← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 198

Sashe 99

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa tayi ta fita tana fad'in "A'a wallahi ba zai yiwu ba, bari na d'auko wayata na kira Sa'ada ta zo ta sa Amna ta sakar mana tukunya, yau ni naga ikon Allah."

Tana daf da kaiwa d'akinta lieutenant ya shigo, wanda ya kasa zama ya matsu ya ga halin da Zeituna take ciki, sunkuyar da kai tayi tace "Ina wuni Abban Ammar."

Cikin sakin fuska ya amsa da "Lafiya lau, ya gidan?"

Ba b'ata lokaci tace "To da sauk'i dai gaskiya." Da mamaki ya kalleta yace "Lafiya dai ko? Ko wani abun ya faru ne?"

Cikin sunkuyar da kai ta fad'a mishi duk abinda ke faruwa, murmushi taga yayi yace "To ku samu ku lallab'a ta mana, kunsan dai fad'a da zagi ba zaisa ta huce ba."

"Eh hakane, yanzu ma zan d'auko waya ne na kira Sa'ada saita lallasar mana ita."

Da 'yar dariya lieutenant yace "To ke ba zaki lallab'ata ba?"

"To ai ni bansan ta inda zan fara bane, ita kuma ta saba da rigimar bibbiyu dama."

Dariya ya sake yi yace "Da gaskiyarki kuma, tana ina Amnar?"

Nuna sama tayi tace "Tana sama dai a tunani na."

"Bari na jaraba na gani ko zan iya." Ya fad'a yana wucewa d'akinsu dake sama, zaune tayi falo ta jira shi ya fito taji ya suka k'are, yana zuwa saida ya k'wank'wasa k'ofar d'akin yayi sallama, kusan a tare Hamna da Amna suka amsa wanda kowace ke kan gadonta babu mai kallon wata, saida kowace ta gyara zaman tufafinta kafin Amna da gadonta ne farko ta taso ta bud'e k'ofar, gaishe shi tayi ya amsa cikin sakin fuska tare da dafa kanta, murmushi yayi kafin yace "Amnata baki jin yunwa ne?"

Da sauri ta d'aga matsakaitan idonta ta kalleshi sai kuma tayi k'asa da su tana jujjuyasu, jin shiru yasa yace " 'Yata, yunwa nake ji, kuma na zo gida an fad'a min wai kin rik'e tukunyar girkin, shine nace bara na zo na rok'i alfarma, ko baki saketa dan ni ba ki saki dan k'annanki da kuma angonki Alhaji, wanda kinsan basa juriyar yunwa, da safe ma ance basu ci wani abun kirki ba."

Ganin tayi shiru yasa ya sake dafa kanta yace "A taimaka mana kinji, kiyi hak'uri komai ya wuce."

D'agowa tayi ta kalleshi tayi murmushi tace "Ba komai Abbanmu, nima ba'a son raina bane haka ta faru."

Murmushi ya mata yace "Nagode 'yata, Allah miki albarka."

Da murmushi ta masa da "Ameen Abbanmu."

Juyawa yayi ya samu Zeinabu zaune yace "To ku tashi ku duba tukunyar ku gani."

Yanda yayi maganar yasa ita ma tayi dariya tace "Yaran nan, mun gode Allah da yasa basu da k'ohi, da ina ga zuwa yanzu duk mun kamu da ciwon yunwa."

Dariya yayi yace "To wai ya akayi ma haka ta faru bayan kuma basu da k'ohi? Abun da mamaki fa."

"Wallahi nima ya ban mamaki." Madafa ta wuce shima ya shige d'akin Zeituna, kwance ya sameta akan sallaya ta idar da sallah, yanzu ma doguwar riga ce jikinta da hijab, sululu ta mik'e zaune cike da kunya tace "Sannu da zuwa, ina wuni."

Yaji dad'in gaisuwar data mishi dan haka ma ya saki murmushi ya sunkuya ya d'agota ta mik'e tsaye, saida suka k'arasa bakin gado ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyarshi yana kallon fuskarta, yanda take sunkuyar da kai kamar zata nitse k'asa, d'ago hab'arta yayi ya juyo da kallonta kanshi yace "Wai ke yaushe kunyar nan zata k'are ne? Ba zan iya tuna ranar da muka had'a ido dake ba fa? Ya kamata ace ance yanzu kin saba ko dan igiyar data d'aure mu wuri guda ni dake."

Zeituna dai k'ala ba tace ba sai sunkuyar da kai da take, ba tare daya daina mata kallon nan ba yace " Na zo duba jikinki ne fa, to ya kike ji yanzu? Ba kya jin ciwon komai?"

Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta saboda tsananin kunyar data kamata, dariya yayi tare da k'amk'ame ta sosai a jikinshi yana sumbatar ta, (Harkar fa ta manya ce, nayi nan ni dai🏃‍♀️).

Zeinabu na zuwa suka duba tukunya sai suka ga har dambun ya fara rusuna alamar zai d'auki dahuwa, ajiyar zuciya ta sauke tace "Ikon Allah, duk da ana cewa a daina yarda da canfi amma wani abun idan ka ganshi dole ka amince, to Allah ka gafarta mana."

Lieutenant bai jima ba ya sake fita dan baya son Hajia ta saka masa na jiyamu, fitarshi kuma ta bawa Zeituna damar zuwa madafa aka k'arasa sauran aiki da ita, suna cikin jera kwanukan abincin Ummy ta dawo, wanka tayi ta fito lokacin har Hajia ta ci nata abincin ita kad'ai akan makeken teburin daya had'a kujera goma sha biyu, fitowar Ummy suma matan da su Hamna suka zauna suka ci na su abincin, a wurin ne Ummy ta dannawa Amar kira, bayan ya d'auka tace "Kana cikin gida ne?"

