Sashe 84
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya tura a kirata wai ta zo ta ga kayan da za'a kai gidansu tsinanniyar yarinyar da ita ta tabbata saida ta san yadda ta yi ta kwanta da shi daren jiya, duk da akwai angaren mahaifiyarshi tsakanin angarenshi da na ta, amma dake ba bacci tayi ba tana ta safa da marwa na tunanin abinda ke faruwa, saida kunnuwanta suka jiyo mata ihun yarinyar nan kfin a yan sakanni ta ji ihun tamkar na wanda aka rufewa baki ne. Gashi da ta shiga inda Saleemar take tare da jakadiya tana lindar mata jiki da garin musawul, yadda ta ga idanunta da kakkare jikinta da take, shine dan ya tabbatar mata da abinda take zargi ya ce ta zo ta gani, to ta gani kuma ta ji haushi sai me? In ma ba iskanci ba gudan kayan nan daga lefen zuwa kyautar da ya ce a bayar tamkar na wanda ya ratsa budurwa hu u a dare aya, hada wani banzar makullin mota daya ora a kai wai ita ma a cikin kyautar take. e kawai tayi ta kalli gimbiyar Ramlat tace "Kayan sunyi, Allah yasa albarka." Murmushi ta mata tace "Ameen, an gode." Kallon hadimar da zasu tafi kan kayan tayi tace "Zaku iya tafiya, idan kun je ku mi a mana gaisuwarmu, in sha Allah zan zo na gansu nima." A ladabce ta amsa kafin su mi e suna lailayar akwatunan da sauran kayayyakin na arzi i, kallon jakadiyar sarkin tayi wacce ta kawo sa on tana murmushi tace "Jakadiya, ki mi a godiyarmu ga sarki, sarauniya Saleema na godiya." Amsawa tayi ita ma kafin ta fita a falon, gyara zama gimbiya Ramlat tayi tana murmushi a oye zuciyarta cike da matsanancin farin cikin da ita kanta bata san adadinshi ba, a yanzu dai kam babu abinda za ta ce da ubangiji sai godiya. *Alhamdulillah.* 20/06/2022 22:07 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _45_ Wato kowane a da kalar nasa arzi in, yanzu kam ya fahimci haka duba da abubuwan da suka dinga faruwa da ya kamata a ce sun zamar masa darasi na rayuwa, alkairin duniya da jawo masa martaba yarinyar nan ce ta yi, yayin da wa anda yake dauka nashi ne saboda bokonsu ya kasa samun ko da girmamawar da uba ya dace ya samu a wajen ansa, yanzu da yake tsaye kan kayan da aka kawo daga fadar mai mara awa, rabi na lefen arsa rabi kuma ko da ba'a fa a masa ba shi yasan saboda ya samu arsa a yadda ya dace ne ya masa wannan kyautar karramawa, wanda bai ta a samu daga mazan sauran an uwan ba, su kan zo dai suyi godiya idan gari ya wayewa shila ya san dan al'ada ce ta zo da hakan. Tsakin da Ardiya tayi ta mi e ne yasa shi kallonta ya ta e baki yace "Mai ba in ciki saidai ya mutu, amma ko farawa baiyi ba, dan ba zaka san harkar ta girma ba ce sai randa *uwata ta haifi magajin masarauta*." Dakatawa tayi ta kalleshi tace "Me kake nufi Alhaji? ar ba in ciki ce ni?" A da ile yace "Kin ji na fa a? Na miki magana ne nan?" Harara ta dallo masa tace "Wallahi ban ga abinda za ku samu dalilin Saleema ba na muku ba in ciki, yo ina abun yake?" Murmushi yayi yace "Alhamdulillah kawai zan ce." Girgiza kai tayi cike da takaici tace "Ni fa Alhaji na kasa gane maka, tun jiya kake wani wula antani, saboda ka yaudare ni ne? Ko dan arka ta auri sarki?" Fashewa yayi da dariya yace "Yaudara? Yaudara fa kika ce? Ta me?" A hassale tace "Nan fa akin muka gama magana da kai akan ar uwata na sonta da aure, tsaf muka gama magana da kai, amma da ka tashi me kayi? Kawai sai muji aurenta, ai wannan ba halin babba na gari bane." Cike da shegantaka yace "Ai kinsan an ce gaba da gabanta aljani ya taka wuta, idan ana babbar gwiwa wa ya fa a miki ana jiyo aurin zomo? Sawun gwiwa ne ya take na ra umi Hajiata, shiyasa na ba wa ata ra umi a sahara, ba an tsako ba." Ta cika ta cika sosai, tsabar hassala irjinta har wani sama ya fara yi, juyawa tayi idanunta na sako wallar takaici ta juya ta bar masa falon, dan dama ta zo ne kamar yadda suka bu aceta dan kar ta ce na zata ao ba a ce hassada take, amma a yanzu kam ta san mutanen nan sun mata nisan da ba fa za ta kamosu ba, a gaskiya lamarin nan bai mata ba kuma ji take tamkar ta kashesu ko ta huta. Shigowar Safiya akin ta gama sallamar ba in da suka zo ganin kayan arzi in nan yasa shi sakin murmushi, da gaske gurfanawa yayi a gabanta sanda tayi zaune tana fa in "Abban Hajia ka ga kayan ko?" Tamkar wani bawa a gaban uwargijiyarsa haka ya rusuna gabanta cike da tsokana yana dariya yace "Na gani ranki