Sashe 48
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Innusa yayan Suley ne ya kwanta rashin lafiya mai tsanani, Suley na shiga gidan ya ganshi sai dai baya samun wani sakin fuska daga kan Ramma har shi Innusa, domin kuwa suna matuk'ar jin zafin ci gaban da yake samu a harkokinshi, dan Suley mutum ne mai k'wazo, duk abinda yasan zai samu riba a kai to ya kan siyoshi ya siyar, ya zama d'an kasuwa da ake ji da shi a wannan lokacin, sannan matarshi da suke gani buzuwa ce wanda a lokacin sun san auren buzuwa *jidali* ne kamar yanda wani mawak'i ya fad'a, har yan uku yaje dasu sun ga baffan nasu har Gambo yana cewa idan ya zama likita zai bashi magani ya warke, Zeeya ce bata je ba dan haka Suley yace taje ta dubashi, kunsan dai halin kayan gidan Suley sai kuwa tace babu inda zata je, wannan karan bud'e mata ido yayi yace wallahi ko a kai ne saiya d'auketa, hakan ne yasa ta shiryawa suka tafi tare da dare, wata atamfa ce a jikinta wacce a wannan zamani sai wane da wane mai sunan *ABC* a jikinta, hak'ik'a tasan mijinta namiji ne na gaske, dan duk abinda zai shigo dashi garin nan komai tsadarshi saiya fara kawo mata shi kafin ya fara siyarwa a gari, d'inkin riga da zane ne aka mata wacce rigar aka mata tattara da robo take ja sosai, kallabin daya kamata ta d'aura shi ta d'aura a k'ugu (wanda kowa yasan a zamanin iyayenmu da kakaninmu wannan ba wani abu bane dan mace ta fita kai sake, musamman idan aka ce ma anyiwa kan gyara), dama kuma ba kasafai aka cika saka gyale ba, sai dai a yafa zanin atamfar a mazaunin gyalen, maimakon ta d'ora zanin ta rufe kanta sai kawai ta ninkeshi gida biyu ta d'ora saman kafad'a, takalminta ta saka bak'ak'e k'afa ciki masu tudu sosai, inda kuma kanta ya ci uban gyara (coiffure) sai k'amshi yake da walk'iya, a haka fa suka jero suka zo har gidan duk da babu nisa, tunda suka shigo matan gidan da yara ke kallonta, hak'ik'a fa ta had'u sosai, sai dai bak'in ciki kawai da hassada ya hanaka fad'an hakan, Suley kawai ke gaisawa da su suna amsawa sama sama yana tambayar mai jiki, saida ya gama tsaf kafin Zeeya ta kalli Ramma cikin ido tace "Ya mai jikin?"
Ita ma kamar yanda ta tambaya haka ta mayar mata da "Mai jiki da sauk'i."
K'ala ba tace ba dan ita ma ba k'aunar su take ba kamar yanda basa k'aunar ta da kuma mijinta da yaranta, tun a labarin daya bata da kuma yanda yanzu suke zaune anan shekara kusan tara kenan ta fahimci haka, ita kuma duk wanda baya k'aunar mijinta da zuri'arta ita ce baya so, dan ita fa tana mugun bala'in son Suley, kawai dai tuna yanda aurensu ya kasance ne da irin zaman da sukayi yasa take jin ba zata iya neman sulhu ba ko ta kyautata mishi, mik'ewa sukayi zasu tafi tana gaba Suley ya ciro kud'i masu yawa ya aje gaban shinfid'ar Innusa yace a siya mishi magani, kullum idan ya zo ya bayar suna karb'a, amma yau Innusa daya kalli matar Suley ya ga ta take nashi matan har biyu, ga uban shirin da tayi sai ranshi ya b'ace, d'aukar kud'in yayi ya watso mishi yana fad'in "D'auki tsiyarka bana so, da can kai kake siya min maganin, ni zaka wa birgar mata, to bana son alfarmarka, dan wannan kud'in ganinsu nake kamar alfarma ce daga gareka, ni kuma duk wata alfarma da zata fito daga wajenka bana buk'atar ta a gidan duniyar nan, Suley babu ni babu kai wallahi na tsaneka."
Zeeya da tunda ya fara magana ta dawo ta tsaya take kallonshi , kallon Suley tayi taga sai doka murmushi take yana girgiza kai, a hankali yace "Allah ya baka lafiya kai dai, nasan zafin ciwo ne."
Haushi ne yasa taji kamar ta mare shi, dan haka ita ta kalli Innusa tace "Ka ce baka son alfarma kowace iri ce indai daga *Suleyy* ta fito?"
Kallonta Suley yayi saboda wani bala'in dad'i da yaji sunanshi yayi a bakinta, bai tab'a jin sunan cikin nutsuwa ba kamar yau, Innusa ne yace "Eh haka nace, ke ba tashi ma kaf zuri'ar shi da zuri'ata ba ma buk'ata, kuma ko bayan raina ban lamunce wani daga cikin tsatsona ya nemi alfarma ko taimakon zuri'ar Suley ba."
Murmushi tayi tace "Ni kuma Zeeya'atu muddin ina numfashi a doran k'asa sai na saka neman alfarmar Suley, idan haka bata faru ba to ka sani zuri'ar ka zata nemi taimakon zuri'ar Suley da ikon Allah, ka rubuta wannan ka aje ka kuma d'auka yanzu fad'an tsakani na da kai ne ba da mijina ba, dan shi yafi k'arfin ajinka yanzu."
Tana fad'a ta juya ta kama hannun Suley kamar yaro suka fita, kallonta kawai yake yana mamakinta, shin abinda aka mishi ne ya b'ata mata rai? To meyasa? Saboda tana sona? To meyasa bata nuna min soyayyar? Da haka suka k'arasa gida har ciki d'aki kafin ta saki hannunshi, ganin kallon da yake mata yasa ta fara cire shirin jikinta dan ta rage ma kanta nauyi, Suley na ganin haka saiya durmiya da ita duniyar maji dad'i daya jima har ya manta rabon da yaje can d'in, ita kanta fa ta gane tayi kewarshi sosai, *wannan rana*, *wannan dare*, shine ya shiga cikin tarihin rayuwar aurensu da ba zasu tab'a mantawa ba, kwana sukayi suna fad'awa juna kalamai masu taushi, kwana sukayi suna gajiyar da junansu da nuna yanda sukayi kewar juna, yan uku ma sai d'akin Husseina suka kwana da sukaji iyayen na su sun k'i bud'e musu k'ofa.
*Abu* kamar ya canza ashe ba haka bane, dan tunda gari ya waye Suley ya fahimci hakan, har yanzu dai ba wata girmamawa tsakaninsu, sai dai duk wannan billin rashin mutumcin da d'aga mishi murya ta daina, abinci ma yanzu har na safiya kawo mishi take ko ta aika cikin yaran wani ya kai mishi, idan an kwana biyu kuma ta kan ziyarce shi har d'akin shi ya d'an samu nutsuwa, kuma duk da haka tana nan tana tunanin hanyar da zata saka Innusa neman alfarma ko taimako wata rana, tana ji a jikinta zamani zai zo da komai zai zama ko dai d'an kud'i ko kuma alfarma, da wannan harta samu tsayayyar magana ta kuma tsaya a kanta.