← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 198

Sashe 116

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirun yayi yana kallonshi, saida ya saisaita nutsuwarsa sannan yace "Zan fita ne Alhaji, asibiti zanje, akwai marasa lafiyan da zan gani nan da minti ashirin."

D'an jinjina kai lieutenant yayi alamar gamsuwa tare da cewa "Saika dawo, amma karka cika dare ka bar min 'yata ita kad'ai, kasan har yanzu bak'i ne su."

Juyawa yayi bai ce komai zai tafi sai kuma lieutenant yace
"Dama ina son ganinka." Dawowa yayi yana fad'in "Gani."

Saida ya saci kallon Zeituna kafin yace "Yarinyar da ta zo d'azu gidan nan me yasa ka mareta? Baka san yer uwarta ce ba?"

Kallon daya ma Zeituna yasa lieutenant cewa "To ba ita ta fad'a min ba, yanzu daga gidan muke kuma ran iyayenta ya b'ace, har naji mahaifinta na cewa ma zai zo har gidan nan ya rama mata."

Wani murmushin yau ga banza ta samu ya ma lieutenant, mayar da kallonshi yayi ga Zeituna yace "Uwa ni kam ina ne gidanku ma?"

"Babu nisa da nan ai, kana shiga kwanar..." A firgice lieutenant ya kalleta saboda jin zata kwafsa, shi fa ya fita sanin waye d'anshi, shi ya haifi abinshi, dakatar da ita yayi da cewa "Ke kuma miye haka? Daga ya tambayeki saiki fad'a masa."

Kallon ashe ka harbo jirgin ya masa tare da sakin murmushi yace "Abba hak'uri zanje na basu, kace yace zai zo har nan, ku surukai ne bai kamata a samu matsala a tsakaninsu a dalilina ba."

Da sauri Zeituna tace "Kwanar beauté salon, a jerin gidan Alhaji Chapi'u cikin bukkokin nan."

Murmushi yayi sosai wanda yasa hak'oranshi fitowa saboda jin dad'i, lumshe ido lieutenant yayi alamar shikenan, ta fad'a an gama kuma, juyawa ya sake yi sai kuma Zeituna ta kalli lieutenant kallon dake ankarar dashi bai mishi addua'r ba, yanda ya kalli Ammar yasa shi tsayawa yace "Alhaji kana son wani abu ne?"

Saida ya k'ara gimtse fuska sannan ya d'aga mishi hannu alamar ya zo, matsowa yayi kusa da shi a lokacin ya dafa kanshi ba tare daya kalle shi ba yace "Allah ya maka albarka, saika dawo, ka kula da kyau, kada kayi abinda zaka zubar mana da mutumci."

D'ago kai yayi ya kalle shi, tabbas dai shine daya sani ya saka mishi albarka, sai dai ba yayi ne saboda ya cancanta ba, baiyi ba saboda ya haife shi, yayi ne saboda an sa shi, jinjina kai yayi alamar to tare da kallon Zeituna, murmushi ya mata na jin dad'in namijin k'ok'arin da tayi yace " Nagode uwa."

Kallonshi yayi tare da juyo mishi kumatunshi yace "Ka k'arasa kadarka Abba na."

Kallon ban fahimta ba ya mishi yace "Ban gane ba? Me kake nufi?"

Kallonshi yayi yace "Sumbata ta zakayi, yaushe rabon da kayi haka dan Allah, ko da muna yara ma baka cika yi ba saboda kai ba mazauni bane."

Kallon Zeituna lieutenant yayi ya gimtse fuska, da ido ta masa alamar kayi mana, sake matsowa yayi yace "Abba sauri nake fa."

Saida ya rufe ido ya fara matso da fuskarshi kusan tashi, a hankali ya sake bakinshi kan lallausan kumatunshi had'e da k'asumbarshi, a hankali ya sauke mishi sumba mai kyau inda Zeituna taji sautin "Mtsss."

Wangale baki tayi tsabar farin ciki kamar an mata albishir da gidan aljanna tace "Weeee, munyi nasara."

