A'uzubillah!" Ta fara ambata a ranta, dan kuwa a cikin shigar ta Hameeda ce ka ai ta ga da an dama-dama, saboda ita ce ta sa doguwar riga irin na material in da ake ingawa da an-kwalinta, inkin ya bi jikinta yanda ya fito mata da surarta, kallabin kuma ta orashi a kan ne kawai amma ba ta aure ba. Amma shigar Ummee abun ya munana sosai, dan riga da wando ne da suka kamata, wandon ma irin wanda ya age mata bai sauka ba sosai, sai takalma dake afarta afa ciki, kanta kuma wata ar yaloluwar hula ce ta ora sai gashinta na doki da ya bayyana. Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli fuskokin iyayen, dukansu fara'a ce a fuskarsu har da tagomashin fa a musu "Sai kun dawo." Da gudu Hamdeeya ta tashi ta bi bayansu tana fa in "Ni ma zan je." Dariya Alhaji Auwal ya yale da ita yace "Tafi a hankali to kar ki fa Suna fita ya auki wayarshi ya turawa Mu'az sa o cewa ya kar i makullin morarshi hannun dreba akwai ku i ciki sai su tafi. Saleema da har yanzu ta kasa daina kallonsu da mamaki ne yasa ta an numfasa, a ladabce sosai cikin nutsuwa bayan ta aje cokalin hannunta tace "... *Ku yi ha uri da wannan.* *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:37 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _9_ A ladabce sosai cikin nutsuwa bayan ta aje cokalin hannunta tace "Abba, ku yi ha uri dan Allah idan abinda zan fa a zai ata muku rai..." Da hannunta ta anyi alama tace "Sai na ga kamar ba ku damu da yanda su ka fita ba kamar dai yanda yanke faruwa a gidanmu, Abba a ganinku haka dai-dai garesu a matsayinsu na a mata? Ina ganin kamar rufin asirinku da na su shine ku tayasu kare mutumcinsu..." Ganin duk sun ura mata kamar mamakinta suke ko kuma dai wani abun sai ta tsagaita, an sake kallonsu tayi cike da kunya musamman ma amarya da ta ga kamar ta na mata kallon jin haushi, sunkuyar da kanta tayi asa tace" Ina ara baku ha uri, na yi aiki da fa ar Manzon Allah (S. A. W) ne, ya koya mana hani ga mummunan aiki idan ka na da iko, sannan ya fa a mana idan za ka iya ka hana da hannayenka, idan ba zaka iya ba da harshenka, idan ba zaka iya ba ya ce to da zuciyarka, ma'ana ka yamaci abun a zuciyarka, shiyasa na mu ku magana amma ban yi da raini ko ata muku ba." Mamar Ummee da take ganin kamar da arta Ummee ne take, dan ita bata ga aibun shigar su Hadeeya ba ma sam, cikin fushin da ta kasa oyewa ta kalli Saleema tace" Kinga an mata ki yi abinda ya shafeki, bana son mutum mai shiga sabgar da babu ruwansa, ina aibun shigarsu a nan? Yaranki ne mu da za ki zaunar da mu kina mana wannan maganganun? Oho! Idan na fahimceki so ki ke ki ce mu in ba mu san abinda ya dace ba sai ke." Dogon tsaki ta ja ta mi e tsaye tana aukar wayarta ta juya ta bar wurin, da kallo Alhaji Auwal ya bita kafin ya maido kallonshi kan Saleema da ba ta ji da i ba tace" Abba dan Allah ka bata ha uri, ita dama gaskiya aci ne da ita, mafi alkairin mutane kuma shi ne wanda za'a fa a ma gaskiya ya auka har ya yi anfani da ita." Ajiyar zuciya ta sauke jiki a sanyaye ta mi e tsaye ta kallesu tace" A ci lafiya." Juyawa ta yi za ta fita a falon Hajia Rabi tace" Ina kuma za ki je?" Juyowa tayi da fara'a tace" Zan fita waje ne." Jinjina kai Alhaji Auwal ya yi yace" To, amma ki kula da kanki." ar dariya tayi tace" Ba ofar gida zan fita ba, iya farfajiya ne kawai." A tare suka jinjina kai cike da jin aunar yarinyar, in har suka i abinda ta fa a to ba su da wata hujja ta in ta, sannan ba ita su ka i ba sai gaskiyar da ta fa a, dan haka ma suka ji ta birgesu duk da su ma ba su ga aibun shigar ta su ba sai yanzu ne da ta fa a hotunan shigarsu ke dawo musu a kai, musamman ma ta Ummee da ta fi munana. *Ta na* fita a hankali ta shiga an zagayawa ta na jin ina ma tana da waya da ta kira Mamanta, amma sai ta yanke shawarar idan Hadeeya ta dawo za ta kar i ta ta sai