Sashe 81
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D'aya hannunshi ya fito da shi ya kama yalwatattar k'asumbarshi yana shafawa, takowa yayi kusanta yana kallon idonta babu wani d'ar ko tsoro cikin taushin murya yace "Ummy, ko zaki iya tuna abinda ya faru muna da shekara goma sha shida a duniya ni da Amar? Mun samu matsala dashi akan riga, a lokacin Amar nada rigima sosai, ko abu nawa ne saiya nuna nashi ne ko yana son shi saboda yasan kowa zai goya masa baya, asalin rigar tawa ce, kuma ke ma kinsan haka saboda kinga alamar da nama tawa, amma sai kika rufe ido dake da duk sauran mutanen gidan kuka ce dole sai dai ni na hak'ura tunda nine babba, hakan ne yasa nima raina ya b'ace a cikin dare na yaga duka rigunan da reza, amma me zai faru? Washe gari Hajia ta mareni a fuskata ta zageni zagin da ko kare tayi wa saiya zubar da hawaye, ta kira ni d'an iska har ba adadi, ta kira ni shege munafiki mai bak'ar zuciya..."
Sunkuyar da kai yayi yasa yatsa d'aya yana share hawayenshi, ba tare daya d'ago ba yace "Zagin da yafi tsaya min a rai shine data kalle ni a gabanki a gaban idon mahaifina ta kira ni da *d'an Allah bani*, wai da tasan haka zan zama da ko da aka haifeni tasa an min allurar mutuwa, a wannan ranar ta fad'a ni, ni Ammar nine *annobar ahalinta*, zuciya nayi na fita farfajiyar gidan ina kuka, na wuni a wuri d'aya zaune da tunanin ko zan samu wanda zai zo ya rarrashe ni ya kwantar min da hankali, amma babu wanda ya zo kusa da ni, a lokacin mahaifiyata ce kawai nake ganin zata iya zuwa kusa dani kuma ta rarrasheni, ganin ke baki zo ba yasa ni naje har d'akin ki, Ummy me kikayi a lokacin?"
"Ina shiga kika rufe ni da wani fad'an wai na fita na baki wuri, haka kema kika sake kirana d'an iska mai ja miki magana, a k'arshe bud'a baki ki kayi kika ce wai na fice miki daga nan ba kya son gani na ko kad'an, Ummy kinsan meya hana ni barin gidan nan a wannan ranar?"
Ummy dake kallon yanda hawaye ke zuba a idonshi kasa amsa mishi tayi, dafe k'irjin shi yayi saitin zuciyarshi ya ci gaba yayi da cewa "Ummy *saboda soyayyarki ne*, ina ji a jikina kamar idan na tafi na barki a gidan Hajia zata ci gaba da k'untata miki, hakan yasa na hak'ura na zauna duk da zafin da nake ji a zuciyata, bayan faruwar hakan kwana shida na d'auka ina zuwa d'akin ki da nufin gaishe ki, amma sai kika ce ko amincin da nake nema miki ba kya so bare kuma gaisuwa ta, daga ranar ne ya zamana duk d'akin da zan shiga a gidan nan bana iya sallama, Ummy zan fara gaishe ki ranar da kika fara kallona kamar d'an da kika haifa, zanje wajen Abba."
Yana fad'a ya juya ya fita da sauri sosai, fad'awa tayi kan gado dab'as kamar an turata, sai dai ta nemi hawaye ta rasa, maganganunshi ke dawo mata, kenan babu abinda yake mantawa? Zai fara gashe ni ranar dana fara kallonshi *kamar d'a*, kamar d'a? Ba ma d'ana ba? Tunawa da tayi yace zaije wajen lieutenant kuma tasan ba lallai su kwashe lafiya ba, dan haka ta mik'e ta d'auki wayarta ta fara kiran lieutenant, amma bai d'aga ba saboda wayar na silence yana ganawa da wasu manyan mutane, aje wayar tayi ta fito falo sam bata wani saka wani al'amarin a kai ba bare tayi tunanin halin da d'an nata ke ciki.
