← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 198

Sashe 78

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki yayi ya kashe wayar, hakan kuma yasa Abdullahi yarda d'ari bisa d'ari cewa zai zo, dan haka ya ci gaba da tsayuwa a bakin titin, ai kuwa baifi minti ashirin ba saiga motar Ammar, dan dama yasan gidan da jimawa dan anjima ana ma gidan tsare tsare tsare da tanadi, k'arasawa sukayi k'ofar gidan Abdullahiya shiga ya samu su Hamna cirko cirko su biyar a farfajiyar gidan, Hamna ya kalla yace "Hamna ki taso ga Ammar nan zai tafi dake."

"Wa!? Ta fad'a da k'arfi tana zaro ido ta d'ora da "Waya fad'a mishi ina nan? Meyasa sai yanzu ya zo bayan ban ganshi d'azu ba?"

Abdullahi ne yace "Yanzu dai ba lokacin magana bane ki taso ku tafi kafin ya mana tijara ni dake."

Mik'ewa tayi tace "Ina zuwa." Cikin d'akin ta shiga ta samu amaryar tare da babbar yayarta tana k'ara gyara mata d'aki, uwar d'aki suka shiga Hamna tace "Dan Allah k'awata taimako zaki min."

"Taimakon me kuma k'awata?" Cikin fargaba tace "Yah Ammar ne ya zo d'auka ta, kuma jiya ma a wurin kamun ku saida ya min fad'a kan fita babu hijabi, shine nake so dan Allah ki ara min ko da babban mayafi ne, insha Allahu gobe idan na taso daga école zan biyo na kawo miki."

Murmushi tayi ta nuna mata wurin kayan tace "Besty akan wannan ne har kike cewa wani taimako? Ki duba ga kayan nan sai ki zab'a."

"Yawwa." Ta fad'a tana bud'a wurin kayan, wani babban mayafi ta d'auka wanda ya dace da kayan nata, ita kanta data kalli madubi sai taga tafi kyau da kamala, sai ta ganta kamar wata amaryar ita ma, fitowa tayi zata fita sauran k'awayen suka ce ai ba zata barsu ba, tare suka fito inda ta zagaya zata shiga motar, da kallo ya bita har ta shigo, amma take jikinshi ya bashi wannan ba mayafinta bane, cikin lallami Abdullahi ya zuro kai yace "Abokina ka taimaka ka aje wad'annan ma mana, in kayi haka zaka samu lada fa."

Kallonshi yayi fuskar nan a d'aure yace "Me zai hana ka basu makwanci a gidan naka? Ai sabgaka suka zo? Ni munyi da kai zan zo d'aukar maka mata ne?"

Murmushi Abdullahi yayi yace "Ba haka bane, amma dai ka taimaka."

Mayar da kallonshi yayi kan titi yace "Kasan zasu rage maka jin dad'i kenan? Shine ni ma zaka takura min."

Kallon yan matan yayi da suka saki baki suna kallonshi yace "Ku muje."

Da sauri wuka bud'a suka shiga suka zauna, ko kallon Abdullahi baiyi ba ya ja suka wuce, saida sukayi tafiya mai nisa babu mai magana kafin ya daidaita madubin gabanshi yana k'arewa yan matan kallo, a ranshi yake k'yamar irin shigarsu kamar ba yaran musulmi ba, babu wacce babu k'arin gashi a kanta da muguwar kwalliya ta d'aukar hankali, girgiza kai yayi ya juya ya kalli Hamna, sai kace wata malama k'wafa yayi ya ci gaba da tuk'i, sunyi nisa muryar d'aya daga cikin yan matan tace "K'awa Hamna da kina da yaya kyakyawa haka shine bamu sani ba?"

Wani buhun haushi ne ya tasowa Hamna, tasan halin k'awarta dan haka ta d'aure fuska ta kalli Ammar da yake tunanin kalar iskancin da zai tatawa yarinyar, tab'e baki tayi a zuciyarta tace "Wai kyakyakwa, humm."

