Sashe 67
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
alamar e, harara Ardiya ta wurga masa ta mi e cike da jin haushi ta kalleshi tace "Alhaji zamu iya yin magana?" Kallonta yayi sai kuma ya kalli Safiya, tashi tsaye yayi yana fa in "Ina zuwa Maman biyu." Fitaa tayi ya rufa mata baya yana jin shi fa takura masa take so ta yi, Allah Allah yake yammar nan tayi a yi aikin nan cikin nasara ya ga baiwar Allahn can ta samu lafiya, kai shi fa bai ma ta a sanin haka yake son Safiya ba saida cikin nan ya canza mata halittarta gaba aya, wani tausayinta ke awainiya da shi kullum, baya son gusawa nan da can sai ya ga kamar wani abu zai faru da ita. Lubna dake akin kallon anwar mahaifiyarsu tayi da ita tana dai zaune ne akin amma kunyar Alhajin take ji tace "Ikon Allah, mata tayi ta gatsinar fuska tamkar tana gaban kashi." e bakin anwar mahaifiyarsu tayi wacce ita ta rage musu a wanda dai zasu iya kira na iyayensu tace "Ita ta sani, in sha Allah Safiya lafiya za ta haihu." "Allah yasa." Lubna ta fa a suna kallon Saleema da ta zauna kusa da Mamanta tace "Mama na kawo miki madara?" Girgiza mata kai kawai tayi, a shafwa e Saleema ta ora kanta a kafa ar Safiyar dan kuka ke son kwace mata, halin da Mamanta take yana bata tausayi sosai, ita ma a asibitin take kwana dan ba za ta iya zama a gidan ba babu mamanta, ri o hannun Safiyar tayi tana murzawa tana fa in "Allah ya baki lafiya Mamana, in sha Allah za'ayi aikin nan lafiya." Murmushi kawai Safiya tayi ita dai tana zaune kan gadon afafunta na asa, zaman ma ba da inshi take ji ba bare kuma kwanciya. Shigowa Alhaji Yusuf yayi da alamar acin rai tare da shi, wanda Ardiya ce ta unsa masa wai wula antata yake ko gidan ma baya zuwa, ya so kwatanta mata a tsanake ar uwarta na bu atar kulawarshi, amma har take masa tsaki tace wai idan yana so su dawwama a asibitin sannan ta juya ta barshi, shi ga sakarai ba? Kusan Saleema ya tsaya a sanyaye yace "Wai ke baki ga halin da take ciki bane za ki wani hayeta?" Kamar jira take a mata magana kawai ta tusa kanta a kafa ar Mamanta ta fashe da kuka, tsugunno yayi irin na maza ya ri o hannun Saleema yace "Haba Hajia, saboda Allah me ye irin haka yanzu? Ni ne kike so kiga ina kuka?" Girgiza kai tayi amma ba ta daina kukan ba, ganin yadda take turmusa kanta a jikin Safiya kamar ma nema take tayi kwance yasa shi juyawa ya kalli Lub'a dake fa in "Saleema kiyi ha uri mana, ki mata addu'a kinji." Zaune yayi inda ya tashi azun ya jawo hannun Saleema ya zaunar da ita kusa da shi, karo na farko a rayuwar ta da dai wayonta da haka ta faru, kanta da ya jawo ya ora a irjinshi yana shafa kanta yana fa in" Shikena to Hajajjuna ya isa, ki yi ta mata addu'a kinji, ba fa abinda zai sameta in sha Allah, aiki ne kawai za'a mata a ciro miki aninki, ba kina so ki ganshi ba?" Cikin shashe ar kuka ta rufe fuskarta da hannu tana jin kunyar yau ita ce jikin Abbansu, aga kai tayi alamar e, murmushi ya saki mai sauti yace" To kula shine zakiyi kuka? Ke dai ki jira ta haihu lafiya ki gani, har ku i zan baki masu yawa kiyi biki kema, ki tara awayenki ki gwangwaza shagalin da har a tv sai anyi labarinshi, kinji ko Baby." Shashe ar da take saukewa yasa dariyar da ta saki ta fito cikin sigar da ta sa duka akin suka kwashe da dariya, anwar Mamansu Safiya kam tashi tayi ta fita dan ita gaskiya bata son rayuwar nan ta Alhaji Yusf da babu kunya a ciki, yo har ina za ta iya da wannan ita? Cikin farin ciki aka fito musu da santalelen yaron da aka ciro bayan aiki cikin nasara, riga-riga ake wajen kar anshi tsakanin Saleema da mahaifinta da saida yayi sujada ga Allah da wannan babbar kyauta, tunda ya ora idanunshi a kan yaron wasu hawayen farin ciki suka lullu eshi, sumbatar yaron ya shiga yi kafin ya kalli Saleema da sigar tsokana yace "Hajiata sai dai kiyi ha uri, amma daga yau na yayeki ni dai, bayan shekara sha takwas an miki ane, lallai ke * ar baiwa ce*." Dariya tayi a ranta tana ayyana "Dama ni ar Mamana ce, na san ai ba za ta yayeni ba ita." i dai ba wata tsiya ba Alhaji Yusuf kashesu yake dalilin wannan aruwa da ya samu, wanda hakan ke ona zuciyar Ardiya ka rantse ita ke bashi ku in, saida sukayi kwana biyar a asibiti kafin a sallameta jikinta yayi sau i sosai, nan suka koma gida ana jego mai cike da nutsuwa, inda Saleema ta zama tamkar ita ma kishiyar Safiyar ce, san kuwa uta ke tsaye kan girkin gidan, dan takaici yasa Ardiya ara sammakon zuwa wajen aikinta, bata dawowa sai bayan magariba, idan ka ga ta le a wajen mai jego to dare ne yayi ba kowa a lokacin. Ba wanda ya damu da tsiyarta tunda ba abinda aka ce dole sai ita za ta yi, kamar yadda babu wanda ya damu hakan, dan iya kulawar da Saleema ma ke bawa Mamanta ka ai ya isheta ta rayu cikin aminci. Dan kuwa takanas Saleema ta auki hutun zuwa wajen koyon inkinta, sai Fareeda da ta zo ganin jariri tare da Mamanta. *Alhamdulillah.