shi da e, uwa ga matar sarkin mara awa, suruka ga mai mara awa, Allah dai ya ja zamaninki Hajjajuuna." Tintsirewa tayi da dariya ta kamo hannunshi tace "Abban Hajia, ashe haka ka uya fadanci kaima?" Kallonta yayi yana murmushi yace "Tun fa tsohon sarki yana da rai muna kai masa caffa a gida, kinga dole mu iya, kuma jiya ma ai mun je muka kai wa sabon sarki gaisuwarmu, duk da dai ban sani ba, amma ni haka na dinga hura hanci a matsayina na surukin mai gado." Dariya kawai Safiya take har ya koma kusanta ya zauna tana kallonshi tace" A gaskiya jiya ka aga min hankalina a gidan nan, gabadaya fa na yarda cewa wannan yaron ka aurata mata." Murmushi yayi yana shafa gemunshi yace" Ni kaina har muka gama gaisawa da su ban san su wa ye ba, saida suka gabatar min da su sannan na fahimta, da suka zo min da lamarin nan rasa nutsuwata nayi, wai yarima Abdus-samad da mahaifiyarsa na ro on irina a wajena a basu auren *Haleematu*, baiyi dogon tunani ba na amince dan ban ga abun takaici a ciki ba." A hankali ta kwantar da kanta a kafa arshi tace" Yanzu tana can ta wayi gari a ba on wuri, sabuwar rayuwa da sabon wuri, na san jiya ta farka dan yin fitsari, amma ban san ya ta yi ba? Dan na san dai mai martaba ai ba zai rakata ban aki ba." Dariya yayi yana girgiza kai yace" Wannan ar taki da baiwarta ta kasanxe ta musamman, kar ki ji mamaki idan na ce miki sarkinmu yayi tsaye ofar ban aki yauin da take ciki tana biyan bu atarta." Dariya ita ma tayi tace" Haba dai Abban Hajia, kar ka zuzuta lamarin arka mana." Dariya yayi shima yace" Da gaske nake miki Hajiata." Cike da nisha i suke zanta lamarin arsu da sabuwar rayuwar sa za ta tsinci kanta a ciki mai tattare da alubale da fitittinu, saidai su fi mata fatan farin ciki fiye da ba in cikin da zai iya ziyartarta wasu lokuta. _______________ Yarinyar da ta turo a aukar mata yaron ya kalla fuskarshi a ha e yace "Ke sakeshi." Sakin hannunshi tayi tana kumburo baki ta juya ta fita a shagon, da harara ya bi yarinyar sannan ya kalli *Sudais* in yace "Koma ka zauna." Zaune yayi yana kallon Baban na shi yana lasar alewar hannunshi, ba jimawa Mubarak dake hangen titi ya kalleshi yace "Yaya Huzeifa, gata nan fa ta zo da kanta." Va tare daya kalleshi ba yace "Barta ta zo, yau za ta ga haukan da ya fi na ta." Sharhasila na shigowa ba sallama ta kama hannun Sudais tace "Muje." Wani mugun kallo ya watsa mata a ufule yace "Sakeshi Sharha, wallahi a ane nake yau kuma kanki zan huce kika min hauka, ba gidan uban da zai je." Da mamaki ta kalleshi tace "Zagi fa ka yi Abban Sudais, lafiyarka kuwa?" Mubarak ne yace "Ina fa lafiya, yarinyar da kikayi sanadin rabashi da ita ta aure mana sarki, ganinta ma yanzu wuya zai mana, kuma duk ke ce sila." Nunashi tayi tace "Ka ga ba da kai nake magana ba, kuma na ji da i da hakan ta faru, ka ga ai sai ya cire rai yanzu, dan inuwarta m..." Mari ya wankawa fuskarta, marin da tun waccen lokacin ya so kifa mata shi amma bai samu dama ba, ya yanzun nan ya samu labari a wajen Fareeda da sukayi waya cewa ita sai yau ta samu damar zuwa gidansu Saleema, a nan ta ga kayan arzikin da aka turo daga fada, kuma ta zo tana neman yi masa hauka? A razane ta kalleshi dafe da kuncinta tace "Ka mareni?" arin fitowa daga tsakanin telar da kujerar yayi yana fa in "Bari ma ki gani." Tsaye tayi ba ta gusa ba shi kuma so yayi ta fice a shagon, amma saita saki hannun Sudais ta gyara tsayuwarta tace "Babu indazan je saidai ka kasheni, Huzeifa dan na nuna ina sonka ne kake wula antani, to wallahi ko kana so ko baka so sai ka maidani akina, idan ba haka ba na dinga hanaka kwanciyar hankali kenan, kuma kai baka isa ka ce wannan ba anmu bane ni da kai." Da yatsa ya nunata yace" Mafarkinki kenan a kaina, shiyasa za ki are rayuwarki a gantali, ke kenan kullum yawon biki da aiki, an gaya miki kare ne ya cijeni da zan sake maidaki, da me kika areni a zamanmu na farko?" Cikin kukan ba in ciki tace" Wallahi ka ji tsoron Allah, yanzu ni ce zaka ce ban are ka da komai ba?" A harzu e yace" Na fa arya nayi." Kamo hannun Sudais yayi sannan yace" Wuce ki bar nan shagon." Jinjina kai tayi tace" San fita, amma wallahi sai na dawo, kuma a dai ni na haifi abuna, dan haka ba zaka rabani da shi ba." Hararenta yayi yqce" Kika dawo karyaki zanyi." Murgu a masa baki tayi tace" Ka karyani in, ai