← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 198

Sashe 30

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihan ce tayi saurin mik'ewa saboda shakkar uwar da take tana fad'in "Sorry Ammie."

Da harara ta bita harta shiga kitchen d'in su Ammie ta d'auko ruwa da lemu har kala uku, tunda ta tashi Saleem ya bi bayanta da kallo, a ranshi yace "Tabbas ke ce *target* d'ina."

Su Bilkis ne suka ce mishi sannu dan shi ba niyyar gaishe da su yake ba saboda hankalinshi baya nan, cike da kunya ya gaishesu har Raihan ta dawo ta dire farantin gabanshi, tunda ya d'ora idonshi a kanta ya kasa d'aukewa, har ta zuba mishi lemun ta mik'a mishi ta mik'e ta koma inda take ta zauna yana kallonta, Fadila ce ta lura da kallon dan haka a ranta taji ita da zai so Raihan d'in ma ya taimaka mata saita samu Abdul ita kad'ai, yana d'an kurb'a lemun ya aje ya mik'e yace zai tafi, godiya Sameera ta masa tace ya gaishe da Abbakar da jiki, kuma insha Allahu zataje ta duboshi dan ta jima rabonta da can, Abdul ne ya mik'e ya d'an taka mishi har k'ofar gida ya shiga motarshi kafin ya bar unguwar.

Yana fita wayar Sameera tayi k'ara, d'auka tayi ta duba sunan taga sarki Imran ne, d'auka tayi tana murmushi da zolaya tace "Allah ya taimaki sarkin Basraba, k'anena ya kake?"

D'aga b'angaren Imran ne yace "Yarinyar nan fa kin gama raina ni, shekara uku na baki amma har kike kirana da k'aninki."

Cikin dariya tace "Amma dai kasan k'anwata kake aure ko?"

Saida ya kalli Ameera wacce ke mik'o mishi smootie d'in ayaba yace "And so what? Ni kuma yayanki ne."

Cikin dariya tace "To ya garin na ka mai martaba?"

Imran ne yace "Muguwa, ban sani ba to, kina son sanin yanda garin yake da aka ce za'a baki mulkinshi kika ce ba kya so? Gashi kinsa duk an takura ni ta ko ina."

Tunda ya fara magana take dariya saida ya tsaya tace " Ai na fad'a muku ba zan iya mulki ba, amma ko yanzu bata b'ace ba ai, idan ka samu labarin wata masarautar zata kawowa taku hari to kayi gaggawar sanar dani dan mu shirya dakaru ni kuma zan jagoranci yak'in."

Murmushi Imran yayi yace "Ke 'yar bala'i ko? To bama fatan tashin hankali mu.

Kafin tace wani abu yace "Ina mamana take da yarana?"

Saida ta kalli Ammie tace "Duka lafiyarsu k'alau, ina yaran nawa da yar uwata?"

Katseta yayi da fad'in "Dakata dallah ki saurare ni, serious magana fa na kiraki muyi."

Mik'ewa tayi daga wurin ta shiga bedroom d'in Ammie ta zauna bakin gado tace "What's the matter?"

Nan ya kwashe komai ya fad'a mata duk yanda ake ciki kafin ya d'ora da "Yanzu haka ban fad'awa Umma ba, dan nasan halinta ba wani farin ciki zatayi da zab'in na takawa ba, haka ma sistern ki ban san ta yanda zan fara fad'a mata ba, please Sam tell me what do i do now, wallahi i'm confuse."

Dariya Sameera tayi tace "Hey! What trouble in this issue? Listen to me brother, maganar nan babu wata matsala ko tashin hankali, ka samu aunty ka fad'a mata komai dake faruwa, sannan ka jira abinda uncle da liman zasu tattauna, idan har maganar ta fad'a shine saika samu Ameera ka fad'a mata, i hope zata fahimce ka d'ari bisa d'ari."

Ajiyar zuciya ya sauke yana hangen Ameera dake gyaran kayanshi yace "Ok, yanzu zanyi abinda kika ce, but make me sure k'anwarki ba zata d'aga min hankali ba."

Dariya tayi tace "I'm verry sure, kai dallah rago wallahi ka cika tsoro, kamar dai ba jinin *Ali zaki (Haidar)*."

Wata sayayyar ajiyar zuciya ya sake saukewa yace "Babu abinda ke kayar min da gaba a duniyar nan kamar idonki dana Ameera, sometimes bana iya kallon k'wayar idonku na fad'a muku abinda ke raina."

Tashi tayi zata fito tace "Matsoraci, u know me ai tha's why u scrad me."

Daga inda yake yace "God forbid na ji tsoronki, kema duk iskancin ki ai kina shakkar wannan yaron."

Zaro ido tayi tace "La la la la, mijin nawa ne yaro? Kai amma sarkin nan baka da mutumci aradu, amma ba komai kai da yallab'ai ne, zai sameka har Basraba dan kayi repeatn abinda ka fad'a."

Yasan tsaf Abbas zai titsiyeshi kan ya maimaita kamar yanda tace, shiyasa yace "In dai kina k'aunar iyayenmu karki fad'a masa, abinda ma a daren nan jirgi na zai tashi zuwa Belgium (ya fad'i hakane dan tayi tunanin zai bar garin)."

Dariya tayi tace "Fad'uwa ta zo daidai da seat kenan, ai shi tuni ya rigaka isa can."

Da sauri yace "No wonder yau mukayi magana dake perfect, banji yana ta min iskanci ba ko yana shinshinarki yana kissing d'inki ba, ashe jarababben baya gari."

Dariya tayi harta fito suna ci gaba da raharsu, cikin zolaya yace "Dallah ni bani uwata na kwashi albarka."

