Sashe 89
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ruhinta da gangar jikinta, ranki shi da e tunda nake aikin nan ban ta a cin karo da wanda ya gagareni ba, tunda nake a harkar nan ban ta a ganin wata halitta da ake ba wa kariyar yarinyar nan ba, sannan..." ufule tace " Ba wannan nake son ji ba malam, ta ina zamuyi nasara a kanta? Shi kawai nake son ji." Numfasawa yayi yace" Ranki shi da e a gaskiya ba wata dama daga yarinyar, sai sai dai akwai mafita." A da ile tace" Me ye mafitar?" orawa yayi da" Idan da zamu san abinda ke faruwa tsakaninta da sarki Abdus-samad, sannan mu samu zanin da suka kwanta a kanshi...ba wai kwanciya bacci ba, ina nufin zanen da sukayi mu'amular aure a kanshi, to zamu iya yin wani abu a kai, sannan..." Shirun da yayi yasa ta fa in" Sannan me?" orawa yayi da" Akwai rubutun da zan turo miki anjima a dinga sakawa shi sarki a abun sha, da sannu zamu sake samunshi, idan mun jaraba ta waccen angaren bamuyi basara ba, to ta angarenshi sai mu samu tazgaron da muke bu ata." Dogon numfashi taja tace "Duka abubuwan daka lissafa masu sau i ne gareni in dai bu ata za ta biya, saidai ina so ka bani tabbacin tasirin aikin, dan bana son tsaiko dayawa saboda rashin isashen lokaci." Cike da bata tabbacin da shi kanshi bai da tabbaci a kai yace "Ai wannan karan aikin nan idan muka samu nasara a kai bana tunanin ko mala'ika ya sakko daga sama zai iya gano bakin zaren (wal'iyazubillah), bare wata aramar yarinya da ko tafasa batayi ba bare ta one." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan, ka bani nan da gobe, zan sa a samo mana zanin gadon, dan na fa a maka yarinyar nan ba haka take zaune ba, a daren ranar da aka aura musu aure a ranar ya je gareta, shiyasa bana so muyi sanya." "In sha Allah ranki shi da e, zamu nuna mata mu a tafiye muka kwana." Da haka sukayi sallama ta aje wayar ta fito ta samu matashin nan da har yanzu yana zaune yana jiranta, tana fitowa ya ara rusunawa yana mata barka da fitowa, zaune tayi cike da gadara tana kallonshi ta yatsina fuska tace" Uhum, me ya faru?" ara sadda kanshi yayi yace "Ranki shi da e, Allah ya taimaki gimbiya, dama wani labari ne ke yafe dani." A ma oshi ta sake amsawa da "Uhum." orawa yayi da "Ranki shi da e akwai matsala, wannan sarauniyar za ta bamu matsala, dan kuwa nema take ta ruguza mana tsare-tsarenmu, yanzu haka daga madafa nake, kuma ita ce ta bu aci da mu je, ta kar e makullin hannuna na madafar ta ba wa Mariya, sannan ta ce ba za'a sake fiddawa mai martaba abinci, ita da kanta ce za ta dafa." Da sauri ta ago daga jinginar da tayi cikin aga sauti tace" Me? Ita ce ta fa i hakan?" Rusunawa yayi yace" Ita da kanta Allah ya ja zamaninki." Girgiza kai tayi tace" Ba zai yiwu ba, wacexe ita? Yaushe ta zo gidan da har aa ta nemi canza mana tsari?" Wani huci ta dinga saukewa tamkar ta yi gudu tace" Shikenan, gimbiya uwar mai gado ta san da maganar?" Girgiza kai yayi a hankali yace" Bana tunanin ta san da maganar." Jinjina kai tayi tace" Shikenan, ka je zan sake nemanka." a hannu ya mata jinjina irin ta sarakai kafin ya fita a falon. Ita ka ai ta dinga cika tana batsewa tana ayyana" Ina! Ba zai yiwu ba, wallahi arya kike, ni nan sai na sa ki zama tamkar hoto a gidan nan, ba iko shine burinki ba? To zai gagareki sai dai kiyi kallo." ______________ Saleema kuma na falonta aka ma mai inkin iso, asa ta zauna tana kwasar gaisuwa, saleema kuma duk sai ta ji ba da i yadda babbar mace ke gaisheta haka, jakadiyar ce ta nuna matar tace" Alkah ya taimaki *uwar magaji*, mai inkin matan fada kenan, gimbiya uwar mai martaba sarkina ce ta ce na mata iso zuwa nan dan ta aunaki, saboda za ta tafi da kayan inkinki." Gyara zamanta tayi a nutse tace" Shikenan, bismillah." A nutse matar ta mi e tana aje jakar dake rataye a kafa arta, mikewa Saleema ma tayi ta cire hijabin dake jikinta dan ta bata damar yin abinda ya kamata, sunkutawa tayi ta bu a jakar ta ciro al alami da aramin littafin da take rubuta awon sannan ta matso ri e da abun aunawa. Cikin nutsuwa ta dinga aunata tana rubutawa a littafin har ta kammala sannan ta kalleta a nutse tace "Ranki shi da e ko akwai irin kalar da kike so a miki?" Girgiza kai Saleema tayi tace "Ki yi kawai, ban da za Rusunawa tayi alamar girmamawa sannan ta shiga maida kayan a jakarta, cikin nutsuwa Saleema tace "Ko zan iya samun almakashi wurinki idan za ki sake dawowa?" Kallonta tayi sai kuma ta ciro na cikin jakarta tace "Ga wannan ranki shi da Girgiza kai tayi tace "A'a, wannan