← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 198

Sashe 126

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar sukar mashi taji a zuciyarta, tsam tayi kamar zata saki wayar, zuciyarta saida ta buga saboda jin abinda ta fad'a, to ita meye makomarta kenan? Tana d'auke da banzan cikinshi fa, ba zai yiwu ba gaskiya, dole tayi gaggawar tsayar da wannan abun haka, ba zata juri jin wannan kunyar ba, jiki a sanyaye Hamna ta amsa mata da "...

*Alhamdulillah*

*Yawan sharhi yawan rubutu.*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.N.A]* ☆🖊️

_Bismillahir rahamanir rahim_

_45_

"Abun mamaki, na d'auka zaku jima baku saba ba."

Murmushi tayi tace "Nima haka."

Hamna ce tace "Amma dai kina shan duka da rashin kunya?"

Dariya tayi sosai kafin tace "Toi même tu le sais."

Fira sosai sukayi cike da kewar junansu kafin daga bisani suyi sallama. Ammar ma fitarshi wajen lieutenant yaje, shi kad'ai ya samu kan makeken lallausan karfet kishingid'e cikin k'ananan kaya yana sha iskar mangwaro dake kad'awa, zaunawa yayi shima yana fad'in "Abba barka da hutawa."

Zaune ya tashi yana fad'in "Har ka iso?"

"Um Abba." Ya fad'a yana d'aukar roban ruwa ya d'aga kai yana tsiyayawa yasha, saida ya gama ya kalleshi yace "Abba ka ce na zo, lafiya dai ko?"

Tank'washe k'afafu lieutenant yayi ya kalleshi a nutse yace "Ammar, ina so ne na sani, meye matsalarka a rayuwa?"

D'aga kai yayi ya kalleshi ido cikin ido, kamar mai son fahimtar wani abu sai kuma ya kawar da kansa yace "Soyayya, da kuma k'auna."

Mamaki ne ya cikashi sosai na abinda ya fad'a, kallonshi yayi sosai yace "Ban gane ba."

Murmushi yayi yace "Ba zan iya cewa komai ba Abba, kayi tunani ka fahimci abinda nake nufi, amma ka sani nayi jarumta sosai da har ban iya gallabarku ba, yara irina da suka rasa abinda nima na rasa wasu su kan kashe kawunansu, wasu su kan kashe 'yan uwansu da ake nuna musu fifiko akansu, wasu kuma su fad'a shaye shaye da tunanin samun mafitar matsalarsu, wasu suna zama 'yan ta'adda ko kuma su fi k'arfin iyayensu, wasu kuma a wayi gari su k'i iyayensu su tsanesu, idan sun girma zasu iya mantawa da su suma, Abba duk abu d'aya yakan iya jawo wannan matsalolin, rashin samun kulawa daga iyayen da suka haifeka, wanda ma basa ganinsu a doron duniya ya suka k'arata bare kai da kake ganinsu kuma sunyi watsi da kai?"

Wuri d'aya ya kafe da ido yana kallo da daskarewar tunani ta yanda baya tuna komai a k'walwarshi, jin shirun yayi yawa yasa Ammar kallonshi, murmushi yayi ganin yayi kamar gunki ya rik'o hannunshi, suna had'a ido ba tare daya daina murmushin ba cikin rawar murya mai kama data kuka yace "Abba, ka daina kirana d'an iska bana jin dad'i, bana son kana hantarata musamman a gaban mutane, ina so ka dinga sa min albarka kana min addua'r alkairi."

Sakin hannunshi yayi ya sunkuyar da kai, siraren hawaye ne yaji sun taho mishi, hannu yasa ya share ya d'ago ya kalle shi, tausayin shi ne ya kama shi sai kawai ya zuro hannu ya dafa kanshi, sake kallonshi yayi sai kawai zuciyarshi ta karye ya fashe da kuka, cikin tashin hankali ya matso kusanshi ya fara share mishi hawayen yana fad'in "Kai lafiya? Meye na kuka kuma? Yi hak'uri mana kaji, na daina daga yau ba zan sake ba."

Tafukan hannaye yasa ya rufe fuskarshi ya kwantar da kanshi kan k'afar lieutenant, daddab'a shi ya fara yana rarrashi, da k'yar ya tsagaita da kukan amma bai d'aga daga k'afarshi ba, sun jima haka kafin ya tashi zaune suka fara hira, sosai suka ji dad'in wannan lokacin saboda hirar fahimtar da sukayi, har ta kai ta kawo lieutenant yana sanar dashi harkokinshi na yau da kullum, k'aratowar magrib tasa su d'aukar makullan motarsu suka bar wurin.

*Bayan wata uku*

Rayuwa tayi dad'i sosai a b'angaren Ammar da Amna, zama suke na fahimtar juna da girmamawa, duk da kalmar so bata tab'a shiga tsakaninsu ba amma wata kalmar idan ya zage damtse ya mirgino mata ita kanta har kasa d'auka yake, babu kasawa a salon kulawar da yake nuna mata, haka kuma babu kasawa a salon muguntar da yake mata, zamu iya cewa soyayya ce da kuma wahala, yanzu haka har ta saba da muguntarshi, ba wuya zai kai mata k'ulli ko zagi, kuma a take a wurin zai ce ta yafe mishi, dan haka bata sa wannan a matsayin abun damuwa ba.Yanzu haka Allah ya azurtasu da samun k'aruwa, ya rub'anya kular da yake mata, shiyasa ya daina tab'a lafiyar jikinta idan dai ba kashe arna yake ba wanda baya wasa da kashe su. A b'angaren Abba ma yanzu komai yayi daidai, aiki kam lieutenant shi ke abinsa, amma kasuwanci kuma duk ya damk'a ragamar hannun Ammar da Amar, shima kuma Amar yana ganin tashi kalar cutar, sai dai kuma shima ya saba kamar yanda matarshi ma ta saba.