Saida ta k'araso kusan Ammie tace "What are u eaten na baka na following down? Gata in dai Ammie duk tsiyarka zaka bar min abata."

Ammie ta ba wayar suka gaisa harda su Imranatu ma da sauran yaran kafin daga bisani suyi sallama.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Sai dare kad'ai Imran ya samu uwar d'aki ya fad'a mata abinda suka tattauna da takawa, ranta ya kai k'ololuwa wajen b'aci, ace d'an ta kuma babban d'anta wai ba zai iya fara sirri da ita ba, ba yabo ba fallasa ta nuna mishi ai ba komai kawai Allah yasa alkairi, dan tasan waziri zai lalata komai, shi kuma mamaki ne ya sa shi mik'ewa da k'yar ya mata sallama.

*Me waziri zaiyi? Wa sarki zai aura? Me zai samu takawa?*

_See u.✋_
03/06/2020 à 23:33 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_7_

"Dan Allah baiwar Allah ki tsaya, zo ki shiga mota saina kaiki duk inda zaki je."

Kasa had'a ido tayi da shi sai lumshe ido take kamar jiri zai deb'eta, jin ba tace komai ba sai k'ok'arin tafiya da take yasa ya sake tareta yace "Ki dubi girman Allah baiwar Allah ki saurare ni, ki zo na kaiki asibitin, zan taimakawa mahaifinki ya samu lafiya, karki d'auki abinda ya faru yanzun da son raina nima wall..."

Bai k'arasa saboda tafiya data fara yi, ji take kamar ta watsa mishi mari ko guda goma ne ko ta huce, amma kuma tsoronshi take ji, karta mareshi ranshi ya b'ace ya sake murk'usheta a wajen, dan ta fahimci sunyi hannun riga da imani, sake wucewa tayi ko kallonshi ba tayi ba bare ta saurare shi, shi kuma tausayin yarinyar ne ya kama shi sosai, juyawa yayi yana kallonta tana tafiya da k'yar waacce ya gani cikin karsashi wani lokaci daya wuce, wata zuciyar ce ta fad'a mishi "To me kenan kayi Jibril? Ka lalata rayuwar yarinyar daka had'u da ita yanzun nan? Yarinyar da ko sunanta baka sani ba, shin baka tunanin sanadiyar abinda ya faru ta rasa mijin aure? Ba ma wannan ba Jibril, shin kasan me zai iya biyowa baya sakamakon hakan? Kai tirr da wannan rayuwa taka."

Da gudu ya sake tare gabanta kamar zai rik'e ta saboda yanda ya bud'e hannayenshi a dole tareta zaiyi yana fad'in "Kinga baiwar Allah, dan Allah ki zo muje mota sai mu tafi tare, na amince ki kaini wajen iyayenki na taimaka miki, idan har mahaifinki ya samu lafiya na miki alk'awarin zan aure ki, ki zo muje dan Allah."

Wani kallo ta watso mishi dake nuna me ka d'auke ni? Amma ba tayi magana ba ta sake giftawa zata wuce, hijabinta ya rik'e tana juyowa suka had'a ido, ruwan dake sauka da k'arfi ne suka fara tsagaitawa a hankali, cikin raunin murya yace "Idan ba zaki aminta da ni ba dan Allah ki fad'a min sunanki da gidanku, zan zo, zan zo wajen iyayenki na nemi izinin aurenki."

Wasu hawayen takaici ne taji sun taho mata bata shirya ba, wai yau ita ce wani namiji da bata san shi ba kuma akan hanya ya mata fyad'e, kamar a film ko kuma tatsuniya, ko kuma kamar ana rayuwa a garin maguzawa, da k'arfi ta bige hannunshi ta sake juyawa tayi tafiyarta, baya da zab'in daya wuce ya shiga motarshi ya tayar ya bi bayanta, ba jimawa suka isa asibitin, tana zuwa a k'ofar d'akin da mahaifinta ke kwance ta samu duk dangi an fito sai sharar hawaye suke, mahaifiyarta da ke kuka sosai ta matsa kusanta tana tambayar lafiya, shirun da kowa ya mata ya tabbatar mata da mahaifinta ya rasu, Mari na gamsuwa da abinda zuciyarta ta fad'a mata sai lokacin ta ji wani azababben kuka na bak'in cikin mutuwar mahaifinta da abinda ya faru da ita yanzun, durk'ushewa tayi wajen ta fashe da kuka sosai kamar ranta zai fita, nan dangi har da kakarta suka dinga rarrashinta suna bata hak'uri, amma Mari ta zama kamar dutsi ko jinsu ba tayi sai kuka kawai, duk abin nan dake faruwa a idon Jibril dake hangensu daga nesa, lura da abinda ke faruwa yasa ya k'ara jin ba dad'i sosai, gyara tsayuwa yayi da niyyar ko zai kwana nan sai ya ga gidansu, amma rashin sa'a sai kiran gaggawa ya shigo wayarshi cewa ana nemanshi, dan a lokacin bai jima da fara aiki da wannan projetn ba, kawunshi Gambo ya shiga gaba har saida ya ga ya samu wannan aikin, dan haka baya da zab'in daya wuce ya shiga motar ya bar wajen.

Ko da ya isa inda suka sauka ya d'auka kira ne na ka zo yanzu ka koma, ashe a lokacin wani abu ne ya taso da dole za'a tura su wani garin, kuma shine zai wakilci tawagar, haka suka kama hanya zuciyarshi kamar zata fashe, ya rasa meke mishi dad'i a rayuwa, kamar ya fasa ihu yake ji ko zaiji sauk'in abinda ke ranshi.
Chapter 30 · 0% Book details