Yana fitowa ya samu Amna ta gaji da jiranshi, Hamna kuma ta d'auki moton ta tafiyarta, yana shiga taga ya had'a kanshi da sitiyarin motar yana sauke wata k'akk'arfar ajiyar zuciya, ya kusan minti biyar kafin ya d'ago ya jawo lotus d'in dake cikin motar ya goge fuskarshi da kyau, tayar da motar yayi suka fita daga gidan, saida suka fara tafiya ya kalleta wacce ita ma take kallonshi ganin sabon yanayi a tare dashi yace "Kinyi latti ko?"
Ganin idonshi jawur alamar kuka ba wai b'acin rai ba yasa saida gabanta ya fad'i, duk sai taji jikinta yayi sanyi tana son sanin meye damuwar, cikin taushin murya tace "Yah Ammar lafiya? Me yake faruwa?"
Kallonta yayi yana doka wani uban murmushi ya kuma kalli gabanshi ya ci gaba da tuk'i, har ta fidda ran zai mata magana sai kuma ta ji cikin wani yanayi dake nuna damuwar dake zuciyar mutum yana sakin murmushi yace "Amna meyasa zaki tambayeni me yake faruwa? Shin baki tab'a lura da abinda ke faruwa bane?"
Girgiza mishi kai tayi hakan yasa ya kalleta yace "Tunda kike a gidan nan kin tab'a jin wani Ammar Allah yayi maka albarka? Ko kuma zan fita kiji wani yace Allah ya tsare ko a dawo lafiya? Ko kuma kiji ance Allah ya taimake ka ko makamantan haka?"
Shiru tayi alamar zurfafa tunani da sauri yace "Karki ba kanki wahala, ba zaki tuna ba dan babu ranar."
Ci gaba yayi da tuk'i harya sauketa, har zata shiga cikin makarantar yace "Ko na zo na rakaki ne? Kin makara fa sosai."
Cikin sanyin jiki tace "A'a yah Ammar, kaje kawai, kai ma nasan ka makara a asibiti."
Jinjina kai yayi alamar to ya fara k'ok'arin tayar da motar, kamar daga sama ko saukar ruwa ya tsinci muryar Amna cikin wani mugun yanayin da har k'asan zuciyarshi ta birgeshi tana fad'in "Allah ya kiyaye hanya yah Ammar, Allah ya baka abinda kaje nema, Allah ya tsare mana gabanka da bayanka, saika dawo."
Tana fad'a ta d'aga masa hannu alamar bye bye ta shige ciki, da kallo ya bita yayin da yake jin wani farin ciki na nuk'urk'usar zuciyarshi, wani murmushi ya saki wanda shi kanshi ya manta rabon da yayi irinshi, ba tare daya daina murmushin ba ya ja mota sai asibiti.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Maryama da Iklima sun duk'ufa shirye shirye na gyaran jikinta da sauran abubuwan, kulawar da kakarta da kuma mahaifiyarta ke nuna mata kamar yanzu suka haifeta, haka ma Huda soyayya suke nunawa yarinyar sosai, wanda a yanzu Huda bata da aiki sai fad'in Abbanta Jibril wanda ya yanka mata saniya, yau ma asibiti suka shirya suka tafi aka cire mata robar da aka saka mata dan hana d'aukar ciki, a hanyarsu ta dawowa Iklima ke cewa "Yanzu Mari kin shirya haihuwa kenan da zaran kin shiga gidan?"
Murmushi ta mata tace "To me zanyi idan ba haihuwar? Bana da budurcin da zaiga mutumci na da shi, nasan ina shiga gidan soyayyar da yake nuna min zata ragu, kinga kuwa kafin na fara fuskantar tasku k'wara ina shiga na fara dire masa 'ya'ya."
