← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 198

Sashe 4

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hajia Zeinabu* (mahaifiyar Junaid) ce tace "Um um fa Hamna, hanyar lafiya abita da shekara, tunda yace ku kashe to ku kashe, ko kuma ki jasu kuje d'akin ku sai kuyi acan."

Wata kyakyawar mata mai k'aramin jiki ce fara kuma doguwa ce tace "Saboda yace baya so shikenan sai a daina? Me zai hana ya fita waje tunda namiji ne shi, amma yana cikin gida kamar wata garar kunya."

Zeinabu ce tace "Da dai kin basu shawara su koma ciki zaifi ai."

Hamna ce ta kalli yaran tace "Kai mu ci gaba da nishad'inmu, kunsan boss ba fara'a yake ba bare maganar nishad'i, shi ya sa yake kishi da duk wanda yake yinsu."

Tana maganar ne tana amma sai taga yaran kowa yayi zaune tare da mak'alewa wuri d'aya, tab'e baki tayi tace "Sai kace mala'ika nr shi daga ya turo sak'o ta waya amma duk kun tsorata."

Kallonta ne ya kai kan Amna data kafeta da ido, cikin dubara Amna ta d'ora hannunta a bakinta da yatsa d'aya take mata nuni da k'ofar shigowa falon, da k'yar ta fahimci abinda take nuna mata ta juya dan ganin ko meye, ai ko ido cikin ido suka kalli juna ita da Ammar wanda yake tsaye k'ik'am ya cije gefen labb'enshi na k'asa, ai da gudu Hamna ta koma bayan Ummi tana mata rad'a wai "Dan Allah Ummi ki bashi hak'uri mu samu ya bar gidan nan."

Ummi da tunda ta ganshi ta had'e rai kamar dai shi kalloshi take sosai, ganin yanda take kallonshi yasan sai ranshi ya b'ace in yayi magana, dan k'aramin aiki ne a gurin Ummi ta zageshi a gabansu har ma tayi yunk'urin marin shi, dan haka yayi k'wafa ya juya ya bar d'akin, yaran na gabin haka suka daka tsalle da shewa wai ya tafi bai dake su ba.

Yana barin nan kai tsaye asibitinsu ya wuce mai sunan *Clinik Aminci*, (na canza mata suna saboda kar na saka na ainahin sunan familyn ya fito fili), yana zuwa ya fito daga mota ya tunkari shiga ciki, a babban falon da mutane ke zama ya samu duk gurin zaman an cikeshi, kuma yana da tabbacin wanda yake da rendez-vous (appointment) da su ne, wata irin sallama ce yayi wanda na farko kawai yaji shi sai wanda suka ga bakinshi ya motsa, dan ranshi b'acewa yake idan ya zo asibitin ma, a ganinshi da yanzu watak'ila yana filin daga suna bada wuta, amma an zaunar dashi yana tambayar lafiyar mutane (mutum baya sanin abinda yake, haka kuma baka sanin mahimmancin abinda ke hannunka saika rasa shi), malamar asibitin dake zaune akan babban teburi wacce ita ke kula da wanda zasu shiga da kuma fara duba lafiyarsu, kallonshi kawai tayi dan ko ta gaishe shi ma ba amsawa zaiyi ba, tsaye yayi gabanta ya sauke jajayen idonshi akanta yace "Zan shiga, su bi layi da kyau, a kuma dinga shiga da hanzari saboda gudun b'ata min lokaci."

"Ok docteur." Ta fad'a tana bin bayanshi da kallo, tab'e baki tayi tana gunguni tana fad'in "Kamar dai ba *Sa'ada* ce ta haife shi, ita faran faran da mutane, shi kuma sai shegen tsamin rai, Allah ya sawak'e maka."