Daga b'angarensu ya amsa da "Eh Ummy, kin dawo ne?"

"Na dawo, ka jira yanzu za'a aiko miki da abinci." Amsawa yayi da "To Ummy."

Tana aje wayar ta kalli Kamal dake kusa da ita tace "Ka shiga madafa abincinsu na nan a kula ka kai musu."

Soueiba ce ta kalli Kamal tace "Daga nan ka duba ka gani ko Jibril yana nan sai su ci tare."

Da kai kawai ya mata alamar to, Zeinabu ce ta kalleta tace "Yana ciki ai, na ga shigowar motarshi kuma har yanzu tana nan, tare da Junaid ma suka shiga."

Soueiba ce tace "Ah to shikenan, ka kai musu kawai, kace idan ma bai ishesu ba sai su zo a k'ara musu, dan yau kowa ya wuni da yunwa saboda Amna yau ta hora mu."

Dariya suka kwashe da ita banda Zeituna da tayi shiru tsananin mamaki ya k'ara rufeta, sai yanzu ne data shigo gidan ta fara fahimtar wata b'oyayyar rayuwa da suke, kowa d'an shi kawai ya sani bai damu dana d'an uwa ba, sannan ita kuma Ummy da take da yara biyu d'ayan kawai ta damu da shi, amma Ammar dake babban d'an ta bata nuna kulawa a kanshi ba, kuma ta tabbatar yana gidan dan ya riga sauran ma zuwa gidan, hakan yasa taji ba dad'i sosai ta mik'e daga kujerar ta nufi madafa, wani kwano ta samu madaidaici mai kyau ta zuba dambun ciki sannan ta samu k'aramin shi ta zuba had'in nik'akk'en naman da petit poit sannan ta fito, kai tsaye hanyar waje ta nufa ta kuma sa'ar had'uwa da Kamal ya dawo, kwanon ta bashi tace "Kamal, ka kaiwa yah Ammar kaji."

Kallonta yayi yace "Aunty Zeituna, har yanzu yah Ammar zaki ci gaba da kiranshi?"

Dariya tayi tace "To ya kake so na kirashi? Ai yayana ne a zahiri, ka je ka kai masa ka dawo."

"To." Ya fad'a yana juyawa ya koma b'angarensu, yana zuwa wata sallamar ya sake yi ya shiga, kai tsaye d'akin Ammar ya nufa har Amar na fad'in "Autan Ummy ina zaka je?"

"Wajen babban yaya." Ya fad'a ko juyowa baiyi ba, k'wank'wasa k'ofar d'akin yayi tare da turawa ya shiga, kwance yake yana kallon sama yayi nisa a tunani, har ya tsaya gabanshi ya aje kwanon k'asa bai kalleshi ba saida yace "Yah Ammar ga abincinka nan."

A hankali ya kalleshi ya tashi zaune, kallon kwanon yayi ya sake kallon Kamal yace "Abinci na kuma?"

"Eh." Kamal yace ya juya da niyyar fita, sake cewa yayi "Abinci fa? Wa yace ka kawo min?"

Juyowa yayi yace "Aunty Zeituna ce, amaryar Abba."

Bushewa yayi da dariya kamar mahaukaci sabon kamu, irin dariyar da yake yi ce yasa Kamal cewa "Yah Ammar lafiya?"

Tsayawa yayi ta kalleshi yace "Ko da nace, ni nasan inba bak'o ba babu wanda zai aiko min da abinci, to naga dai ko uwar data haifeni bata damu da ci na ba bare kuma wanda suke kewaye da ita."

Jinjina kai yayi yace "Amaryar Abba, amma me yasa zata aiko min da abinci?" Kamal ne yace "Ni ma ban sani ba."

Da mamaki Kamal yace "Zaka ci kenan?"

K'uri ya masa da ido yana kallo hakan yasa ya fita ya rufe mishi d'akin, yana ganin fitarshi ya shafa cikin da har kukan yunwa yake masa amma kasala ta hana shi fita ya je ya ci abinci, murmushi yayi yace "Zan ci mana Kamal, har na manta kalar d'and'anon abincin gidan mu, ina ma Ummy ce ta aikoka da abincin nan, da na ci da farin ciki da kuma karsashi ko da bana yanayin cin abincin, amma gashi matar data shigo gidan nan jiya wacce nayi mata kashedi akan uwata ita ce ta zubo abinci wai akawo min, duk da bansan manufarta na yin haka ba amma dai hakan yasa na ji kamar an kula dani ne."

D'auko kwanon yayi ya bud'a, take yaji yawunshi sun tsinke, tashi yayi yaje ban d'aki ya wanko hanayyenshi ya fito, saida yayi bismillah tare da fad'in "A'u'zu bikalmatillahi tammat-min sharri ma kalaq." Duk yayi hakane dan aniyarta ta koma mata wai idan ma abinda ya mata jiya ne zaisa ta fara gaggawar d'aukar mataki akan shi.

*A gurguje*

Da magribar wannan ranar aka kawo kayan Amar ma, shi ma dai kamar yanda Ammar yayi haka ya kawo, sai dai ba shine ya kawo ba, wasu daga cikin yan uwa na dangin mahaifinsu da kuma abokan lieutenant ne suka kawo, anan kuma take kafin su tafi Hajia ta shaida musu nan da kwana goma sha hud'u sati biyu kenan za ayi bikin, dan haka a shirya da kyau kafin lokacin, da haka labari ya riski kowa inda aka shiga shirya ma wannan rana.
Chapter 99 · 0% Book details