"To amma meyasa ba zaki fad'a masa gaskiyar waye wannan d'an uwan nasa ba? Ina ga hakan zaifi."
Murmushi ta sakeyi tace "Zan fad'a masa, amma bayan naje gidan."
A hankali Iklima tace "To Allah yasa alkairi."
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Kawu Mamu ma tuni yaje rugagensu yayi shelar bikin Zeituna, wacce yanzu a gidan kamar sarauniya, wani lokacin kawu da kanshi ke kawo mata abinci har bukkarsu, wani lokacin ma idan akayi tuwo sai yace ba zata ci tuwo ba, da kanshi zai fita ya siyo mata tsire ko gasassar kaza ya kawo mata, Zeituna saidai tayi wanka ta sake kaya ta koma ta zauna kan katifar Jumare da yanzu kawu yace ta zama ta ta har a d'aura aure, yau dai kam kanta ya sake kullewa da taga yan uwa na zuwa wai gobe aurenta da lieutenant, jira kawai take taga goben tayi saita tabbatarwa da kanta, sai dai kuma ana haka kawu Mamu ya sanar da ita Alhaji yace anjima da dare lieutenant zai zo su gana, hakan yasa ta k'arasa wuninta da muguwar fargabar had'uwarta da lieutenant d'in.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Yana sauka daga aiki da rana kai tsaye douanes ya wuce, yana fitowa daga mota ya tunkari ofishin, saida wani yaron lieutenant yace masa yana ganawa da bak'i, amma saiya nuna mishi d'an shi ne kuma abune na gaggawa, yana shiga ofishin babu sallama ya same shi zaune tare da wasu manyan alhazzai biyu, tsaye yayi yana kallonshi inda lieutenant ya mik'e da mamakin rashin sallamarshi ko neman izinin shiga bare gaishe da mutanen, cikin jin haushi yace "Wai kai mahaukaci ina ne? Ya zaka shigo wuri babu izini babu gaishe da mutane ka wani yi mana tsaye? To uban wa kake bi bashi anan? Me ma ya kawo ka?"
Kawar da kanshi yayi yana kallon mutanen da suma suke kallonshi, abun mamaki sai lieutenant yaga sun mik'e suna bawa Ammar hannu da fad'in "Likita, kaine anan? Ya kake ya aiki?"
Ba fara'a ya amsa da "Alhamdulillah."
D'ayan ne yace "Yallab'ai ko yaron wajenka ne?"
Cikin ji kunyar amsawa ya d'an jinjina kai alamar eh, murmushi sukayi sai d'ayan da yace "Ko da nace, ashe likita gadon mutumci da kirki yayi tun daga gida, ai likita na ne dake duba ni, yana da son mutane wallahi da jansu a jiki indai aka ce majinyacinshi ne kai."
Kallon lieutenant sukayi suka bashi hannu suka ce "Ba damuwa yallab'ai, zamu jiraku a waje harku gama, nasan abune mai mahimmanci ya kawo shi."
Yana fad'a suka fita suka barsu, cikin jin haushi da halayarshi ya koma ya zauna yace "Meya kawo ka nan?"
Ba tare daya zauna ba yace "Abba ina son sanin wani abu ne, na tambayi Ummy tace na zo na tambayeka, shiyasa na zo."
Fuska a d'aure yace "Menene?"
A tak'aice yace " Wani laifi Ummy tayi daka yarda zaka mata kishiya?"
Da k'arfi ya buga teburin gabanshi ya mik'e yana fad'in "Shirmen banza! Dama abinda ya kawoka kenan? Uwarta ka ce ta turoka ka min wannan tambayar?"
Fuska a murtuke yace "Babu ruwanta, kawai ina son sani ne, idan akwai laifin data maka ka fad'a min?"
Nuna mishi k'ofa yayi yace "Banda lokacin wannan haukan naka, ka b'ace min da gani daga nan."