Sashe 42
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shekaru sun kuma ja dayawa amma su Hassana har yanzu babu ma-nemin aure, hakan ya fara damun Saratu fiye da zato ta yanda har ta kan zubar da hawaye idan ta gansu masha Allah sunata yawo a tsakar gida, sai dai bata san meye matsalar ba kuma, wannan ne yasa wata rana wata mak'wabciyarsu mai sunan *Delu* suna daka a tsakar gidan saboda Ramma bata nan take fad'a mata ta tashi tsaye akan yaranta, dan ko shakka babu akwai sihiri a jikinsu daya hana su aure, bud'ar bakin Saratu cewa tayi "To yanzu Delu meye abunyi? Wallahi lamarin yaran yana damuna sosai, kawai dan banda abokin shawara ne."
Da sauri Delu tace "Haba ke kuwa Saratu, ai mun zama d'aya, damuwarki damuwata ce, akwai abunyi kam in zaki yarda."
Cike da damuwa tace "Zan yarda mana Delu, idan ban samu mafita ba zan saka yaran a gabane na dinga gatsarsu ina ci? Kawai ki fad'a min kedai."
"Yawwa Sarai, kina ji ko." Ta fad'a tana yin k'asa da muryarta ta ci gaba da cewa "Akwai wani malami dana sani can bayan gidan sarki idan kin gangara tudun nan, wallahi yana bada taimako sosai dan aikinshi kamar yankar wuk'a ne, to ina tabbatar miki da zaki same shi da matsalarki wallahi zata zama tarihi."
Jim ta d'anyi kafin tace "Da gaske Delu? To amma ai matsalar ita ce ni ba komai gareni ba kinsani kema, ko abinci mai kyau ba samunshi muke a gidan nan ba, to taya zan samu kud'in da zan bayar a matsayin sadakar aikin da za'a mana?"
Dafa kafad'ar ta tayi tace "Haba Saratu, ni da ke fa yanzu mun zama d'aya, idan da ba zan taimaka miki ba aida ba zan fara fad'a miki maganar malamin nan ba ma, dan haka ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zan rakaku idan kun tashi tafiya, kuma ni nan zan sayar da d'aya daga cikin awakina dan ganin yaran nan sun samu mijin aure."
Cikin farin ciki Saratu tace "Da gaske Delu? Kai amma naji dad'i da wannan taimakon da kika mana, Allah ya biyaki da gidan aljanna."
"Ameen." Ta fad'a tana d'aga tab'aryarta sama suka ci gaba da daka, suna haka Ramma ta shigo gidan, saida ta k'are musu kallo kafin tace "Yanzu dan na fita daga gidan shine har da min gayyar tsiya a gidan nan, to yayi kyau bari Alhaji ya dawo gidan sai ki fad'a mi shi abinda matar nan take yi, dan na tabbatar gulma kukeyi tunda ai bata zuwa gidan idan ina nan."
Durk'usawa Sarai tayi har k'asa tana fad'in "Dan Allah Hajia kiyi hak'uri na tuba, wallahi ba zamu sake ba daga yau kiyi hak'uri ki min rai."
Delu ce tace "Kinga Saratu tashi, ni zan tafi kar na ja miki matsala ba da niyyar haka na shigo ba, amma dai ya kamata ki rage tsoron nan tunda miji ba shi ya hallice ki ba."
Da kallo kawai Sarai ta bita a zuciyarta kuma tana fad'in "Dan baki san bala'in shi bane Delu akan matar nan tashi, ke dai Allah ya mana tsari da irinsu Hajia kawai."
Dan kuwa tasan inhar ta fad'a mishi to fa ya mata k'aramin hukunci shine ya mata dukan tsiya bayan idon 'ya'yansu, shine ya mata gata kenan, masifa Ramma ta ci gaba da yi ai kawai munafurci ne ya kawo Delu tunda bata cika zuwa gidan ba musamman ma idan tana gidan, Husseina da Husseina suna d'akin Ramma d'aya na gyaran d'akin d'aya na shara, suma tana shiga ta balbalesu akan basu gama gyaran ba tun lokacin data bar gidan, nan fa ta had'e su ta zage son ranta, da magrib Sarai da 'yan biyu suna zaune a d'akin su sai fitar k'wai (aci balbal) dake bayar da haske, Sarari ce ta lek'o a hankali tsakar gidan taga babu kowa, dawowa tayi ta kalli Hassana tace "Husseina, kinga yi sauri kafin Babanku ya shigo ki tambayo min Delu ki ce nace yaushe ne tafiyar nan, idan ta fad'a miki sai ki ce nace ni ba zanje ba amma ku zaku tafi tare da ita."
"To." Kawai Husseina ta fad'a ta tashi ta fita tana waiwayen d'akin Ramma, tana fita Alhaji Hassan kuma ya danno kai cikin gidan, kamar kullum kai tsaye d'akin Ramma ya nufa, tana jin motsinshi ta fashe da kukan makurci, nan fa hankalinshi ya gama watsewa Ramma na kuka, bai samu nutsuwa ba har saida yaga tayi shiru ta fara zayyana masa abinda ya faru kamar haka "Gaskiya Alhaji na gaji, na gaji da irin cin mutumcin da Sarai ke min a gidan nan, wai daga nasa k'afa na fita shikenan saina tarar da Sarai da Delu a gidan nan sunata cin nama na, a k'arshe ma dana musu magana kar ka so kaga rashin mutumcin da suka min ba, da nace kuma idan ka zo zan fad'a maka dan ka shiga tsakani na da ita, amma wai sai Sarai ta bud'a baki tace ai kai miji ne kawai ba ubangiji ba, dan haka baka da wuta ko aljannar da zaka sakata, dan haka ni kawai ka rama min cin mutumcin da ta min gaban k'awar ta."
