Sashe 48
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
game da Hadeeya wacce ke ri e da waya tana aukar hoto, harara ya watsa mata ya aue kai ita kuma ta yi saurin tare gabanshi, rai a jagule yace "Hadeeya kauce min a hanya?" Fari ta masa da idanu cike da salon shegantaka tace "Me ya kawoka? Ai ban ce ka zo ba ko?" Rai ace yace "Ke gusa min daga nan kafin na takaki. Ke ce za ki fa a min abinda zan yi?" Tsaki ya ja ya sake arin ra ata ya wuce ta sake tareshi, wayar hannunta ta nuna mishi tace "Ka ga ka saurare ko kuma wannan hoton yanzun nan ka ganshi a manhajar tik tok, ka san dai labari ne mai zafi? Kuma ka yi tunanin abinda zai iya faruwa." Da yanayin mamaki yace "Hadeeya, ar uwar ta ki? Za ki iya mata haka dama?" e baki tayi tace "Ita da take son rabani da kai fa, bata san ina sonka bane?" Girgiza kai yayi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Saboda ni yanzu sai ki tona mata asiri haka? Hadeeya har jikinta fa ya fito." Irin kallon nan qna kai ka sani, ka yi ka gama take kallonshi alamar dai ko oho! Ba alamar wasa yace "Kinga bani wayar nan." Da sauri ta ja baya tace "Ka wata mana." Sai kuma ta soka wayar a cikin aljihunta na bayan dogon wandon dake jikinta sannan ta juyo masa uwawunta tace "Ka auka mana, wurin ai ba ba onka bane." Rintse idanu yayi wata kunya ta kamashi, sai yake ji da fa bai fara mata iskanci ba da ba ta yarda ta masa haka ba, kenan ya zai yi yanzu? Bu a idanu yayi ya sauke numfashi yace "Yanzu me kike so?" Nunoshi tayi da yatsa tace "Kai, kai na ke so." Girgiza mata kai yayi yace "Me yasa kike sona? Jikina ko wani abun?" Kanne masa ido aya tayi tace "Duka ma..." Sai kuma ta aga masa gira tace "Kuma ma ai kai ka fara, ni ina sonka kuma zan aureka." Da yanayi na rarrashi yace "Hadeeya, ke yarinya ce, ba zan iya auren mai asa da shekara sha takwas ba, sannan ina son Yayarki da aure." Da yanayi na rashin wayo tace "To ka fasa aurenta mana, ni sai ka aureni." Ajiyar zuciya ya sauke ya sassauta murya yace "Hadeeya, ki goge hoton nan dan Allah, Saleema ba ta cancanci haka daga gareki ba, dan Allah Hadeeya." Harara ta wanka masa tace "Sai ka yi kuma, ni kaga tafiya tunda ba za ka yi abinda na ce ba." Da sauri ya taka afarshi zuwa gareta yace "Kinga Hadeeya..." Juyowa tayi tana kallonshi, a nutse yace "Kar kiyi komai dan Allah, ki bari zuwa gobe sai muyi magana." Murmushi ta masa tare da watso masa sumbata tace "Shikenan rabin rai." Shigewa tayi akinsu shi kuma ya an jim na wasu da u kafin ya nufi akin su Saleema, yana shigewa mai aikinsu da ke shirin shigowa falon tana tsaye ta ji komai kuma ta ga komai, da mamakin da ya so kasheta ta shigo ta aje jug in a inda ya dace ta juya zuciyarta cike da tunani. Tsaye yayi ofar akin bayan yayi sallama, sau biyu Safiya na fa a masa ya shigo, Saleema na jin haka ta tashi daga sallaya ta shige ban aki tana rintse idanunta, dan ra in jikinta aruwa yake ba raguwa ba, saida ya zauna kan kujerar dake daf da ofar shiga ita kuma tana zaune bakin gado suka gaisa, bayan gaisuwar kuma shiru ne ya biyo baya na wasu mintoci, numfasawa yayi cike da girmamawa ba tare daya kalli fuskarta ba yace "Mama, me ya faru haka? Me Saleema tai wa Abba?" ufule cikin acin ran dake ta azalzalarta kuma jiran dawowarshi gidan take ta amayar da abinda ke ranta tace "Fin arfi mana, daga yarinya ta nuna ga abinda take so ta yi shikenan sai ya rufe min a da duka, na gaji wallahi zai zo ya sameni gidan, na gaji da iyayyar da yake nuna mata." Shi kanshi Mu'az ya fahimci zuciya ce ta kai mata wuya, yau da gobe kuma sai Allah, a ladabce yace" A yi ha uri Mama, komai zai wuce." Sai kuma ya aga kanshi yace" Ina Saleema?" Nuna masa ofar ban akin tayi tace" Yanzu ta shiga ciki, ba ta son ka ganta ne a halin nan." Cike da tausayi yace" Mama ba ta bu atar ganin likita?" e abunda ya tokare mata ma ogwaro tayi tace" Nima na so mu tafi, amma ta ce ba ta jin komai." Ajiyar zuciyar ya sauke ya an yi shiru, da u ka an suka shu e ya mi e yana mata sallama, dan ya san Saleema ba zata yarda ta ganshi ba, har ya fita sai kuma Safiya ta bi ofar da kallo, a kan la anta ta furta" Amma wa ya fa a masa? Ya akayi ya sani?" auki wasu sakanni tana wannan tunanin ssai kuma ta share ta hanyar kiran Saleema ta fito daga ban akin, tana