Kallonshi Ammar yayi ya rik'o hannunshi, yana so yayi magana amma yana jin kamar ba zai iya ba, sai dai daga kallon da yake aika masa zaka fahimci shauk'inshi da kuma kaunar mahaifinshi, sakin hannunshi yayi ya juya zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo, kallonshi yayi yace "Nagode Abba, da ina samun irin haka kullum kaso hamsin na abinda ke zuciyata zai warke."

Kallon Zeituna yayi yace "Uwa ce ke mai wuyar samu, uwa mai tsadar gaske."

Yana fad'a ya juya barsu nan tsaye, kallon Zeituna yayi yace "To yanzu kinji dad'i."

Turo baki tayi gaba ta girgiza tace "Fiye da zatonka."Juyawa tayi da sauri ita ma ta nufi babban falo ta manta da lieutenant tsaye, bin bayanta yayi yana mamakin halinta da yarinta, wato dole indai ka auri yarinya komai tsufanka sai tasa wata rana kayi k'uruciya kai ma.

Tun magriba ta shirya tare da Huda tana jiran shigowar Junaid dan yasan abinda ke faruwa, tayi niyya zata zauna anan tare da yarta, idan kuma yace bai yarda ba zata nuna mishi sai dai ta bar gidan, tasan kuma yana sonta ba zai yarda ta bar gidan ba. Bai shigo ba sai bayan sallah isha'i, yana sallama Huda ta tafi a guje ta rumgume shi saboda sabon da sukayi na kwanakin baya, shima rumgumeta yayi cikin farin ciki yana fad'in "Huda ke ce a gidan namu? Yaushe kika zo?"

Saida ta d'ago ta kalleshi tace "D'azu muka zo ni da tanti Iklima."

Da farin ciki yace "Da kyau, kice ziyara kika kawo mana, amma dai zaki kwanar mana anan ko?"

Juyawa tayi ta kalli mahaifiyarta dake tsaye bayansu, k'arasa mik'ewa yayi tsaye shima yana kallonta, kwalliya ce tayi ta d'aukar hankali da fitar hayyaci, k'ananan kaya ne jikinta wanda suka nuna komai, murmushi ta sakar masa tare da matsowa ta rumgume shi, cikin kunne ta rad'a mishi cewa "Sannu da zuwa gwarzona."

D'an sumbatar kumatunta yayi tare da cewa "Sannu da gida."

Juyawa Huda tayi ta koma kan kujera ta zauna, binta yayi da kallo sannan ya kalli Maryama yace "Amma anan zata kwana ko?"

Kama shi tayi suka nufi d'aki tana rik'e da k'ugunshi tace "Eh, ai dama da aka taho da ita ba dan ta koma bane, zata zauna anan ne tare dani, tunda kaga Mama ba lafiya ne da ita ba, Inna kuma girma ya zo ba zata iya kula da ita ba."

Sam shi dai baiji wani abu ba a game da zaman Huda anan, sai dai yasan zasu samu matsala da Hajia, haka ma mahaifiyarshi dake da tsegumi, zata ga kamar yarinyar zata gaje shi ne, jin shiru yasa ta lek'a fuskarshi tace "Ya dai? Ko baka amince bane?"

Kallonta yayi yace "Haba dai, wacece Huda da har zan kasa amincewa? Ko ba komai fa yarinya na samu a sauk'i."

Murmushin jin dad'i tayi ta rumgume shi tace "Nagode gwarzona, Allah ya bar min kai."

Tun daga falo sautin kuka ke tashi har zuwa uwar d'akin, yayi rarrashin duniya da ban baki amma ta k'i dainawa, yayi duk yan dubarun daya sani amma maganar d'aya ce har yanzu ita ce "Wallahi zafi, ciwo nake ji, shikenan mutuwa zanyi, ni kawai ka kaini wurin Mama na."