Wani huci yayi yace "Yanzu dama akan Saratu ne kike kuka haka? Me ya sa zaki tsaya ki bawa kanki wahala? Naga ai kina da damar dake kanki zaki hukunta ta ko bana nan, amma ba komai zata gae kurenta, wallahi zata san ta tab'a ki a gidan nan, yau zanga waya d'aure mata gindi a garin nan."
Fitowa yayi daga d'akin ta biyo bayanshi tana ci gaba da rera kukan iskanci, shi kam d'akin shi ya shiga ya d'auko bulalar fata ya nufi d'akin Saratu da ita, suna zaune ita da Husseina saiko ya fad'o d'akin kamar an turo shi yana fad'in "Ina kike marar mutumci, har ni zaki wa fitsara a gida."
Bai tsaya komai ba ya rufeta da duka da wannan bulalar, kamar yanda ta fad'awa yaran cewa babu ruwansu duk abinda suka ga mahaifinsu na mata, wannan dalilin ne ya tilastawa Hassana mik'ewa ta fito daga d'akin tana zubarda hawaye, karo ta ci da Ramma dake shirin shiga d'akin wanda yasa kafad'ar su ta had'u, kashe Hassana tayi da mari tana fad'in "Dan ubanki ni zaki bige? Ai bani nake dukan uwar taki ba, ubanki ne gashi nan idan zaki rama mata ne."
D'auke hannunta tayi daga kunci ta rab'ata zata wuce Ramma ta sake cewa "Koda yake ma ai ba 'yan halak ta haifa ba shiyasa babu mai jin zafin abinda ake mata duk cikinku."
Daf da k'ofar shigowa gidan ta tsaya tana kuka, cikin sand'a Husseina ta shigo dan kar kowa ya ji shigowarta, amma tana dosowa taji ihun mahaifiyar ta da gudu ta banko kai tana shirin zarcewa d'akin, da k'arfi Hassana ta rik'e ta gam tana fad'in "A'a Husseina, kinsan fa abinda Iyya ta fad'a mana, dan Allah ki barsu."
Fizgewa tayi cikin zafin rai tana fad'in "Dallah malama ni sake ni, haka kawai muna ji muna gani saiya kashe mana uwa bayan ba wata tsiya yake tsinana mana ba."
Sosai ta sake rik'e ta tace "To me zamuyi? Idan kin shiga zaki rama mata ne? Ko kuma zaki masa magana ne yaji? Kawai ki barshi idan ya gaji da dukanta ai zai dakata."
Cikin b'acin rai da tafasar zuciya ta zauna k'asa dab'as ta fashe da kuka ita ma, kuma har lokacin Hassan bai daina dukanta ba har ta kai tayi shiru, suna haka cirko cirko suka ga ya fito daga d'akin yana ta bambami, Husseina kam da harara ta bishi ta mik'e suka shiga d'akin da gudu, zaune suka sameta rakub'e da bango sai shashek'a da take yi, kamar yanda suka saba Hassana ce ta rulgumota tana jijjigata tana fad'in "Kiyi hak'uri Iyya, kiyi hak'uri dan Allah komai zai zama tarihi wata rana."
Suna haka kuma Suley ya shigo da sallama d'akin jiki a matuk'ar sanyaye sai ledar dake hannunshi, Hassana kad'ai ta amsa mishi kafin ya zauna gefensu ya mik'awa Husseina ledar hannunshi, sai lokacin Hassana tace "Suley kana lafiya? Na ganka kamar baka lafiya?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yace "Lafiya ta lau Hassana, na zo zan shigo ciki na ji hayaniya da sautin Iyya, shiyasa ban shigo ba tunda banga abinda zan iya yi ba."
Husseina ce ta kalle shi tace "Wai har kaima dake namiji baka tab'a ji a zuciyarka ba kana so ka d'auki tsohon nan ka nunawa sama shi sannan ka sauke k'eyar shi k'asa? Gaskiya ni na fara gajiya."
Kallonta yayi zaiyi magana Saratu ta mik'e saboda tuna abinda ya fad'a mata da zai fita cewa ta kai mi shi abincin shi yanzun nan, ganin ta fita ta bar musu d'akin yasa sukayi shiru kawai.
Sai bayan kwana biyu Delu ta shirya tare da su Hassana suka tafi wajen malamin nan, shima kuma aradu Saratu ta tara da kai domin ba barinsu ake suna fita ba, haka Delu ta tafi dasu wajen malam Rabi'u, sam a ranta babu mummunan nufi sai na son taimaka musu, amma sai gashi tunda malamin ya d'ora idonshi akan Husseina sai yawunshi ya tsinke, ta wani fannin ya fad'a musu gaskiya kam da yace asiri ne aka musu dan kar suyi aure, ta wani b'angare kuma b'atar da su yayi da yace akwai maganin da zai bayar suyi aiki da shi amma dole Husseina ce zata dawo gobe ta karb'a, ba musu suka juyo suka dawo gidan, yau ma Hassana da Husseina shegen duka suka sha wajen Babansu saboda fitar da sukayi, amma hakan bai hanata komawa ba washe gari da magriba kamar yanda sukayi da malam, wannan zuwan kuma shine ya wargaza duk wani tanadi da tattali data jima tanawa kanta, duk yanda ta so bijere masa bai bata dama ba saboda ya nuna mata k'arfi, kuma tun farko ya riga daya ci galaba a kanta, a wannan zuwan ne malam rabi'u ya rabata da mutumcinta ta hanyar yin kaca-kaca da shi.