ta kira dan su gaisa, saida ta kai arshen katangar da a saninta nan in bayan gida ne sai ta dakata saboda akwai duhu wurin, juyawa ta yi da nufin arasawa wajen motoci da ta ga akwai haske ta ko ina. Sai dai kamar gizo kunnuwanta su ke jiyo mata abun da ya kayar mata da gaba duk da ba ta san me ye ba? Amma dai ta shiga zulumi da umbin mamakin wa ye haka? Me kuma ya same shi da yake irin haka? Alhalin daga ji muryar osasshen namiji ne. Cikin san a ta an fara le a kanta, ba ta ga komai ba sai dai ta ara jin sautin kusa da ita, tako ta yi da bai wuce uku zuwa hu u ba ta sake le awa dan a tsorace take. Da bala'in sauri ta rufe bakinta da tafin hannunta na hagu ta saki siririn numfashin da ya fitar da sauti kamar wacce ta sha yaji, gaba aya ta walalo idonta tsabar ka uwar da ta yi na ganin wannan lamari, take jikinta ya auki rawa tamkar mazari, da mugun gudu zuciyarta ta shiga bugawa, dan a rayuwarta ba ta ta a mummunan gani irin wannan ba na yau. Tabbas ba ta tsiraicinsu ba saboda duhun da ke mamaye a wurin, sai dai hasken wata wanda dama aya ne a cikin dalilin da ya sa ubangiji ya saka mana shi dan ya haska mana abunda ya shigarana duhu a yanar idonmu, ta hakane ta gane su waye a wurin da kuma abinda suke aikatawa. Riskar yanayin da bai ta a samu ba yasa su kansu suka tsorata sosai, yarinyar dur ushewa ta yi ita kanta jikinta ya auki ari, inda shi ma ya shiga kiciniyar saka wandonshi, jikinta na makyarkyata ta juya da sauri sosai ta tunkari komawa inda ta fito, tana jin ya biyota yana kiran "Sssaleema, Saleema dan Allah... Saleema dan Allah tsaya ki saurare ni, na ro eki S..." Shigewar da ta yi falon da sauri ya sa dole ya ja birki ya tsaya ya na hangenta, ganin ta nufi sama alamar masaukinsu za ta shiga ya sa ya daki iska yana buga afarshi da mugun haushi ya furta" Shiiiit!" Dafe kanshi ya yi aya hannun kuma ya ri ugu ya na safa da marwa a ofar akin ya rasa me zai yi, juyowar da zaiyi yarinyar ta taho har yanzu jikinta ari yake duk ta rufe fuskarta da tsohon hijabinta alamar kuka take, saida ta zo kusa da shi ta dur usa cikin kuka tace "Dan Allah na ro eka ka antani hakanan, na gaji da wannan rayuwar, yanzu haka ni da mhaifiyata da an uwana muna samun abun da za mu ci dai-dai gwargwado." A rikice Mu'awwaz ya zuba hannayenshi biyu cikin aljihu ya lalaba ya ciro ku i, mi o mata yayi cikin tashin hankali yace" Kar i, daga yau kar na sake ganinki gidan nan, ki tafi kar ki sake zuwa." A razane ta ago ta kalleshi sannan ta kalli ku in, a alla za ta iya jan jari da su, da haka za ta tsira daga sharrinshi, kar a ta yi ta mi e tana fa in" Nagode." Juyawa ta yi za ta fice sai kuma ya canza shawara, da gudu ya tari gabanta yana fa in" Kin ga! Gobe ma ki dawo, saboda nasan halin Abba da sa ido a kan komai, idan ya ji ba ki zo ba zai sa a bincika masa, ni kuma ina tsoron kar yarinyar can ta fa a masa abinda ta gani." asa ta yi da kanta alamar hukuncin nan bai mata ba, ita kam da ya barta ta tafiyarta shikenan, amma ita kanta kunya ba za ta barta ta zo gobe ba, cikin taushin murya ya sake fa in" Dan Allah ki zo gobe kin ji, bana so Abba ya yi zargin wani abu aka miki." Kallonshi ta sake yi irin kallon nan na da ke nuni ko dai wani abun za ka sake min? Kamar ya fahimci kallon kuwa sai yace" Na rantse miki da Allah ba abinda zan miki, wallahi haka ba za ta sake faruwa ba." Fuska a gintse ta aga kai alamar to, sannan ta ra ashi ta wuce ta bar gidan tana kuka na takaicin yanda ta rasa mutumcinta dan kawai ta ciyar da ahalinta, yanzu gashi dalilin haka ba ta san me zai faru ba a gaba. *10:46* su Hadeeya suka dawo gidan, har sun fito daga motar Mu'az ya bi Hadeeya da wani kallo yace " anwata zo ki ji." Juyowa tayi ta na sakar masa fari da ido ta dawo ta zauna, ganin bata rufe ofar ba yasa shi zura hannu ta gabanta kamar wanda zai ta