* 13/06/2022 17:25 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _37_ Zaro idanu Safiya tayi ta shiga aga afafunta da sauri tana fa in "Na shiga uku ni Safiya! Saleema wa ya sa ki yi mishi wanka? Ko ni kinga ina mishi?" Saleema kam da ta ta are ta wala yaron a cikin robar wanka da ruwan masu umi murmushi tayi tace "Mama na iya fa, gani nayi Mama Bilki tana wani aiki ke kuma kina wanka, kuma har mutane sun fara zuwa." Tsaye tayi tana kallo, kuma wallahi wankan take masa ta tallabe yaron da hannu aya tana goga mishi lallausan sosonshi da sabulu a jiki, sala sala take bi tana wanke mishi ko ina, da mamaki ta yi zaune kan gado tace" Wa ya koya miki Saleema? Ni fa ban iya ba wallahi, ko ke dana haifeki sai da kika fara zama na fara miki wanka." Dariya tayi tace" Abinda gabana Mama Bilki ke mishi, kullum ina so inyi dan nasan hanani zakuyi ai, Mama ba wuya fa." Shigowar Mama Bilki ne yasa ta ita ma rarako ido ta taho a guje tana fa in" Sallalahu alaihi wa sallam! Safiya kina kallo?" Dariya tayi tace" Mama ki barta ta iya fa." Dakatawa dattijuwar tayi sai ta ga kuma babu kuskure, ri e ha a tayi tace" Ikon Allah, tun kina budurwa kin iya wanka jariri? Lallai." Ba ta kulasu ba sai aga yaron da tayi daga cikin ruwa ta auki lallausan towel inshi ta na eshi ciki, bushe masa kunnuwa da idanu tayi kafin tayi zauna gaban garwashin da Mama Bilki ta zauna tana jiran ta mi a mata yaron, saidai da kanta ta dinga ora hannunta bakin kaskon idan yayi zafi saita danna masa cibiyarsa wacce ta fita kwana biyu kenan, haka ta dinga tausa mishi jikinshi da umin wutar nan, hatta da kwalli da mai saida ta shafawa yaron sannan ta saka mishi pempers wacce dama ita ke saka mishi kullum dan Mama Bilki ta ce iya ba ta iya alla wannan jaraba ba. Tsaf ta fito da anenta cikin shirin riga da wando na kanti masu kyau ta shafa mishi turare na su na jarirai sannan ta mi e ta bawa Mamanta shi tace "A bashi yasha." Juyawa tayi ta shige ban aki ita ma dan yin wanka yau suna, da kallo Safiya ta bita tana murmushi, uta ka ai ta san me take hangowa a tare da arta, idan ta ce arta za ta zama abar alfahari babbar mace nan gaba za'a iya cewa dan ita ta haifeta, amma ita ka ai ta san me take gani a tare da ita, tana ji a jikinta za ta taka matsayin da ba lallai a samu mai kwatankwacin irinshi a danginta ba dana Babanta. An gudanar da biki cikin farin ciki da kwanciyar hankali, yaro ya ci sunan *Ahmad* sai fatan Allah ya raya kan sunna. Kwana biyu da yin biki Saleema ta koma bakin aikinta, ma'ana Fareeda ta ci gaba da zuwa tana koya mata abinda ta iya, ranar Lahadi kuma sai ta je ga Huzeifa dan orawa, sai dai ta canza lokacin tafiya daga zuwan safiya da take, dan yanzu sai ta kai azahar bata tafi ba, kuma hakan ya faru ne sakamakon Abbansu da ya daina baccin safe, yana ida sallar asuba zai zo akin ya auki Ahmad, haka rana zata fito suna ta shawagi a farfajiyar shi da yaron da tsabar sha uwa har kamar ya fi yarda da mahaifin fiye da uwar. A haka watarana Huzeifa ya ma Saleema hanyar da ta samu gurbi a wajen wani katafaren koyar da inki, wanda a shekara sau aya mamallakin gurin ke zuwa daga Niamey yana duba sauran jahohin, ana yaye wasu a lokacin ana kuma aukar wasu, a haka Saleema aka bata gurbin zama na sati biyu, dan zamansu a ajin farko kaf ta amsa tambayoyin da babban ma inkin ya mata tare da nuna mishi a aikace, hakan yasa ya ce abinda zata koya ba bu atar jimawa dan dama ba haka suke so ba saboda gudun matsala. A lokacin saida ta nemi izini gurin mahaifinta kan tana son zuwa gidan aunty Lubna saboda bikin arta da ya tashi, bai hanata ba dan ya yarda bikin ne zai kaita gidan, hakan ya bata damar kwashe kwana goma cir tana abinda ya dace, ba aramin farin ciki ta ke da kasancewar hakan ba, duk da tana jin ba da i