fitowa kan gado ta kwanta tana sauke numfashi idanunta na tara mata hawaye musamman hannunta da ya fi mata zugi. *Ardiya* na dawowa Hadeeya ta sanar da su abinda ya faru har da aukar hoton ta nuna musu, tsaki Ardiya tayi dan lokacin ba i maza ne a gidan sun zo kayan lefen Saleema, dan haka ita abun bai wani dameta ba kamar yadda kawo k ayan nan ya fi damunta, gashi irin kawowar nan aka yi hatta da Safiya ba wani an uwa nata dan ba wanda ya san a yau in za'a kawo. Ardiya ba ta ji ranta ua sake aci ba saida anen Alhaji Yusuf ya shigo da ku in da aka kawo ya nunawa iyayen mata dan su shaida tare da goro da kuma fa a musu an tsayar da rana sati hu u kawai garesu. Hadeeya na kan kujera gefe tana jin sanda basu ku in, harara ta dinga galla masa tana yatsina baki tana ayyana ina ma Saleema za ta yi wannan sa'ar, ai wannan milyoyin da ita suka dace ba Saleema ba. *Washe Gari* Kiran Hadeeya ne ya tasheshi a baccin da yake na farin cikin jiya an sake tabbatar masa da Saleema za ta zama tasa, tunda ya ga lambarta bai so auka ba da fari, saida ta sake kira na uku ka ai ya aga, bai ce mata uffan ba saida ita ta fara da "Ya yi kyau Yaya Mu'az, kaga kenan yanzu sai na tura wannan hoton kowa ya gani, tunda ba ka damu da wanda zasu ganta ba." Tashi zaune yayi da sauri yace "A'a dakata!" Gyara zamanshi ya arayi yace "Hadeeya, me kike nema ne gareni? Dan Allah ki fa amin abinda kike so, daga ku i, matsayi, aiki da sauransu, zan tsaya miki na ga kin samu, amma ban da maganar nan Hadeeya." Wata lalatacciyar dariya tayi tace "Yaya Mu'az, duka abin nan da ka zana iyayena za su iya tsaya min na sameshi, ba dole sai kai ne za ka tsaya min ba." Numfashi ya sauke yace "Shikenan, zan kiraki muyi magana." Da yanayi na raini tace "Ka ga ni fa ba sakara bace, jiya ma haka ka fa a min zamuyi magana, amma ba ka kirani ba bare muyi maganar, wallahi idan ka kuma shareni sai dai ka ga hoton tsiraicin matar da zaka aura a manhajar nan." if! Ta datse kiran shi kuma ya jefar da wayar ya shiga hautsina gashin kanshi kamar zai yi hauka, zuciyarsa abubuwa d dama take raya mishi game da yarinyar nan, ba tare da tsayar da abinda zai mata ba ya tashi ya shiga wanka. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:50 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _29_ Tun jiya Saleema ke lalla arta amma ta i ko kulata, yanzu haka ma da take zaune har yanzu jikinta kayan jiya ne, a tsanake ta kalleta da ladabi tace "Mama, dan ki manta da abun nan, Mama ni fa na masa laifi, bai kamata a ce na kai ararsa gun wani ba, shi fa mahaifina ne, dan Allah Mama ki daina hushi da shi, kinga fa bai dace ba sam, jiya sa in sa kikayi da shi." Wata uwar harara ta wurgo mata a kausashe tace" Ke! In zaki kama min bakinki ki kama min, in ba haka ba zan ha a dake, wato ke ko kishin kanki ma ba kya yi, ya dakeki kamar jaka amma kina bani ha uri, dan ya haifeki halittarki ya yi? Baiwarsa ce ke? To ba zai yiwu ba, na fa a masa sai ya sakeni na bar masa gidansa." A razane Saleema ta furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Mama saki?" Nunota tayi da yatsa tace" Kar ki kuma tanka min." Hawaye ne suka gangaro mata tace" Dan Allah Mama kar kiyi haka, Mama a kai..." Tattausar sallamar da ya yi tasa ta ha e sauran kalaman ta kalli ofar, jikinta har ari yake ta sadda kanta tace" Abba ina kwana." urawa fuskarta idanu yayi yana kallo, irin yansa fuskarta ta fa a lokaci aya, da irin taushin yarinyar gareshi, ha a sai a kanta ne yake sanin shi ma ubane, ba tare da wani ya tanka masa ba ya sauke ajiyar zuciya tare da kallon *rigimammiyar matarshi*, a rayuwarshi kaf bai ta a sanin haka ta iya masifa da tijara ba sai jiya, wai shi Safiya ta ma tsaye ta tara hannu sai ya saketa? To ya saketa shi kuwa ya shiga gidan uban wa a duniyar nan? Ai wallahi mutu ka raba takalmin kaza, mutuwa ce ka ai za ta rabashida Safiya, amma ko larura ta gidan duniya baya jin za ta iya sakashi rabuwa da ita. ara takowa yayi a nutse ba tare da ya amsa gaisuwar Saleema ba ya kalli Safiya yace "Maman Hajia ina kwana?" Kamar yadda tun shigowarshi ba ta aga kai ta kalleshi ba, haka yanzu ma kamar ba ta san yayi ba, wayarta kawai take ta latsawa, an kallon Saleema yayi da gefen idanu, hakan yasa ta saurin saukowa daga kan