Ammar kuma juyawa yayi zai kalli k'awarta ta sai kuma ya ga ita sai wani had'e fuska take, kallon gabanshi yayi hakan yasa k'awar cewa " Yayanmu mun gode fa daka d'auko mu, dan har mun fara tunanin k'aryar da zamu fad'a a gida zuwa gobe."

Cike da shak'iyanci yace "Karki damu, ai mace irinki tafi k'arfin ta rasa mai sa'ar da zai d'auko ta, ni ne da godiya."

Fasa mata kai yayi da wannan maganar tashi, sai kawai tace "Nagode, amma nima sa'ata ce ace na shiga motarka har muna musayar yawu da kai."

Tsaki sukaji wanda yasa shi kallon Hamna da tayi tsakin, to na meye? Haka kawai taji ranta na b'acewa sai kumbura take, kamar Ammar yasan me take ji a zuciyarta sai kuwa ya biyewa k'awar suna ta hira, saida aka kawo inda zasu sauka tace "Mai kyau zaka iya aje ni anan ma."

Da murmushi yace "To mai kyau." Pakawa yayi su biyu suka sauka ya zuro kanshi yace "Bansan nawa ne farashin lambar wayarki ba, amma zan so ki fad'a min komai tsadarta zan biya dan a bani."

Cike da duniyanci tace "Farashinta mai tsadar gaske ne, amma kai na musamman ne, dan haka kawo wayarka na saka maka kyauta."

Cikin fara'a ya mik'o mata wayar yace "Ina godiya da wannan karamcin."

Tana cikin saka masa tace "Ai karrama mai karamci yafi k'arfin iyawata ni kad'ai, kai babban mutum ne."

Saida ya saci kallon Hamna yayi murmushi yace "Kinsan ba kowa yake gane girma da darajarka ba, wasu idan sukaga suna rayuwa tare da kai sai su mayar da kai kamar abun banza."

Bashi wayar tayi ya amsa tana fad'in "Ka rabu da su kawai, zasu fahimta ne a sannu duk ranar daka mallaki wacce zata dinga nuna musu darajar taka."

Wani murmushi yayi na iskanci yana goge lambar yayin da ita kuma take tunanin yana saka lambar ne a wayarshi yace "Ke wasu fa mahaukata ne basa fahimta duk yanda zakiyi da su, ki barsu da shan kayan ruwa kawai suna cika musu mafitsara."

Dariya tayi sosai yayin da sauran kuma sukaji kunya, kamar tasan da Hamna yake sai cewa tayi "Barta kawai, zan dinga fahimtar da ita matsayinka ko ta fara ganin girmanka."

Ammar ne yace "Amma zan iya sanin adadin matakan tsaron dake gidanku? Domin idan na tashi zuwa nasan irin shirin da zanyi."

Murmushi ta masa tace "Ka zo duk sanda kake so, zaka samu k'ofa a bud'e."

Da wani yanayin shegantaka yace "Allah ko?" Ita ma a salon wayewa ta marmad'a masa ido, hannu ya zuro ya bata da niyyar su gaisa yana fad'in "Saina kiraki mai kyau."

Bashi hannu tayi wanda yasha akaihu zargama zargama ita ma suka gaisa tace "Sai na jika mai kyau."

Kashe mata ido yayi ba tare daya saki hannunta ba yace "Za dai ki jini a waya mai kyau, amma jina ai sai bayan aure."

Murmushi tayi harda sunkuyar da kai tana d'an matsa hannunshi mai laushin gaske tace "Har kasa na fara tunanin kaina a matsayin matarka."

Kallon wannan mahaukaciya ce ya mata yace "Ni fa tunda na ganki nake jin ina k'amshin lalle."

Cikin b'acin rai da jin kamar ta rufe shi da duka tace "Dan Allah ni muje ka kaini gida na gaji da jin wannan zancen na ku."