Tagumi ya zuba yana kallonta, da farko tausayi take bashi saboda shi kanshi yasan ta aikatu sosai, bai d'auka zata jure wahalar daya bata ba, amma da tafiya ta tafi saita fara bashi haushi saboda ganin kamar da gangan take yi, amma yanzu mamaki kawai take bashi, dan shi dai baiga abun jininin ba. Duk da taga irin kallon da yake mata baisa ta daina kukan ba, har ga Allah zafi take ji ta yanda tana zaune ne kawai saboda kar yaga rakinta yayi yawa, ganin ya k'ura mata ido ya daina rarrashinta ma wanda ke sa ta d'anji dad'i yasa ta k'ara bud'a murya tana murza k'afafu k'asa da yarfa hannaye tana fad'in "Ni kawai ka kaini wajen uwata, Allah ba zan zauna da kai ba yah Jibril, haka kawai duk ka rugurguza ni daga wasa, ni ba zan iya ba ka kaini gida kawai."

Cire tagumi yayi ya rufe baki yana dariyar mugunta, lallai yayi babban laifi, domin kuwa daga yan shafe shafe ko da taga zai wuce gona da iri ta fara tsora ta so zille masa, amma saiya kwantar mata da hankali da cewa ai kawai wasa ce yake mata, data tambaye shi da mamaki tace "Wasa fa?" Sai cewa yayi "Eh mana, Hajia ta had'a mu da k'annanmu ba dole mu dinga muku wasa ba."

To fa daga nan ne aka yi tazarce ya mata baja-baja, ko da ta lura dariya yake mata saita k'ara himma, cikin dariya ya jawota jikinshi ya rumgume, d'ago kanta yayi ya saita bakinshi cikin kunnenta yace "Yi hak'uri mana 'yar k'anwata, ba zan sake ba daga yau kinji, kukan ya isa haka kar kisa na d'auka ke raguwa ce ba zaki iya dani ba."

Da sauri ta mayar da kanta cikin k'irjinshi ta rufe fuska, dariya yayi yana k'ara matseta yace "Kin hak'ura yanzu?"

Kai ta d'aga mishi alamar eh, sake matseta yayi ya jingina bayanshi a kujerar yana shafata, cikin saisaita murya yace "Idan Allah ya tashe mu gobe ki tasheni da wuri, dan dole naje na gaishe da kakarku na kuma gode mata data bani ke."

D'an d'agowa tayi tace "Kakarmu? Kai fa?" Girgiza kai yayi yace "Jamila ba zan uya da kakarku ba, ku dai kuyita hak'uri da ita wata rana sai labari."

Jinjina kai tayi tace "Lallai ma, ai kuwa zanje na fad'a mata abinda ka ce."

Murmushi yayi ya sumbaci goshinta yace "Ni ma saina had'ata da hawan jininta."

Kallonshi tayi tace "Hawan jininta kuma?"

"Eh mana, babban yayanmu ba, Ammar." Murmushi tayi ita ma tace "Allah sarki besty Amna, ko a wani hali take?"

Bushewa sukayi da dariya dukansu inda yace "Bana jin a shekara goma zata fahimci mutumin nan."

Cikin sanyi jiki Jamila tace "Zuwa lokacin da zata fahimce shi kuma jikinta ya farfashe da duka, zagi kuma tayi buhu buhu har ta fara siyarwa ita ma."

Cikin dariya Jibril yace "Bak'ar magana, yab'a magana, gatse, habaici, maganar rashin kunya kuma zasu zama abincinta ne, shiyasa na so Hajia ta had'a shi da kankana, ko ba komai mun daina kallon tv daga ranar, dan kullum da dramar da zamu gani a wajensu."

Girgiza kai Jamila tayi tace "Zasu wahalar da junansu ne ai, ita dai bata jin magana, cikin sauk'i ba zai ce ta bari ta bari ba, shi kuma ba nauyin duka yake ji ba, amma kaga Amna tana tsoronshi dama, ko had'a ido bata iya wa dashi, kaga za'a samu sauk'i."

"Kema kince wani abu." Ya fad'a yana kallon tvn dake aiki, haka suka ci gaba da hirarsu akan Ammar suna yi suna dariya, a irin hakane har Jibril ya bata labarin wani abu daya faru a shekarun bata da yawo.

*A duk cikin labarin nan wannan labarin da Jibril ya bayar shi yafi sani dariya.*😂
Chapter 116 · 0% Book details