← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 116

Sashe 45

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abinda kika aikata ba da sanina ba ban auki mataki a kanki ba, shi ne yanzu za ki zo min da maganar banza?" Gyara tsayuwa yayi cike da bata tabbaci yace "To bari ki ji, wallahi idan kika ara maganar inki a gidan nan, ba ke ka ai ba har mahifiyarki sai ta gane shayi tsurar ruwa ne." A mugun tsawace yace "Tashi ki bani wuri." A zabure ta mi e da sauri za ta bar akin, muryarsa ce ta sake dakar kunnuwanta yana fa in "Aurenki nan da wata aya, kuma zan tabbatar shi kanshi Mu'az in bai barki kin zubar mana da mutumcinmu ba ta hanyar fara inki." Kuka ne ya wace mata da ya sakata rufe bakinta ta juya da gudu ta koma aki inda ta baro Mamanta, tana shiga ta fa a kan gadon kusa da Mamanta, Safiya dake zaune da carbinta a hannu tana ja ta kalleta ta ta e baki tace" Da na fa a miki wahalar banza za ki yi ba ki yarda ba, mahaifinki ba mutane ne da ake shawo kansu ta sau i ba, ki ma ha ura in za ki ha ura, ni baki ganni ba? Sha'awar abincin siyarwa nake, har an uwana ya sa ma min aiki a wani gurin cin abinci da zan dinga yi musu sinasir da wainar shinkafa, a gida zan yi su zo su auka su bani ku ina, amma haka ya ba awa idanunshi toka ya ce ba da shi za'a yi wannan zubar da mutumcin ba." Da sigar tambaya tace" Da ya nuna baya so me kika ga na yi? Ha ura na yi ya ce shi zai dinga bani albashi duk wata, kuma gashi yana bani sai in mantuwa ya yi, ke ma ki auki hakan a matsayin addarki, idan kikayi aurenki wata ila Mu'az ya taimaka miki." Sai lokacin ta ago kanta tana ta shashe a tamkar za ta mutu tace" Mama Abba fa cewa ya yi wai har Yaya Mu'az in zai fa a masa kar ya saki ya taimake ni saboda zubar da mutumcinsu ne, Mama me yasa Abba baya so na? Na auka na yi abinda zai yi alfahari da ni, amma har yay bakinshi bai iya nuna min irin arin da na yi ba, me yasa?" Shiru Safiya tayi ta ci gaba da carbinta dan in ta ce za ta yi magana za ta iya yin kuka ita ma, dan gaskiya ba ta jin da i ha uri kawai take. Ta na laziminta wata dabarar ta fa o mata, da sauri ta kalli Saleema da ta sake maida kanta asa tana kuka tace "Kinga tashi zaune, ki saurareni." A sa ule ta tashi zaune tana ta sharar hawaye, cikin nutsuwa Safiya tace "Kina ji, mahaifinki yana ganin girman surukinki wato Alhaji Auwal, ki kirasa ko ki je gidan ki fa a masa, na tabbata idan shi ne ya masa magana zai barki ki yi abinda ranki ya ke so." Da sauri ta fara share hawayen inda fara'a ta maye fuskarta sa anin yanzun da take kuka tace" Hakane fa Mama, ban yi wannan tunanin ba, kuma kinga ko da ma ba zai yarda ba hakan zai bani damar na fara koya bayan aurenmu." Murmushi Safiya tayi tace" Ni ma yanzu tunanin ya zo min, Allah ya bada sa'a." "Ameen." Ta fa a tana sauka daga kan gadon ta nufi inda ta li a wayarta caji, da mamaki Mamanta ta kalleta tace "Ba dai yanzu za ki kirashi ba?" A shagwa e tace "E mana Mama, da gaggawa ai ya fi." Da alamar nusarwa tace "Amma kinsan da gaggawa aikin she an ne, ki bari zuwa yamma ko dare lokacin yana gida, amma yanzu na san duk inda yake yana wata sabgar." Cike da rashin jin da i ta jinjina kai ta cire hijabinta ta jefo kan gado sannan ta zo ta zauna, sai take jin kamar ta aga hannu sama ta yi addu'ar Allah ya kawo yammar nan yanzu dan ta kira Alhaji Auwal wanda zuciyarta ke raya mata tabbas yanzun kam Abbanta zai amince dan baya tsallake maganar mai gidan na sa kuma amini ta wata fuskar. ______________ Shigowarshi akin kenan daga wanka yana son fita kunnuwanshi suka jiyo mishi abinda sam bai auka a shekaru da ilimi irin na Sharha za ta aikata haka ba, da kunnuwanshi ya ji tana fa a ma awarta da bakinta cewa "Ai awata ki bari kawai, jiya na ara son mijina fiye da yadda kike tunani, ashe wannan shiru shirun da sanyin nan kamar marar lakka ha e da gemun nan irin na ustazai, ashe dai kayan aiki ne a cikin tattausar suffar nan." Dariya tayi na wasu da u kafin tace"Ai babu wata ar buru... Da za ta sake kallon mijina na yaleta, yadda na san shi in..." Dizge wayar da aka yi daga kunnenta yasa ta mi ewa tsaye da sauri tana kallonshi, da fari bala'i ta so rufeshi da shi, amma da ta ga fuskarshi a matu ar ha e ga tsantsar acin rai data hango shinfi e a fuskarshi, sai ta ha e na ta