Juyowa yayi ya mata wani kallon zan ma ci ubanki ne yarinya, kawar da kai tayi shi kuma ya saki hannun k'awar ta ta yana fad'in "Saida safe."

Jan motar yayi suka wuce har saida ya aje sauran ma kafin suka d'auki hanyar gida, babu mai magana ko kallon wani har suka kusa isa gida, a daidai su sha kwana motar police ke nan da alama wucewa zasuyi motar ta samu matsala, haka kawai wani police ya tsayar dasu, tsayawa yayi ya sauke madubin motar yana kallonshi daga shi har shi kowa fuska babu annuri, police d'in ne yace a harshen fransanci " Malam daga ina haka a daren nan?"

A hankali Ammar ya kalli agogon hannunshi k'irar gucci ta fata, ganin duka yanzu ne k'arfe *11:18* na dare yasa ya kalleshi yace "Daga inda ka aike mu mana."

Da alamar tambaya police d'in yace "Me? Malam wace irin amsa ce haka? Tambayarka muke daga ina kake?"

"Amsar kenan na baka, akan me zaka tare ni yanzu kana tambayata daga ina nake?"

Hassala yayi yace "Wai waye kai da zaka ce ba za'a tambayeka ba? Kafi k'arfin doka ne ko me? To fito daga motar sannan ka bamu takardun motar."

Murmushi yi wanda har yasa Hamna tsorata dan tasan k'aramin aiki ne yayi bala'i da shi yasa su kwana a gark'ame, murfin motar ya kama zai fito yana fad'in "Bara na fito kaga tsawo na to."

Cak ya tsaya saboda hannunshi da Hamna ta rik'e, yana kallonta ya ga hawaye har sun cika idonta, cikin rawar murya tace "Dan Allah ka basu takardun mu wuce."

Fizge hannunshi yayi yace "Sake ni dallah, ni zai nunawa wannan k'azamin kakin nashi, waye shi da har zai tambaye ni waye ni? Bari na nuna masa daidai nake da shi, uban wa ma ya bashi damar tsayawa nan d'in."

Zai fito ta sake rik'e rigarshi hawaye suka zubo mata tace "Dan Allah fa nace yah Ammar, ina jin tsoro."

Da k'arfi ya kawar da kanshi daga kallonta saboda jin zafin ganin hawayenta da yayi, police d'in dake tsaye ne yace "Kai nake jira ai ka fito, madame ki barshi mana naga me zaiyi, naji kana fad'in wai k'azamin kaki na, to fito na nuna maka k'arfin ikon kakin nawa."

Cikin hassala da k'ufula ya daki sitiyarin motar da k'arfi, yana son ya fita ya nuna mishi bai tsoronshi sai dai ya kulleshi, amma kuma baya son ganin Hamna cikin damuwar nan, ganin hawayen ta ma yasa shi jin babu dad'i haka yasa shi dole ya juyo ya kalle shi ya saisaita nutsuwarsa ya k'ak'aro murmushin na ganeka kuma zamu had'u ya masa yace "Yallab'ai, ka barmu mu tafi mana, madame d'in nan rigima ce da ita, kasan mace mai ciki saurin hawa."

Jin haka sai police d'in ya k'ara jin wata izza ai sai yace "Kawai ka fito daga motar ka bamu takardunka, yo har mu zaka d'auka wasu sakarkaru har kake fad'a mana magana, yau zaka gani."

Kallon Hamna yayi ita ma ta mishi kallon taimaka ka basu dan Allah, hakan yasa yace mata "Akwai takardun, amma wallahi ba zan bashi ba."

D'aya daga cikin wanda suke tare ne yana duba motar ya matso yace "Ya dai? Lafiya?"

Kafin police d'in yayi magana Ammar yace "Abokina wannan mutumin ne ke son b'ata min lokaci, to wai halan baya da aure ne? Inba haka ba ai da zai fahimci larurar da kan iya saka miji fitowa a dare kuma tare da iyalinshi, ka ganta nan."
Chapter 78 · 0% Book details