Jamila ta gama k'osawa da halin da matar yayan nata take mata, so da dama idan suka had'u saita dinga mata shagub'e da jirwaye mai kama da wanka, tana ninketa ta baibai da wasu maganganun da bata iya gane su ba, ga Huda da take ta k'ok'arin tusata a gurin mijinta ko yaushe, tana hana su shak'at ba dare ba rana, gashi shi kanshi Jibril d'in ta fahimci ya d'an canza daga yanda yake, sai dai har yanzu ta kasa tambayar kowa sai k'unsar bak'in cikinta take ita kad'ai, amma yanzu kam daf take da tayi magana dan abun ya gundureta.

Hankalin Ummy ya tashi sosai ganin har anja watanni ba'a maganar dawowar Hamna gidan, hakan yasa kawai ta shiga ta fita har saida ta kasance d'aya daga cikin wanda zasu tafi information a *France* na wata shida, tayi murna sosai dan haka ta kira Hamna ta fad'a mata komai, a wannan rana basu kwanta ba saida Hamna ta samu mafita kan yanda zatayi ta bar gidan nan, ba gidan kad'ai ba duka garin, dan ita kanta tana so ta tafi kafin cikinta ya shiga wata na biyar har a gane halin da take ciki, gashi masifar Aissata ta isheta, jarabar yau daban ta gobe daban, uba kuma ba mai zama gida ba, ko yana garin ma saita kwana ta wuni basu had'u ba ko a tsakar gidan.

Cikin ikon Allah ko da ta fad'a ma Gambo tanti *Gishata* (k'anwar Ummy) take neman alfarmar taje *Agadez* (asalin Ummy in baku manta ba) ta dinga kwana a wurinta saboda mijinta baya nan, girman Ummy da kuma kimarta na yanda ta raini yaran yasa bai iya mata musu ba yace ya amince ta tafi, amma karta bari Hajia taji dan zatayi fad'a, dad'i sosai taji na barinta da yayi. Da kanshi yasa dreba ya d'auketa sai Agadez inda suka had'u da Ummy anan ita ma da shirin tafiyarta. Gishata tayi mamakin ganinsu lokaci d'aya, bata sare ba saida Ummy tace France zasu je, tambayarsu tayi sai Ummy tace kawai tayi hak'uri idan sun dawo zasu fad'a mata, amma ta musu alk'awari d'aya shine ko wani ya tambayi Hamna karta nuna ta san inda take, sannan ita ma Ummyn bata so kowa yasan ta zo, hankalinta ya tashi da tunanin abinda ke faruwa, amma sai Ummy tace tayi alk'awarin fad'a mata komai idan suka dawo, sannan kad'ai ta d'an nutsu tare da musu fatan alkairi a sanda jirginsu zai d'aga, wanda hatta passeport da visa duk Ummyn ta d'auki nauyinsu a kanta. Tasan kuskure take aikatawa, amma ta riga da ta bar gini tun ran zane, gashi dalilin kuskuren da d'anta ya aikata yau ta wa mijinta k'arya cewa wata hud'u zatayi, dan farko bai so tafiyar ba ko kad'an saboda cikin da yake tunanin tana da shi, da k'yar ta shawo kanshi ya barta da tace wata hud'u ne kawai, gashi shima dalilin k'aryar data mishi har saida ya fad'awa Alhaji ya ma Hajia magana kan a barta ta tafi, ita kam yau ina zata saka kanta ne?.

Tafiyar Hajia saoudia abubuwa sun rage yanda kowa ke abinda ya so, Alhaji dai dama ba mai zafi bane ko tsanani, shi kai ko fad'a ma da wuya kaga yana wa mutum, mafi yawan lokaci ko ya wuni gidan zai wuni a cikin jardin (guardin) ne, ko kuma wajen wasu harkokinshi na daban, amma yau daya zama zata dawo duk sai jikin kowa yayi sanyi, masu girki sun baje bajintarsu duk dan su faranta mata, sai dai duk da haka sun had'a da addu'a kan Allah yasa ta so abinda suka mata ba tare da tayi k'orafi ba.

*Ta farka* ne saboda fitsarin daya cika mata mara, zaune ta tashi cike da kasala kafin ta yaye zanin rufar ta sauka ta shiga ban d'aki, saida ta rintse ido saboda zafinda take jin sanda take fitsarin, tana kammalawa ta kara ruwa da na d'umin da take ajiya kafin ta fito, sai lokacin ta iya jin sanyin dake akwai wanda hakan ke nuna lokacin sanyin ne zaiyi, sake komawa tayi kan gadon ta kwanta taja zani ta rufa ruf, har zata gyara kwanciya taji ya jawota jikinshi ido rufe yana fad'in "Me zakiyi da abun rufa bayan gani? Ni ne gadonki kuma abun rufarki."

Tashi yayi ya mata runfa ya had'a goshinshi da nata yana kallon idonta yace "Kina lafiya duniyata?"

Saida ta sakar masa murmushi tana lumshe ido tace "Lafiyata lau duniyata, bacci kawai nake ji, yaron nan naka baya barina bacci saboda yawan tashi fitsari."

Dariya mata yace "Ki barshi lokacinshi ne yayi, idan kuma kina so idan kina jin fitsarin ki dinga tashi na saina tsotse miki shi."

Cikin dariya ta yamutsa fuska tace "Ta yaya?"
Chapter 126 · 0% Book details