Sashe 70
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da shi, sai dai haihuwa nawa? Allahu a'alam, fitowar ruwan alamu na zata haife duk abinda zata auka a cikinta, farin cikin daya mamayeshi kuma bayan haka, alamu ne na girman soyayyar matar gareshi. Wannan ka ai ya isa ya sakamu farin ciki, sannan muyi masa fatan alkairi, kar mu ce zamu gaggauto da lamarin, garin haka kwa armu zata iya yin ruwa, amma mu barwa Allah komai, shi yasan me yake nufi da jinkirin na shi." Sadda kai tayi tana share hawayen farin ciki, dan ita yana fa in maganar nan hango komai take a idonta har ma ya faru, murmushin daya bayyana a fuskarta ne yasa shi fa in" Ko ke fa, yanzu ki koma gida, ki ci gaba da masa addu'a, sannan kiyi ta addu'o'in dana baki, sannan ku yawaita sada a dan na fa amiki ita mabu in alkairi ce sannan mai cinye zunubai, sannan kamar yadda na fa amiki sirrinki na ki ne, koda kishiyoyinki ba komai ne zaki zanta dasu ba a kai, haka ma *galadima* da su shamaki, idan akwai wanda zan ce miki zaki iya neman shawararsa a fadar nan, bai wuce liman da kuma anin margayi mai martaba ba, kin fahimta." Kallonshi tayi da yanayi na tsoro tace" Yaya, sai kasa na ji ina tsoron kowa dake gidan nan, Yaya a ce rayuwa ba amana, ba wanda za ka iya tattauna matsalarka da shi, yanzu ya zanyi kenan? Idan fa mutanen dake kewaye dani sune musababbin shiga Abbana wannan halin fa?" Murmushi ya mata irin na babba da yaro kanshi sadde asa, kamar ba zai ce mata komai ba sai kuma ya kalleta yace" Rayuwar kenan, kawai kiyi abinda na ce, sannan kada kiyi komai sai da shawarata." Jinjina kai tayi tace" In sha Allah Yaya, nagode sosai, Allah ara girma da lafiya." A tausashe yace" Ameen, ki kula da kanki." Jinjina kai ta sake yi ta mi e tana sake masa sallama, tana fita jakadiyarta da ta yarda da ita na zaune a aya falon, tasowa tayi da sauri ta rusuna tana mata barka da fitowa, gaba tayi ba tare da ta ce komai ba ita kuma ta rufa mata baya. Saida suka koma gida ta zauna a akinta ita ka ai ta sake aukar aramar wayarta ta kira lambar Saleema. Lokacin Saleema sun sauka a Jiddah ta gama waya da Mamanta kenan kiran ya shigo, cike da tunanin irin ku in da za'a ja Saleema ta aga suka gaisa, ga mamakinta sarauniyar cewa tayi "Saleema, dama alfarma nake nema a wajenki, ko zan samu?" Sosai ta ji mamakin sarauniya guda na neman alfarmarta, amsa mata tayi da ko me ye za ta yi, saida ta sauke numfashi tace "Dama ina so ne ki sakamu a addu'o'inki, sannan a islamiyarku ma ki ro a mana barar addu'a gurin sauran alibai da malamenku." Da girmamawa tace "In sha Allah Ranki shi da e addu'ata tana tare da ku, sannan zan isar da sa on ga malaminmu, sannan na yi al awarin ro a muku Allah a wajen da ya fi tsarki, in sha Allah komai zai daidaita." Sai lokacin ne ta san a inda take, bata sake janta da wata hira ba sukayi sallama, hakan yasa Saleema mamakin wai me ke damun matar nan jama'a da kullum take cewa a sakata a addu'a? Ita ba alamar rashin lafiya, kuma dai ba matsala ce ta talauci ba, to kenan me ke damunta? Cikin amincin Allah haka suka aura niyyar yin abinda ya kawosu sannan suka fara gabatar da aya daga cikin farillan da suka hau kawunansu sai dai banda Hamdeeya da ko balaga ba ta yi ba, wannan kwanakin sun kasance mafi daraja ga Saleema, baya ga kasanxewarsu ranakun da ta gabatar da aikinta, haka ma ranaku ne da suka kawo sha uwa tsakaninta da an uwanta, dan kullum suna tare kuma komai tare suke yi, hatta waya da iyayensu mata da suka baro a waya aya suke yi, mahaifinsu dama tare suke haka ma wajen kwanansu aya sai dai shi yana angaren maza ne. Kwana tashi a wurin Allah ba wuya sai gashi sun kammala tsaf sun dawo asarsu ta haihuwa, duk wanda ya ji zuwansu bai yi asa a gwiwa ba wajen zuwa yi musu barka da zuwa da kuma brka da sauke farali. *Sati aya* suka kwashe kafin yau dai Saleela ta shirya fita hannayenta auke da tsarabar da ta tanadarwa Fareeda da Mama da Mubarak da kula chief telor , drebansu ne ya kaita saidai a nan ya barta da cewa zai dawo ya auketa, haka ta shiga ciki ta zube musu kayan arzi in da ta kawo musu, ba ta jima a gidan ba ta fito tare da Fareeda suka shigo shagon, sai dai sun samu wata matashiyar budurwa zaune. Da murmushi a fuska Saleema ta kalleshi tana arasawa kusa da shi tace "Yalla ai barka." Da mamakin ganinta dan bai san ta zo gidan ba ya kalleta da fara'a da tsantsar farin cikin daya kasa oyuwa yace "Haleema, ke ce? Yaushe