← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 198

Sashe 146

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juya fuskarta yayi ko saurarenta baiyi ba ya saita daidai huje na biyu wanda ke sama ya turtsa mata d'an kunnen nan, wata uwar ihu ta saki jin abun ya zo mata bata shirya ba, cikin azaba da rad'ad'i ta fara fad'in "Dan Allah kayi hak'uri ba zamu k'ara ba yah Ammar, zan mutu wallahi dan Allah ka d'aga ni na tuba wallahi."

K'ok'arin juyo d'aya b'angaren ya shiga yi yana fad'in "Yo ku k'ara mana, ai ba musaki bane ni da zan kasa rama mata ba."

Da k'arfi ya juyo d'aya b'angaren ya janye hijabinta nan ma ya jawo kunnen ya saita shi, shima burmuk'a mata yayi na uku kafin ya d'agata yana d'aukar yarinyar yace "Shiru shiru yar baba, tuni ubanki ya d'auki fansa, a shirye muke da duk abinda zai faru ya faru, ba tsoron bala'i muke ba."

Ummy da taji kukan yarinyar ya k'i k'arewa kuma k'arshe taji na uwar yasa ta shigowa d'akin ko sallama ba tayi ba dan tasan d'anta ne ke wani mugun abun, ai kuwa ta samu Amna sai sharar hawaye take da hijabi tana rufe kunnenta, matsowa tayi tana musu kallon tuhuma tace "Me ka mata ita kuma?"

Kallonta yayi yace "Ki tambaye ta Ummy tasan abinda tayi."

Kallon Amna tayi tace "Me kika mishi?"

Cikin rage sautin kukan tace "Ba komai Ummy, marata ce ke ciwo."

Kallon tuhuma ta masa dan bata yarda ba, jinjina kai tayi tace "Karb'i yarinyar ki zo falo to."

Mik'ewa tayi ta tara masa, saida ya kalli idon Amna yace "Gata nan amana na baki, aka sake cutar min 'ya sai ranki ya b'ace."

Juyowa Ummy tayi ta kalleshi jin abinda ya fad'a, shima kallon Ummy yayi yace "Ummy waya ma yarinyar huje saboda Allah?"

Da d'an mamaki tace "Tantinku ce *Zuweira*, da matsala ne?"

Jinjina kai yayi ya nufi kan gadon ya d'auki yan kunnen daya ma Amna huje dashi yace "Yau ko zata ga rashin mutumci wallahi, dama ba shiri muke da ita ba saboda tana kirana da mai kamar shaye shaye, to yau zan mata aikin da ko mai shan cocaïne ba zai mata ba."

Da sauri Amna ta rik'e rigarshi ta baya ta kalleshi tace "Dan Allah yah Ammar ka rufa masa asiri, kasan halin tanti Zuweira fa."

"To sai me? Ita tasan nawa halin amma kuma ta aikata min wannan ta'asar."

Ummy dake kallonsu cikin rashin sani ne tace " Wai miye ya faru?"

Da sauri Amna ta kalleta tace "Ummy dan Allah ki bashi hak'uri karya je."

Kallonshi Ummy tayi tace "Miye wai?"

Ba tare da fargaba ba yace "Ummy huje aka mata bata isa ba, shine zan rama mata."

Zaro ido tayi ta matso kusan Amna ta d'aga hijabinta, tana ganin kunnenta ta kalleshi rai a b'ace tace "Me kayi haka Ammar? Me yasa wai kai duk abinda ya sab'a ma hankali shi kake aikatawa? Hujen daya zama dole dan an ma yarinya shine ka rama kan uwarta, me kenan hakan ke nufi? Ka fita k'aunarta ne?"

Cike da rashin ko in kula yace "Haka aikinta ya nuna bata k'aunarta."

Cikin jin haushi ta nuna mishi k'ofa tace "Fita a gidan nan, ko ko k'ala ban yarda ka fad'a ma Zuweira ba in dai ni na haifeka."

Saida ya rusuna yace "Angama."

Fita yayi yana zuwa falo yayi tsaye yana kallon Zuweira dake shan kunu a babban roba tana ta hira abinta, saida ya rik'e k'ugu ya dinga motsa bakinshi yana fad'in "Shirgegiyar wofi, ki samu yar jaririya ki taushe da uwar cinyarki ki mata hujen, kuma tana kuka hankalinki kwance kina shan kunun da ubanta ne ya siyo hatsin yake biyan ruwan da aka dama kunun, kai amma matar nan fa akwai yar rainin hankali, yau kinci albarkacin Ummy da sai na cire miki zaninki ta kai, amma ba komai ai akwai wata rana."

K'wafar da yayi ce tasa hankalin wasu dawowa kanshi wanda basu kula dashi ba, Ummy suna fitowa tana fad'a ma Amna cewa "Kiyi hak'uri kinji, kar ma ki bari kowa ya sani, ki k'yale shi kawai."

*A gurguje fan's*

Komai ya tafi daidai inda Ammar yayi iya bakin k'ok'arinsa wajen gwangwaje amaryar jego da yaranta, saida ya mata d'inki kalar shida na tanfatsa tanfatsa leshi da shadda, ranar suna kuma kamar yanda ya fad'a ne sunansu ya mayarwa yaranshi, ranar biki gidanshi dake nesa da nan suka zauna shi da abokansa inda Amar dasu Junaid suka d'auki nauyin abinci da abin sha. A gida kuma ko Hamna saida sukayi d'inki har kala uku ita da Amna, anci an sha anyi bidiri sosai an gode Allah sai fatan Allah ya raya yaran.

