← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 198

Sashe 167

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani murmushi ya mata, bayan tsawon lokaci rabon da bakinsu ya had'u yau sai gashi dalilin Shureim yace mata "Fita zamuyi."

Bata kula da abinda ya fad'a mata ba ta zura hannu zata jawo shi, k'ara baya yayi dashi yana kallonta shi ma fuska a had'e yace "Na ce fita zamuyi dashi yanzu, ko kuma ban isa bane?"

Wani kallon rashin mutumci ta masa tace "To miye na tambaya ta bayan gashi ka bawa kanka amsa."

Kai tsaye take nufin bai isa ba kenan, matsowa yayi kusanta sosai har numfashinsu ya fara gauraya ya kalli k'wayar idonta kamar yanda take kallon na shi babu rusunawa yace "Wallahi *kinci albarkacin yaron nan dake tskaninmu*, ba dan haka ba da saina na zubar miki da k'ananan aljanunki, marar kunya kawai da baki iya girmama mutane ba."

Zaro idon da tayi alamar ya akayi haka yasa shi saurin katse mata lissafi da cewa "Eh, na sani, sai kuma yaya yanzu? Shashasha kawai."

Wucewa yayi har ya fara tafiya sai kuma ya tsaya ya juyo, duk da bata juyo ba saida yayi murmushi yace "Zaki iya tuna na tab'a fad'a miki sau d'aya nake aika d'an sak'o na kuma ya isa inda nake da muradin yaje? Ki kama kanki yarinya ko kuma..."

Wucewa yayi rik'e da hannun Shureim ya barta tsaye, saida taji sun tayar da mota tayi saurin wucewa ciki kamar zata tashi sama, bata kula ba tayi karo da Ummy dake niyyar zuwa b'angaren Amna, suna had'a ido ta kama hannunta da k'arfi ta jawota suka k'arasa fitowa daga falon, saida ta juya ta ga babu kowa tace "Ummy, waya sanar dashi maganar nan?"

Dariya Ummy tayi ganin tsoron dake fuskarta duk ta furgice tace "Kwantar da hankalinki to? Ni ai ke zan tambaya wa kika fad'awa har ya fad'a ma Amie maganar nan?"

"Me? Amie kuma?"

Cikin mamaki tace "Ummy ni ban tab'a maganar nan da kowa ba."

"To ya akayi Amie taji har ta fad'awa Amna?"

Gaba d'aya idonta ta k'walalo waje ta dafe k'irjinta dake bugawa da k'arfi, dafata Ummy tayi tace "Kwantar da hankalinki mana."

Girgiza kai tayi tace "Ummy Amna fa kika ce? Taji wannan maganar? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Ummy na shiga uku na lalace, Amna da shegiyar zuciya."

Murmushi ta mata tace "Yanzu dai ki fara nutsuwa tukuna sai kiji abinda ya faru."

Cikin saurin maganar da bata san ta iya shi ba tace "Ummy ina maganar nutsuwa kuma kawai ki fad'a min komai."

A hankali Ummy tace "Shi ya fara samu na da maganar yace Amna ce ta fad'a masa, ita ma kuma wai Amie ce ta fad'a mata, amma fa ita ta d'auki maganar da wasa, muna cikin maganar kuma Hajia ta fahimci akwai matsala ta ja mu d'akinta."

Shirun da tayi ya ba Hamna damar d'ora hannayenta saman kanta tace "Na shiga ni Hamna, na mutu shikenan, Ummy sai me ya faru?"

D'orawa tayi da "Magana mukayi ta fahimtar juna, Hamna idan kika ga yanda Hajia ta fahimce ni har ta bamu shawara wallahi zakiyi mamaki."

Da sauri ta rik'o hannayenta tana fad'in "Ummy kina nufin ba tayi fad'a ba?"

Girgiza kai tayi tace "Ko kad'an in fad'a miki."

Kamar zata fashe da kuka tace "Amma kuma Ummy Amna fa? Ina tsoron ranar da zata ji da abinda zata iya yi wallahi."

Cikin taushin murya tace "Insha Allah ita ma zata fahimce mu fiye ma da Hajia, abinda kike tunanin tayi ba zai tab'a faruwa ba, Amna tana da hak'uri sosai."

"Amma kuma tana da zuciya Ummy." Ta fad'a tana sako siraran hawaye, hannu tasa ta shafe mata tace "Dan Allah karki d'aga hankalinki Hamna, ki nutsu ki shiga ki samu kiyi wanka ki ci abinci, karki yarda wani ya gane kina cikin damuwa, muyi addu'a yanzu Allah ya bata lafiya, ke baki ji abinda ta fad'a ba kwana uku da suka wuce, kallon mahaukaciya ma take wa Amie fa."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan Ummy." Shigewa tayi ciki Ummy ma ta nufi b'angaren Amna.

Ko da taje ta samu an ba wa Amna maganin zazzab'i tasha, d'aki suka ce taje ta kwanta ta huta da kwaramniyar nan, da shigarta d'aki baifi minti sha biyar ba Hamna ta shiga dubata, kwance ta same sai rawar d'ari take, ko da ta tab'a jikinta taji zafi sosai kamar garwashin wuta, idonta sunyi jawur da su kamar ba nata ba, Ummy ta fito ta fad'a ma suka shiga tare, ko da ta ga jikinta tace kawai su kaita asibiti, ba b'ata lokaci Hamna ta jasu dan Ammar ya riga da yayi nesa da gida, acan ya samesu har san jona mata k'arin ruwa. Tsananin zafin jikin baya raguwa sai sama yake, cikin d'an lokaci k'ank'ani ta canza ta fice a hayyacinta, da fari an k'ara mata ruwa sai aka nemi jini ma aka k'ara mata.