ai na aikinki ne, ki kawo min wani dai." Murmushi tayi tace "Ba komai wallahi, indai anfani zakuyi da shi ki ri a tayi tace "Nagode." Fita sukyi a falon jakadiyar ta mata rakiya har zuwa angaren Gimbiya Ramlat. akin baccinta ta shiga ta bu a drower kayanta sabi da aka zuba jiya bayan an nunawa iyayenta, wata kyakyawar atamfa ta auka ta dawo kan gado ta aje hijabinta, a hankali ta shiga warware zanin atamfar sannan ta auki almakashi ta fara yankawa, komai tana yi ne a nutse ba hayaniya, haka take abun ta wani sa'ilin sai ta tsaya ta zubawa atamfar idanu tana jin kamar fa ta manta yankan sai kuma ta yanka har ta samu ta yanka riga irin doguwar nan dake saukowa zuwa gwiwa, sai dai tana jin dole ta aje idan mai inkin nan ta sake dawowa sai ta bata ta duba mata, dan ta san dole a samu kurakurai duba da ko can ma ba ta kammala abinda ta fara ba aka samu matsala sannan yanzu haka rabon da ta ri e almakashi da sunan yanka shekara sama da uku kenan. *FADA* Sosai ya rintse idanu yana sauraren jawabin tsohon dake neman adalci ido rufe, ba tare da ya tsagaita da kukanshi ba ya ci gaba da fa in "Wannan ki e-ki en ba komai suke haddasa mana ba sai masifa, domin kuwa idan aka saka ki an nan mata suka fara rawa, ko kiran sallah basa ji bare su tuna kiran ubangijinsu, a matsayina na babba mai hankali yasa na musu maganar ya kamata a kashe haka kowa ya je yayi sallah, duba da su kansu mawa an maza ne majiya arfi, amma sun saka matayen mutane gaba suna kallo suna ti ar rawa, kawai yaran nan marasa mutumci suka dinga min ihu a kunne har wata fitsararriya ta dinga zagina wai ni magulmaci munafiki ina ruwana? arshe fa yarinyar nan jifana tayi da takalminta ta watsa min ruwan leda a jiki...tunda na ke ba'a ta a cin mutumcina irin haka ba sai yau, shiyasa na garzayo na zo wajen uba mai share kukanmu, baya goya marayu sarkin sarakuna sarki mai adalci, na san za'a auki mataki ko dan gaba." Wanda ke kusa da sarki Abdus-samad a tsaye ne yace" Sarki ya ji kokenka Baba, ka share hawayenka ka samu adalcin mai adalci." a idanunshi yayi da suka an canza launi, da yanayin acin rai sai dai a sanyaye sosai ya bu a muryarshi yace" A garin nan? A gari mai cike da dattawa? Shine za'a samu wannan fitsarar?... " Dakatawa yayi na sakwanni kafin ya ci gaba da cewa" Ba zamu lamunci wannan ba, ba za mu yarda alilan su ja mana hushin ubangijinmu ba, dan haka saga yau sai yau, ba maganar ana biki a ko ina ne a garin nan da kewaye a aza mana ki a..." Numfashi ya sauke kafin ya kalli wazirinsa dake zaune da an-galadima yace" Na oara alhakin hakan akan wuyanku, yau ba sai gobe ba a sanar a gidajen redio cewa wannan in umarnina, idan har muka kama wani ya taka mana doka, to ya kuka da kanshi." Liman dake zaune gefen damanshi ne yace" Allah ya taimakeka, Allah kara lafiya da nisan kwana, wannan shine daidai, dan lamarin nan yayi azantar da ba za ka so ganinta da idanuna ba, wasu shekaru da suka wuce fa wata wa a aka zo da ita, haka za ka ga idan ana bugata mata na cire zanin jikinsu suna musaya a tsakaninsu, wasu fa har wuntsilawa suke tamkar suna kan katifar iyayensu." Kallon liman in yayi a kausashe yace" A garin nan?" Sai kuma ya kalli an-galadima yace" Kana ina ake irin haka? Na auka kai ka dinga kula da harkokin da suka shafi masarauta tun bayan rasuwar mai martaba." Sunkuyar da kanshi yayi yana hararen liman ta asan idanu yace" Allah ya huci zuciyar sarkin sarakuna, Allah ja zamaninka lamarin..." aga masa hannu yayi yace" Dakata, a auki mataki akan lamarin, kuma kar ku auka ya wuce daga yanzu..." ara sautin muryarshi yayi yace" Zan bibiyi komai da kaina a lokacin da babu wanda yayi tsammani." Dogarin dake tsaye bayanshi ya ma alama ya matso kusanshi sosai ya rusuna, a tausashe yace" Duk wanda aka kama a gabatar min da shi, ni zan masa hukunci da kaina." Kirari aka shiga masa tamkar ba wani sai shi tare da ci wa tsohon nan albassa ana masa godiya aka masa izinin fita, a daddafe ya fita daga fadar yana mai godiyarsa a ransa da ka auki matakin da ya dace. *Cikin* gida kuma Saleema na gama aikin da ta saka kanta ta tattare kayan ta aje sannan ta kwashe yallayen ta zubar, ta juya za ta shiga ban akin kenan wayarta ta shiga ruri, dawowa tayi ta auka fuskarta auke da murmushi, a hankali ta zauna bakin gado kafin ta aga tayi shiru, gaba aya shiru ya ratsa wurin har saida ya cira la ansa yace mata "Barka." A nutse ta amsa da "Barka ranka shi da an gajeran tsaki yayi yace "Haba, a nan fa abinda ake ta kirana da shi kenan, a