acin ran tace" Baby ya dai?" wala wayar yayi kan gado ya jaye aramin towel in dake rataye a wuyanshi, a hssale sosai ya cikin aga murya yace" Sharha me ye haka? Wane wane irin dabbaci ne haka? Da girmanki da wayonki za ki zauna kina fa awa awarki sirrina, ni? Ni za ki tonawa asiri?" Rarraba idanu ta fara yi tana neman kare kanta da fa in "Baby... Ba fa...haka...ba ka gan.." "Kinga." Ya fa a yana nunota da yatsa, cikin kakkasar murya ya ora da "Sharhasila kin jima kina min abubuwa na son ranki amma ina aga miki afa, bango ne bana so ki kaini da zai sa ki ga kalata, idan banzayen uminki zakiyi to kiyi iya kanki, amma wallahi kika kuma fa awa wata awarki sirrina Sharhasila sai na miki haukan da ya fi na ki." Zazzaro idanu tayi da mamakin yadda salihin mijinta ke neman riki e mata ya zama wani abun tsoro, har asan zuciyarta ta ji wani abu mai kama da tsoronshi ya arsu tare da sassauta muryarta tace" Baby ka yi ha uri dan Allah ba zan sake ba." Harara ya watsa mata ya ra a ya arasa gaban madubi zai shafa mai, arasa tayi ta rumgumoshi ta baya tana fa in" Na ce ka yi ha uri ko? Wallahi ba zan sake ba." an gajeran tsaki ya ja ya areta daga jikinshi, turo baki tayi ta fara bubbuga afafunta asa tace" A'a, na ce ka yi ha uri ko, ba zan sake ba Baby." A ta aice ya amsa da" Na ji." Da kallo ta dinga bin tattausan jikinshi da kallo, duk da ba ya da mur iyar sura, amma a haka yake da zarrar da ya tsorata alwashin da ta ci a kanshi, hakan ya sa ta ara jinshi asan ranta, dan kuwa ta san mijinta namiji ne da za'a iya wawarsa, dan haka za ta yi iya arinta wajen ganin ta ri e abunta hannu bibbiyu. Har ya gama shiri zai fita fuskarshi a ha e a take, sake bin bayanshi tayi ganin zai fice dan sake bashi ha uri, dan ita fa akwai abubuwa dayawa da take so ta orashi a kai, a yadda kuma ta ga take-takenshi ta san dole sai sun kai ruwa rana kafin ya dinga yin abinda take so, dan ko cikin kayan gara har da makullin mota mahaifinta ya bashi amma ya ce sam ba zai kar a ba, yanzu haka gidan da suke ciki saida mahaifiyarshi ta sa baki sannan ya amince zai zauna, shi ma a haka ya yi al awarin harkar da ya saka gaba tana yin kyau zai canza musu gida. o hannunshi tayi kamar za ta fashe da kuka tace "Dan Allah ka yi hakuri ka saki ranka, haba Baby ha uri fa nake ta baka, ta ya kana ago za ka fita haka fuskarka a murtuke, ai sai ka sa a zageni a ce kamata mijinta ya fita ba farin ciki." Numfashi ya dinga saukexa har guda uku kafin ya kalli fuskarta, a hankali ya tallabo fuskarta a manna mata sumbata a goshi kafin yace" Komai ya wuce, amma ki kiyaye dan Allah, hakan babu kyau, ki sani daga sanda zamu shigo akin nan ni da ke mu rufe, duk wani abu da zai faru a nan to shine sirri, ko da kuwa ata miki rai nayi idan kina da hankali zaki barshi a matsayin sirrinmu, bare kuma wannan lamari, ke ba kya tsoron ki fassarceni a wajen awayenki wata ta ji tana son aurena saboda wannan abu? Ni kuma kinga duk wacce za ta min tayin aurenta ba zan i ba tunda ke kika ja." Takwaf takwaf tayi da fuska irin iris take jira ta fashe da kuka tace" Baby, ka daina ha a kanka da wata, wallahi duk wacce ta kwatanta haka ko? Sai na zazzaga mata fetur na ona yarinya da ranta, Baby zan iya yin komai a kanka." Ajiyar zuciya ya sauke ya girgiza mata kai yace" Sharhasila bana son zafafa kishin nan, mace kike kuma rayuwa marar tabbas ce, ba mu da ikon tafiyar da rayuwarmu yanda muke so, kamar yadda addararmu ba'a hannunmu take ba, bamu san me Allah ya hukunta mana a gaba ba, musulma ce ke Sharhasila wacce ta yi imani da adda mai kyau ko akasin haka, ki dinga sa wa zuciyarki ruwan sanyi, kin ji *tawa*?" A sanyaye ta jinjina masa kai alamar to sannan tace" Baby yanzu tunda mun yi aure ka min al awarin zama nawa ni ka ai mana." Tsurawa fuskarta idanu yayi yana kallo tare da zurfafa tunani akan amsar da zai bata, murmushi ya mata dan kwantar da hankalinta ya rugumota sannan yace" Ina fata na ci gaba da zama naki ke ka ai, kamar yanda a yanzu nima fatana bai wuce ki ci gaba da zama tawa ba, ina sonki amaryata." Wani masifaffen farin ciki ne ya rufeta daya sata matseshi sosai tana sauke numfashi a hankali, a nutse kaikaita ya ora la anshi daidai kunnenta na dama ya ra a mata" Ki fa a min sirrin nan mana na jiya
Chapter 45 · 0% Book details