← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 116

Sashe 74

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yadda ta nuna ana ta addu'a ta san an yi mishi, sai dai ita fa ya inta akan addu'o'in dabam yake, dan hadisi ne ingantacce daga bakin fiyayyen halitta, ta tabbata idan aka yi da gasgatawa za'a samu biyan bu ata, dan haka kar ta fa a a ce an yi, sai kawai cikin ladabi tace "Ranki shi da e, dama ruwan addu'a ne ban so ko kuna da bu ata ba?" Da hanzari Hajia Ramlat tace "Saleema me zai hana? Kin kuwa san irin tashin hankalin da nake ciki game da wannan matsalar? Saleema ina so, ko da kina so a tura a kar a ne saina tura, tunda kin ce ke ba kya fita." Jinjina kai tayi tace "Shinkenan ranki shi da e, a turo in." Da farin ciki suka rabu inda Saleema ta koma aki da sauri, robobin zam-zam guda shida ta auko dan dama ita ma tana aiki dasu ta juyesu a kofi sannan ta auro alwala ta yi sallah raka'a biyu, daga amanar-rasul zuwa ayatul kursiy, suratul jin da fala da nas, duka saida ta karanta kafin ta shiga karanta addu'o'in da duk ta san an ce daga bakin fiyayuen halitta suke kuma suna magani, tana gamawa ta mi e ta auko wani kofin kwalba mai murfi ta juye ruwan a ciki ta ri e da hannaye biyu tana kallon kanta a madubi, lumshe idanu tayi fuskarta auke da murmushi tace "Na yi ne da sanin cewa ka ji ni, Allah kaine Allah, dan girman mulkinka, dan tsarkin zatinka, dan udura da buwayarka, Allah ka aukewa wannan bawa naka duka larurarshi, kai ne Allah, kuma kai kace mu ro eka zaka amsa mana, Ya Rahman, ya Jabbar, ya Mutakabbir, Ya Razza , ya ahhar, ya Hayyu, ya ayyum, ya Wahhab, Allah dan tsarkin sunayen nan naka na aukaka da isa, Allah ka biya mana bu atunmu na alkairi." _"Ameeeen ya Hayyu ya Qayyum."_ Shigowar Hamdeeya akin ne yasa ta juyowa tace" Wai ki zo kin yi ba "Uhum!" Ta fa a tana kama hanyar fita dan dama da hijabinta a jikinta, tana zuwa farfajiyar gidan ta samu dattijon da shigarshi ta sassau an yadi marar nauyi, gaisawa sukayi a mutumce da ladabi kafin ta mi a masa ledar auke mai kofunan tace "Gashi Baba, a bashi yasha da bismillah tare da mafi girman ya ini, sannan a shafa masa a jikinsa in sha Allah komai zai yaye, gobe ma a sake bashi yasha tare da shafa masa, haka har a masa na kwana ukun, idan an ga sauyi sai a ci gaba in sha Allah." Shi dai tunda gimbiya ta turo shi nan yake ganin yarinyar mai mahimmanci ce a garesu, dan haka ya kar a da alamun rusunawa yace" An gama ranki shi da e, Allah ya amince." Murmushi ta masa tace" Ameen, a gaida ranki shi da e." Juyawa tayi ta koma ciki shima ya fice, Ardiya na ganin ta taho ta fito daga bayan ofar da take le asu tana dariya, saida Saleema ta zo zata shige ta kalleta sama da asa tace" Yanzu kuma Saleema da tsofaffi kika koma soyayya? Lallai ta are miki." ala ba ta ce mata ba ta wuce ciki kallo aya kawai ta mata, ita kuma ta e baki tayi tana sake murmushi tace" Shi ma sai na tabbatar ba kowa bane, ko da yake ma daga ganin kayanshi ka san ba zai rasa zama wani tsohon an kasuwa ba." *Ko da* ya kai dattijon nan Sheikh *Mukhtar* ya kar a ya shiga har akin da yariman ke kwance yana bacci, dan tun jiya da suka yi maganar na i ya dafe kai ya fa i shi ba somamme ba kuma ba mai motsi ba. Yana kawowa a hankali ya zauna yana mi a mata yace "Mi aya." e ledar tayi ta fito da kofi aya ta bu e murfin ta mi o masa, kifa masa yayi a baki yace "Yi bismillah." Lumshe idanu yayi sannan ya furta bismillah a asan ma oshi, bashi ruwan yayi yana sha kamar wanda suka masa da i, tas ya shanye sai ka an da aka rage gimbiya ta shafe masa jikinshi da su har saman kanshi. Ganin ya kwanta kamar zai yi bacci yasa Sheikh Mukhtar fa in "Mu barshi ya kwanta, sau i na samu a cikin bacci." Fita sukayi tana ta waiwayenshi, a falo suka samu aninshi zaune, gimbiya ce tace "Ka je akinshi ka zauna, idan yana bu atar wani abun sai ka masa." Jinjina kai yayi ya mi e yana tattare alkyabbarsa ya shige akin. Wuri ya samu ya zauna shima ya buga tagumi yana kallon arfan namijin da ciwo ke neman halakashi, ya auki awa aya zaune shi bai yi bacci ba sai sauraren tattausar ira'ar Sheikh Abdur-rahaman As-sudais dake tashi a aki, yana ta lumshe idanu kamar bacci na son aukarshi kawai ya ji kakkarin amai daga kan gadon. *BAIWAR SALEEMA KENAN* *Alhamdulillah.