← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 198

Sashe 183

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk taurin kanta sai kiyi duba da d'an mutum fa ya tsaga ya fito ta gabanta, amma a hakan ya mata wannan cin wulak'anci, me kike tsammani idan da budurwa ce? Da kenan gawarta ce muka wanke yanzu?"
Dariya dai Zeituna tayi dan gaskiya ta fita gaskiya yau kam.

Safiyar ta yau Jibril dake d'an alak'a dasu ne ya samu labarin rasuwar malam Rabi'u, Labaran ya fara fad'a ma maganar, cewa yayi zai je amma idan Hajiarshi ta amince, yasan kuma ba lallai ta amince ba shiyasa yaje da kanshi, ya jima yana bata hak'uri da bata baki kafin ta yarda su tafi, Labaran da Jibril da Jamil tare da Soueiba da Hajia suka tafi, Husseina ta so Hajia tayi zamanta amma tace to in mutuwa bata zamar mana wa'azi ba me kenan zai ladabtar damu? Haka suka je wajen gaisuwa daga nan kuma har suka je gidansu Mari ganin mamarta.

Jikinta yayi kyau yanzu fiye da da kam dan maganarta ma lafiya lau sai abunda ba'a rasa ba, sai Mari da suka samu tana kan sharholiyarta, ta k'ara mulmujewa tayi jiki sosai, da gani kuma kasan k'ugunta yanzun na magani ne, ta shiga shafe shafe tayi jawur kamar zabiya sai dabbara dabbara na musamman a hannayenta, ta k'ara huje a kunnenta barkatai abun har ya k'azamce.

Sanda suka je bata nan suna zaune ana ta gaisawa da hirar ya bayan rabuwa sai gata ta shigo tana waya, atamfa ce jikinta amma har gwara wasu kayan na kanti akan na jikinta, siket d'in yanda ya kamata kai kace bata iya tafiya, ya fito mata da bankamemen k'ugun nan kam har saiya baka tsoro, rigar kuwa duk rabin nonuwanta a waje suke sun matsu sunyi pam dasu, baya ma haka duk rabinshi waje yake dan haka ko bras ma bata saka ba, atach ne akanta babu kitso ta d'aure da ribom, kwalliya ce ta tashin hankali a fuskarta da gani kasan ko dai biki zata je ko kuma ta dawo ne, duk da ta ganesu sarai amma cike da wulak'anci ta wuce d'aki tana fad'in "Sannunku."

Girgiza kai Jibril yayi ya d'an kalli Mamanta, daga kallon da yaga tabi ta dashi zai fassara maka abinda take ji game da hallayarta, sai yaji tausayinta ya kama shi sosai, da zata amince shi kam daya d'auketa sun tare a sabon gidanshi da zai koma, ko ba komai dai akwai alak'a tsakaninshi da ita. Ko da suka gama gaisuwa suka tashi dan komawa, sallama sukayi sosai suka fita, a soron gidan suka ji ance "Jibril."

Kusan a tare suka juya dukansu, Mari suka gani da d'aurin k'irji na towel kalar pink, dukansu fita sukayi suka barsu, d'auke kanshi yayi daga gare ta, cikin wata shegiyar murya tace "Huda nace ko zaka kawo min ita idan an musu hutu ta zauna tare dani?"

Ba tare daya kalleta ba yace "Ba zai yiwu ba gaskiya, amma dai in aka sake sun zan turota tare da dreba ya kawota, zai kwana anan shima kwana biyu sai su koma tare."

Da mamaki ta kalleshi tace "Ban gane ba? Kana nufin ko wata ba zaka bari ta min ba?"

Bai kalleta ba yace "Ba zai yiwu ba nace, sai anjima."

Ya juya zai fita tace "In ka isa Allah ya tsine min, to me kake nufi dani? In haifi yarinyar a ciki na kace zaka min iko akan ta, Allah baka isa Jibril ko da k'arfi zan k'waci 'yata."

Juyowa yayi ya kalleta sama da k'asa yace "Ni ba sakarai bane Mari, da kin nutsu kin gyara halinki da Huda ta zauna tare da ke, amma a halin yanzu na kawo miki yarinyata mace mai shekara goma sha biyu a duniya, c'est très difficile Mari."