Yana shiga ya mayar da k'ofar ya rufe, makullin mota da wayarshi ya aje akan tamk'amemen teburin dake gabanshi tare da zagayawa wajen wani d'an dogon k'arfe ya zago fara kuma doguwar rigarshi ya saka, abin sauraren numfashi ya d'auko kamar zai saka a kunnuwa sai kuma ya sagalashi a wuya, kujera ya ja ya zauna ya gyarawa abin auna hawan jini zama, wani k'aramin coffre ya bud'e ya d'auko wani farin gilashi ya saka a idonshi, masha Allah, abinka ga kyakyawa kuma farin mutum, sai yayi kyau cikin shigar kamar ka daga da bredi, matsalar d'aya ita ce d'aurewar fuskar nan da babu annuri a cikinta, wani babban littafin ya d'auka ya ciro alk'alami a jikin rigarshi ta ciki ya fara rubutu, ba jimawa da fara rubutun kuma aka k'wank'wasa k'ofa tare da bud'awa aka shigo,sam baiyi alamar yasan da zuwan mutum ba saboda ko d'agowa baiyi ba, har saida matar ta zauna tare da kafeshi da ido, saida ya gama abinda yake ya d'ago a hankali ya sauke ido akan matar na yan dak'ik'u, hannu ya mik'o mata alamar ta bashi katinta da kuma takardun rahoton lafiyarta, da sauri ta mik'a mishi saboda ita tsoro ma ya bata, saida ya gama dubawa da rubuce rubuce bai kalleta ba yace "Ki kwanta kan gadon can."

Tashi tayi ta nufi wajen gadon da aka keyawa ba'a iya ganin wanda ke ciki ta kwanta, tashi yayi ya fara dubata na wasu mintoci kafin ya dawo ya zauna, dawowa tayi ta zauna ita ma tana kallonshi yana ci gaba da rubutu, ya jima kafin ya mik'o mata takardun sai takardar siyan magani yace "Wannan takardar ki bawa wannan likitar dake zaune."

Wata takardar ya mik'o mata yace "Wannan kuma asiyo wad'annan magungunan yanzu, dukansu kina buk'atarsu domin zasu taimaka miki."

Mayar da kanshi yayi k'asa ya fara rubuce rubuce, tashi tayi ita kuma ta fita jiki na rawa dan tayi abinda yace, da haka Ammar yake duba duk wani majinyaci daya shigo har saida lokacin tashinshi yayi, ak'alla awa biyu ya d'auka a asibitin kafin ya tattara ya nufi gida a gajiye, wasu mintuna ne suka kawo shi gida, yana zuwa kuma a k'ofar gida ya samu Hamna tare da wata k'awar ta akan moto da alama tafiya zatayi, tsaki yayi ya shige ciki kai tsaye kuma b'angarensu na samari ya wuce, tun a falon ya tarar da su Amar da su Junaid, kallonsu kawai yayi ya nufi na shi d'akin, Junaid ne yace "Likita bokan turai, baka so a mutu baka so a zauna lafiya, daga asibiti ake halan?"

Tsaye yayi ya rik'e k'ugu ya kalleshi kamar zaiyi magana sai kuma ya wuce, Jibril ne yace "Oh mu 'yasu, mu dai mun shiga uku kam, jama'a namiji da jan aji da yanga kamar wata sabuwar bazawara, wannan naga mai auren shi a duniyar nan."

Dariya Amar yayi yace "Za kuwa ka ganta da idonka, ai irinsu kuma Allah yake had'awa da masu shegen surutu."

Karaf Jibril yace "Kamar irinsu Hamna ba."

Wata harara Junaid ya wurgo masa yace "Ka rufa mana asiri kafin zaman d'akin nan ya gagare mu, yana jin wannan maganar a bakinka Allah saiya maka tiyata a baki."

Dariya suka saka inda suka ci gaba da tattaunawa cikin nishad'i, amma abin haushi duk hirar dangin nan da suke Ammar na d'aki na jin hayaniyarsu yayi shiru har bacci ya d'auke shi.

*Washe gari*

Jiniyar motoci ce ta tashi wasu daga cikin mutanen gidan, daga ciki har da Ammar da Hamna da kuma Amna, sanin ko waye yasa Hamna ko suturta jikinta bata tsaya yi ba daga kayan baccin dake jikinta ta fito, da gudu take saukowa daga matakalar tana fad'in "Abbanmu ya zo, Abbanmu ya zo, Abbanmu ya zo."