Bayan kwana shida kuma akayi bikin Jamila ita ma, bayan biki Zeinabu ta so ta koma d'akinta sai Jibril yace kawai su barta har ta gama wankasaita koma. Umaimah ce kawai yanzu ake jiran haihuwarta, cikin ikon Allah kuma saida ta shiga wata na goma sannan ta haifi 'yarta ita ma masha Allah, haka akayi shagalin sunanta aka gama lafiya.

Kwana biyu da kammalawa Hamna ta rok'i Hajia ta barta ta tafi Abuja wajen koyon kwalliyarta, ta tafi kuma tana yin abinda ya kaita cikin kwanciyar hankali, sati biyu ta d'auka kafin ta dawo gari, Gambo dake hushi da ita na tafiyarta basu sani ba ne ya sauka yanzu da sa bakin Hajia ya bud'e mata gwangwajejiyar salon da babu abinda babu, sabuwar duniya kuma sabuwar rayuwa gareta, tana zuwa aikinta kuma tana yinshi da himmada kulawa saboda tana so, tana iya zuwa ko ina saboda yi wa wasu kwalliya kamar amarya ko mai jego.

*Shekara d'aya*

A cikin shekara d'aya abubuwa dayawa na ta faruwa, wasu na farin ciki wasu na bak'in ciki wasu na jimami, Hamna kuma yanzu mota take hawa tana murzata duk inda take so, sai dai har yanzu taka tsantsan take wajen nunawa yaronta soyayya, wanda yanzu ya saba da ita sosai yana kiranta da *Tata*, lokuta da dama idan ta ga Ammar da yer uwarta suna rayuwar farin ciki sai taji kowa a gidan yana bata haushi, takan ji kamar an daketa kuma an hanata kuka ne, amma aikinta yana d'an d'aukar hankalinta zuwa wani wurin.

Yau ma kamar kullum ko da Amar ya shigo ya samu Umaimah a yanayin daya fi samunta kullum, tsaki kawai yayi ya shige d'akinshi bai kulata ba, saida gabanshi ya fad'i ganin Farisa k'anwar Jibril ta zage tana gyara shinfid'ar gadonshi, cikin mamaki yace "...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_54_

"Farisa me kike yi a d'aki na?"

Ba tare data d'ago ba ta juyo dan ganinshi, hakan ne yasa rigarta dake da sakakken wuya k'irjinta ya fito har yakan iya hango matashiyar inda nononta suka taso, lumshe idonshi yayi ya d'an kawar da kanshi yana sauraren muryarta da yaji yau ta masa daban tana fad'in "Sannu da zuwa yah Amar, aunty Umaimah ce tace na gyara maka d'akinka."

Bud'a idonshi yayi ya sauke su kanta, wani tartsatsi yaji tare da mummunan fad'uwar gaban da baisan da zuwanshi ba ya ziyarce shi, daga k'asa har sama ya kalleta kamar yau ne ya fara ganinta, yarinyar duka shekara ta sha biyar ce take ciki yanzu, amma da yake tana da girman k'asusuwa saika d'auka ta wuce shekarun, a yau dai kuma a yanzu take sai yanzu kibiyar sonta ta harbeshi babu shiri, da fari yayi niyyar mata kashedin karta sake shigo mishi d'aki ne, amma ganinta a cikin riga da siket na katin da suka karb'eta sun tafi da masifar da damuwar duk daya shigo dasu, saida ya gyara murya ya saitata ya lumshe ido yace "Ok, ci gaba."

Jiki a sanyaye ya juyo ya fito, yanda ya barta ya sameta tana ba wa *Khairat* nono, kusa da ita ya matsa ya tsaya gabanta yana ma yarinyar magana, tana jin muryar babanta tayi tsal ta diro daga kan cinyarta ta mak'ale mishi, d'aukarta yayi duk da bata cikin yanayi mai kyau yarinyar, dan kayan jikinta ma basu da kyan gani sai k'arnin nono take, zaune yayi kujera mai fuskantarta ya d'ora Khairat kan cinya ya kalleta da kyau yace "Umaimah, domin Allah in zaki fad'i gaskiya kina ganin haka ya dace kuwa ki tura yarinya har d'akin bacci na wai ta gyara min? Ke kuma gaki zaune ba kya komai."

Cikin fad'a fad'a tace "Bana komai fa kace? Yanzu baka same ni ina bawa yarka nono ba, ko shi ba aiki bane? Yanzu haka girki na kan wuta ban sauke ba, kuma kafi kowa sanin ina da aikin yi tunda ba zaune nake gida ba, dan lokacin da zan dawo gidan haka kawai saina kashe kaina wajen bautar gyaran gida."

Wani kallo ya mata yace "Kashe kaine ke a ganinki?"

Kawar da kai tayi tana jan tsaki hakan yasa ya girgiza kai yace "To kiji da kyau, indai har ke baki da lokacin gyara min d'aki na karki k'ara baiwa kowace yarinya damar shiga d'aki na dan ta min gyara, inhar kinsan ba zaki iya ba ki ban makullin d'akina dana baki saina dinga gyarawa da kaina, kinji na fad'a miki."

Yana fad'a ya mik'e da Khairat suka fita daga d'akin, mik'ewa tayi ita ma zuwa madafa tana fad'in "Masifaffe kawai, sai kace wani tsohon daya gaji da duniya, ka k'i tamnuwa ka k'i had'uwa kullum da b'acin ranka nake kwana, duk abinda nayi banyi daidai ba."

Yana shigowa da sallama yaran biyu suka tafi a guje suka rumgume shi, kan Huda ya dafa yace "Beby ya kike?"

D'aukar *Abdul maleek* yayi ya kamo hannunta suka zauna, Jamila data zubo ma Huda abinci ce cikin jin haushin yarinyar ta aje mata kwanon k'asa tace "Ke."
Chapter 146 · 0% Book details