kika zo gidan?" Hararar wasa ta masa tace "Ba wani nan mana alhudahuda, kai dai kawai hankalinka na kan inki." Dariya yayi ya nunota da yatsa yace "Zamu fara ko? Daga zuwanki?" Dariya tayi ita ma wacce ta bayyanar da ha oran makkarta guda biyu tace "E mana, na yi kewarka *komai daga gareka ne*, shiyasa na kasa ha ura ma har na zo yau duk da ina son yin bacci." Dariya yayi yana jin kanshi a sama, dan fa shi gani yake yarinyar na matu ar sonshi kamar yadda yake ji a zuciyarshi game da ita, sai dai kafin yayi wata magana matashiyar nan ta mi e fuuuu! Ta fice a shagon, da harara Fareeda da ta bita dan yadda ba ta aunar Sharhasila haka bata son yan gidansu, Huzeifa kam ko kula da tsiyar yarinyar bai yi ba duk da kuwa Sharhasila ce ta turota kar an makulli saboda ta jefar da nata wajen yawo, shine ta dawo gidan take neman makulli ta turo a kar a kuma ya aiki Mubarak da motonshi kuma makullayen suna ha e dana shago da gida da duka wani abu mai mahimmanci, zaman da take ma ya ce ta jira ka an ne yanzu zai dawo. Rashin zuwa dreban aukarta yasa ta zauna suka shiga ta a hira sama sama. anwar Sharhasila kuma tana zuwa ta sameta ofar gida a mota tana jiran dawowarta, cike da son kunna wutar husuma tsakanin ma'aurata ta shiga labarta mata duk abinda ya faru a shagon, mamakinta bai wuce kalmar da Saleema ta fa a cewa ta yi kewar komai nashi ba, sai kuma yadda ta san Huzeifa ko ita dake anwar matarshi ba ya mata fara'a, amma yau wata take ma dariya ha ora waje. A haukace, a gigice, a kausashe, a matu ar hargitse Sharhasila ta fito a motarta, gyalenta ne ya fa asa amma ba ta bi ta kanshi ba, boot in mota ta bu e sai huci take tana fa in "Ni zai wula anta? Kenan mahaukaciya ya auke da bai yarda dana fa a masa zan babbaka duk wacce na gani tare da shi ba? Yau zai gani, yau zai san ar tasha ce ni kamar yadda yake fa a, wallahi ku inmu da gatan da na samu bai sa na zama sakarya ba." Babbar ma aura (ban san me zan kirata da hausa ba, abar da ake aure ko kunce usa) ta auka ta nufi hanyar shagon, da gudu yarinyar ta biyota tana fa in" Shar, Shar ki tsaya dan Allah, ki saka gyalenki mana." Ko kulata ba ta yi ba haka ta tunkari shagon ba kunya ba tsoron Allah, ga cikin dake jikinta fiye da wata shida, amma haka ta biyo titin tamkar mahaukaciya sai sambatu take tana jinjina ma aurar nan a hannunta. Kwatsam fa owarta shagon suka gani, kallo aya Saleema ta lata ta auke kai dan abu na farko da ya zo mata shine mahaukaciya ce, ita kuma mahaukaci indai ba mai bugu ba bata tsoronshi, Fareeda da ta san sai mummunan abu ya faru a take ta mi e tana zare idanu, Huzeifa ma da yana ganinta tsakaninshi da Allah saida gabanshi ya fa i ganin yanayin da ta shigo da shi shagon, tabbas yasan ba lafiya ba! Da idanunshi ya ga ta jefi Saleema da mummunan kallo sannan ta nufo kanta gadan gadan, ganin abinda ke hannunta da mugun sauri ya mi e har yana neman yin gaba da telar dan gani yayi ta tsayar dashi sosai, kafin ya fito ya iso inda suke tuni Sharhasila ta shammaci Saleema da ba ta zaton wani abu kwatankwacin haka ya faru ta soka mata wannan zundumemen arfe a ciki, dan dama zama ne tayi duka hannayenta na bayan telar dake bayanta ta jingina, hakan yasa arfen nan ya shiga jikinta sosai. arar da tayi ya sake tsumar da shi da gudu ya araso, Fareeda dake tsaye ihu ta buga ita ma ta juya da gudu ta nufi gidansu dan sanar da Mamansu. Huzeifa kuma na ganin abinda ta aikata ya ora hannaye biyu a kai ya walalo idanu yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna..." Juyawa yayi kan Sharhasila dake ysaye tana huci tana fa in "Gobe kya sake kula mijin wata, banza ar iska kar..." Marin da ya sauke mata yasa ta auke wuta duf! Daidai da shigowar anwarta ya sha i wuyanta da duka hannayenshi da iya arfinta yana fa in "Kin kasheta fa, kin kashe ar mutane Sharha, me ta mikiiiiii?" Duk da wuyar da take ji na sha ar da ya mata dan idanunta a waje suke, amma haka ta saki murmushi tace "Ka kasheni nima, ko ba komai na kashe aya daga cikin masu bibiyarka, ban da asara dan na mutu yanzu." Sakinta yayi a haukace ya sake juyawa kan Saleema da tuni jini ya wanke mata doguwar farar rigar da ta sako da hijabi tana kwance a kan teburin da take zaune tamkar gawa. Kafa unta ya kama yana jijjigta tare da kiran sunanta a haukace, a lokacin su Mama suka shigo a rikice ita da Fareeda. Tashin hankali bayin Allahn nan sun ganshi tsagwaronshi, yarinyar da mahaifinta bai ko