* 15/06/2022 11:51 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _40_ Hankali tashe suka shigo akin sanda aya daga cikin hadiman ta sanar da su, kallo aya Sheikh Mukhtar ya ma aman da yake ya san cutar da ta jima a jikinshi ce yake amayewa, amai ba irin tamkar turirin wuta na tashin haya i, saida ya gama amai suka gyara mishi kwanciya aka tsaftace wurin. Da izinin Allah ko da dare ke yi Abdus-samad ya mi e kan afafunshi kamar ba shi ba. Har zuwa lokacin Sheikh na gidan, a wannan lokacin da ya ga abun al'ajabi kallon Gimbiya yayi yace " *Wacece ita*?" Tsaf ta fa a masa dalilin da yasa ta san Saleema har zuwa yau in nan, jinjina kai yayi yace "Ya ini take da akan ubangijinta, kuma ya barrantar da ya ininta, wata ila ma ita in tana da *BAIRWATA* amma ita kanta bata sani ba, ki yi wani abu akan yarinyar nan Ramlat, ki yi wani abu a kai." Da fara'a ta kalleshi cike da jin da in har yau akwai wanda ke iya kiranta da sunanta kai tsaye ba Hajia ko ranki shi da e da sauransu, jinjina kai tayi tace" Zuwa safe zan kirata na mata godiya." Kallonta yayi ba alamar wasa yace" Ta fi arfin godiya ta fatar baki, ki darajta *Baiwar* da Allah ya mata, shekara nawa muka auka muna ulunboton duk abinda muka sani, ina ce har gaban akin Alla na je musamman na yi wa yaron nan addu'a? Amma me ya sauya? Lokaci aya ta bado ruwan addu'a yasha ya fara amayo cutar dake jikinshi." Jinjina kai tayi cike da farin cikin abinda ke shirin faruwa da su tace "Za'a yi yadda ka ce Yaya, zuwa gobe da safen zan fara kiranta, daga bisani sai muje gidansu tare da kai idan komai ya lafa." Da mamakin rashin fahimtar kalamanta yace "Zuwa gidansu kuma bai yi girma sosai ba?" Girgiza kai tayi tace "Bai yi ba Yaya." Jinjina kai yayi yace "Shikenan, zan biki sau da afa muje, duk abinda kika yi zan kalleki ne na kuma yi miki *ladabi*." Dariya tayi da ta fito da kyawunta har da tsagarta ta barebare dake kan kumatunta da kuma gefen fuskarta sama da kunnuwa ka _______________ Suna zaune a ofar shiga falonsu it da Ahmad da Mamanta Ardiya ta fito daga falon ta nufi ofa hannunta ri e da waya, jim ka an ta dawo tare da ba o yan biye da ita a baya suna ta hira da dariya, saida ta zo daf da su ta kalli Safiya, suma kamar dai sauran kishiyoyi ne, yau fa a gobe a shirya, yanzu haka dake suna magana cike da raha ta nuna mata saurayin tace "Kinga an Yayata da nake baki labari, wanda yake zaune a Japan." Da fara'a Safiya ta waro idanu tace "A'a masha Allah, mutan waje yaushe aka zo?" Da harshenshi da baya fita sosai ya amsa da yar da cewa sati aya kenan, sama sama suka gaisa sai lokacin Saleema ta kalleshi tace "Ina wuni." afafunta dake mi e masu duhu amma kuma tafin afar mai hasken nan ba sosai ba shima, saidai a wanke suke a gyare sai cikon naman dake nuna zasuyi laushi, ga zara zaran yatsunta da wannan ya fi wannan wannan ya fi waccen. Le enshi na asa ya lashe dan abinda ya hango a afafun yasa jin jikinshi amsawa gaba aya har ya ji yana mata sha'awar saka sar afa a afafun, bai iya amsawa ba dan lokacin daya aga kai ya kalli fuskarta da sigar amsawa, a kan irjinta dake bu e ma'ana babu hijabi ya sauke dubanshi, sai kawai ya bi bayan Ardiya dake masa izinin ya shigo ciki. Har akin baccinta ta saukeshi ta kawo masa abun sha kafin ta zauna suna ta a hira a harshensu na buzanci da kuma sirkin faransanci da suke sakawa, shiru ya an ratsa na wasu da u kafin yace "Aunty, wacece wannan a waje na gani?" Yatsina fuska tayi tace " ar mai gidan ce, ga Mamanta nan ka gani har kun gaisa." a idanu yayi yace "Wow! Amma dai akwai halitta a wurin nan, me yasa baku mata aure ba kamar su Hadeeya?" e baki tayi tace "To ai mijin ne babu, idan ta samu za'a mata, yarinyar ce ta cika nauyin afa akan komai, hatta cikinta saida mahaifiyarta ta yi wata goma da shi kafin ta haife, haka ma a karatu ita ce baya, sannan ga ba in jini har yanzu babu saurayi." Wani sakaran murmushi yayi yana ayyana" Ni kam na ga gurin hutuna, ba dai ba in jini ba sai dai rabona." A zahiri kuma cewa yayi" Ta samu mijin ai auntyna." Da sauri ta kalleshi tace" Ban gane ba?" aga mata gira yayi irin na an duniya ya kashe mata idanu aya yace" Ina sonta, zan aureta." Rarako idanu tayi tana kallonshi da mamaki da jin haushin abinda ya fa a mata, ta ya zata yarda Saleema ta auri *Kabil* bayan ta san waye shi kuma an waye? Daga Hadeeya dake auren marar mutuncin nan Zeid, har Hameeda dake auren an mataimakin
Chapter 74 · 0% Book details