*GVR* de Maradi (gwamnan Maradi) *Harouna Suley Hassan Gaga* (Gambo) kenan, mahaifin Hamna da Amna, wanda suke kwashe watanni basu saka shi a ido ba saboda yanayin aikinshi, yanzu haka ma yayi sammakon zuwa ne sabida k'arfe *09:00* zai halarci wani taro na k'addamar da wata sabuwar gidauniya da za'a bud'e, shiyasa ya zo dan ya samu ko da awa biyu ne da iyayenshi, 'ya'yanshi wanda yan uwanshi ke kula dasu da kuma sauran 'yan uwa, kuma bayan rabuwarsu da mahaifiyar su Hamna ya auri wata mata mai sunan *Salamatou*, yar asalin garin Niamey ce bazabarma (zarma), suna tare da ita acan babban birnin niamey, shiyasa ganinshi ma ke zama aiki, dan ko a waya ka kirashi sai ka taki sa'a kake samunshi.

Masha Allahu, gaskiya 'yan biyu akwai kyau kuma kyauta ce ta Allah, uwa uba kuma 'yan uku, cikin d'an takon hanzari yake shigowa falon tare da yi wa masu tsaron lafiyarsa alamar su jira shi, Hassan da Hussein da suka fito cikin shirin fitarsu kowane da kayan aikinshi ne ke tunkarowa suma saboda ganin d'an uwansu rabin jikinsu, sak iri d'aya su ukun, kayan jikinsu ne kawai ya banbanta su, sai dai kuma shi Gambo ya d'an fisu kumari, ganin irin farin cikin dake kan fuskokinsu yasa ya yanke shawarar k'in fad'a musu abinda ya kawoshi, zaiyi shiru har kowa ya gama tafiya wajen aikinshi, kafin su dawo kuma yasan ya bar garin, rumgume juna sukayi dukansu saboda farin ciki, ba jimawa suka raba jikinsu suna kallonshi, Hassan ne ya d'an bugi tunbinshi yace "Meye haka kai kuma? So kake ka zama luti ka barmu, wato kana so a dinga cewa kaine babba garemu ko?"

Murmushi yayi ya gyara babbar rigarshi ta shaddarshi ruwan madara wacce ta dace da shi yace "Ai babba babba ne, kaifa ka fara zuwa duniyar nan kafin mu, kaga kuwa dole mu baka girmanka."

Cikin had'add'en fuskar da babu annuri Hussein dake gyara d'amarar shi ta kakinshi na soja yace "Girman guda nawa ne, ko na minti biyar fa bai kai ba."

Kallonshi Hassan yayi ya kai hannu yana k'arasa sakawa Hussein d'in mab'allan rigarshi kamar wani yaro yana fad'in "Soja mazan fama, ai ka ma rik'e girman nawa na bar maka."

Dukansu ne suka juya saboda muryar Hamna dake kiran Abbanmu ya zo suka kalleta, ganin riga da wando ne a jikinta na bacci yasa Gambo daka mata harara har yana mata nuni da yatsa yace "Maza kije ki canza kayan nan, wai ke yaushe zakiyi hankali ne?"

Cak ta tsaya tare da turo baki gaba, juyawa tayi harda bubbuga k'afa ita bata so ba, Hassan ne yace "Daga zuwanka fa ba zaka fara takura min 'ya ba."

A lokacin Hussein na gyara zaman jar hularsa mai d'auke da lambar girma yace "Idan ya takurata ka kira ka fad'a min, zan nuna maka inda nake ajiyar bindiga ta."

Yana fad'a yasa kai zai nufi d'akin Hajia dan gaisheta cikin wani irin tako kamar wani ingarman doki, (ni fa sai lokacin ma na ce duk d'abi'un shi kamar Ammar, ko kuwa Ammar d'in ne kamar shi) da sauri Gambo yace "Ina kuma zuwa bayan na zo?"

Ko juyowa baiyi ba yace "Zuwanka kuma ba zai dakatar dani daga tafiyar nan da zanyi ba."
Chapter 4 · 0% Book details