Allah da ikonsa kafin gari ya waye ba zaka tab'a kallon Amna kace ita ce ba, ta gigice ta canza duk ta disashe ta zama abar tausayi, gashi tayi kamar ta kumbura a jikinta, zuwa wayewar gari saida aka saka mata wani tiyo dake kai mata ruwa, a hannayenta k'arin ruwa da jini, n'aurar taimaka mata wajen numfashi abubuwan kamar ba a jikin mutum ba.

*Sai daren ranar* kad'ai likitoci suka d'an samu kan matsalar, Ammar ne zaune gaban likitan ya k'ura masa ido inda zuciyarsa ke dukan uku uku, ya kasa had'a yawu ko alama sai tattarasu yake yana son turasu mak'ogoronshi amma sun k'i wucewa, likitan ne ya mayar da hankalinshi kanshi cikin nutsuwa yace "Docteur ya kukayi sakaci haka da marar lafiya? abu ne dake matuk'ar wuya samun irin haka a lokaci d'aya, kuma da an ankara da wuri da an cire mata d'aya a barta da d'ayar, yanzu gashi lokaci ya k'ure mana sosai."

Ammar dake kallon bakinshi kamar kurman dake fahimtar yaren leb'e ne yace "Ban cika fahimtar ka ba fa, ka min gwari gwari zan fahimta."

Saida ya dan furzar da iska ya kalli tsakiyar idonshi yace "Duka sun lalace, k'wadarta."

Da sauri ya dafe kanshi da hannu biyu, sosai yake matse kanshi yana so yaji ya daina sara masa amma abun ya ci tura, da k'yar ya d'aga kai ya kalle shi yace "Ta yaya? Duka biyun zasu lalace lokaci d'aya? Ta yaya dan Allah? Me ye abunyi yanzu?"

Cikin rashin karsashi yace "Mu kan mu abun ya bamu mamaki, dan abune da bai cika faruwa ba gaskiya..."

Katseshi yayi da cewa "Me ye abunyi yanzu?"

Cikin girgiza kai yace "A gaskiya yanayin jikinta ma ba zai bayar da damar da za'a fara mata dialyse ba, dan kaga tana jin jiki sosai kuma kowane dialyse zatayi perdre d'in 10 kg, dan haka ina ga mu..."

Da k'arfi ya mik'e tsaye yana fad'in "Dan haka ayi me? A barta ta mutu kenan? Haka kake so ka ce?"

Girgiza kai yayi yace "Non docteur, amm..."

Cikin daka masa tsawa yace "Kaga fad'a min mafita kawai, ina so ka fad'a min abinda zanyi matata ta samu lafiya, bana son ganinta a halin da take cikin nan."

Shi dai yana so su rabu lafiya dashi sai kawai ya rubuta masa magaunguna yace ya siyo, da gudu ya fita kamar wanda yasha giya dan har yanzu kanshi mugun sara masa yake.

*Kwanansu* biyu a asibiti, abubuwa sun k'ara dagulewa, tun safiyar yau da Ammar ya shigo d'akin ta fara masa nasiha ya rage zuciya ya dinga hak'uri ya kula da yara waye waye, sai kawai zuciyarsa ta karye ya fita daga d'akin, Allah ya sani har zuciyarshi yana son Amna kuma yana son zama da ita, amma baisan wacce k'addara ce ke shirin raba shi da ita ba, baisan ilimin dake cikin rashin lafiyarta ba, tunda ya fita ya zauna cikin masallacin asibitin bai sake tashi daga nan ba, yanda ya ga safiya a cikin shi haka ya riski rana da dare.

Al'amarin bai sake tashin hankalin kowa ba saida ta nemi a kawo mata yaranta, daga kwance haka take shafar kawunansu tana musu murmushi, Ameera da tafi kowanensu shak'uwa da ita ce ta kwanta kan jikinta tana kuka, Ameer ne ya jayeta daga jikinta yana fad'in "Ke baki gani bata da lafiya."

Fizge hannunta tayi ta sake kwantawa kan jikinta, Ummy dake tsaye kusansu ne ta kalli Hamna dake tsaye ita ta kawosu tana hawaye, hannun Ameera ta kama cikin muryar kuka tace "Beby na zo mu je ko? Zaki sha ice cream?"

Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um."

Saida ta share hawayenta ta sake kamota tace "Muje kinji har da madara zan siya miki."

Duk da bata saki jikinta ba haka ta bi Hamna zasu fita, cikin muryar da bata fito sosai ba Amna tacej "Yer uwa."

Juyowa tayi tana kallonta ta tako a hankali ta zo ta tsaya, hannu ta mik'a mata ita ma ta zuro mata na ta hannun ta rik'e gam, murmushi ta saki mai kyawun gaske tace "Karki manta dani kinji, ki ci gaba da min addu'a, ke da yah Ammar zaku kula min da yarana, nasan da haka ban da matsala, karki rabu dasu duk wuya, yah Ammar zai shiga damuwar rashi na, ki...kkk...kw..."

Ganin ta kasa fad'ar kalmar kuma ita kuka ya ci k'arfinta yasa ta fizge hannunta da k'arfi ta tashi a guje ta fita, bata tsaya ba saida ta kai k'ofar asibitin ta durk'ushe nan tana kuka da iya k'arfinta.

Ko da ta fita Amna ta kalli inda Hajia take ta mata alamar ta zo, matsowa Hajia tayi tana kuka ta rik'e hannunta tace "Amna dan Allah kiyi ta addu'a, insha Allahu zaki tashi kinji."
Chapter 167 · 0% Book details