Juyawa yayi ya fita me Mari zatayi sai kuwa ta fara nuna halin rashin kunya da fitsara, har k'ofar gidan ta fita da d'aurin k'irji ta shiga aika mishi munanan ashar, shege tsinanne bak'ar haihuwa ai duk shi ya lalata idan ya manta ta tuna masa, shine yanzu zai mata iko da d'iyarta to bai isa ba, su dai babu wanda ya kulata tuni sukayi nisa ma sai ita suka bari tana haukanta, sai dai yayi niyya ba zai ma kawo Huda ko da tayi kwana biyun bane, zai kira mahaifiyarta ya bata hak'uri tunda ita ma tana son ganin Huda, amma yasan inya kawota tana iya rik'eta hakan kuma zai haifar da tashin hankali, dan akan tarbiyar yarsa zai uya makata kotu ma ta rabata da ita har abada, dan yana mugun son yarinyar yana kuma bata kulawa, duk wani motsi nata a lure yake dashi da taimakon Jamila da yanzu take d'aukar yar kamar nata yaran, sai dai kawai k'addara da kuma yaran zamani da wani lokacin sai su fi iyayen da suka haifesu dubara ma, amma har yanzu yana addu'a Allah ya yafe masa abinda ya aikata a baya ya kuma shirya masa yaransa da sauran zuri'a.

Har azahar bai dawo gidan nan ba saida Ummy ta kirasa ta masa wankin babban bargo, dariya kawai yake mata yana cewa tayi hak'uri to taja wa yarta kunne ta dinga girmama shi, a k'arshe dai tace an k'i aja d'in ya jima bai kasheta ba, sai kusan k'arfe biyu da rabi ya shigo gidan da matuk'ar bacci a idonshi, kai tsaye d'akinta ya shiga ya sameta kan sallaya kwance dan zaman salla ma da k'yar take d'an azawa saboda d'inki hud'u Ummy ta mata, zaune yayi k'asa kusanta ya dafata yana fad'in "Ayyah beby sannu, ashe baki da lafiya? Kai amma wallahi banji dad'i."

Ko kallonshi ba tayi ba bare ta amsa mishi, tallabota yayi ya tayar da ita zauna, da sauri ta rintse ido tace "Washh."

Cikin dubara ta d'an zauna rabi da rabi yanda bata jin zafin sosai, shafa kumatunta yayi yace "Sannu kinji, me ya same ki ne haka? Waya tab'a min ke?"

Idonta cike da k'walla ta kalleshi, da Allah zai ara mata lokaci da cakumar wuyanshi zaatayi sai taji ya daina motsi, sai dai bata da wannan k'arfin a yanzu kam watak'ila ko a gaba, janye hannunshi tayi daga kan kumatunta ta tashi da k'yar ta nufi gado, wannan enveloppe da makullin ta d'auko ta cilla masa a jiki tace "Ka rik'e bana so."

Mik'ewa yayi tsaye yana d'aukar kayan yace "Ban gane na rik'e ba? Naki ne fa."

A k'ufule ta kalleshi tace "Shine nace bana so, ai kasan nafi k'arfinsu ko tunda ni ba ci ma zaune bace, sannan ubana ya d'auke min nauyin komai."

Tab'e baki yayi ya aje mata kan gadon yace "Ni ma kuma idan nayi abu na bashi baya kenan har abada, ko ki rik'e ko ki jefa a kwandon shara ruwanki ne, ni ladar wahalarki ce na biyaki."

Da wani mahaukacin mamaki ta bud'e baki tana kallonshi, ladar wahalarta? Me ya d'auketa to? Tana cikin tunanin taga ya fice a d'akin yana hamma, a hankali ta fita daga d'akin ta bishi d'akinshi daya shiga, ko da ya juyo ya kalleta yayi murmushi yace "Har kin fara nema na da kanki madame?"

Sama da k'asa ta harareshi tana kallo ta ga me zaiyi, tsaf ya haye gado har da jan zani ya rufe, murmushi ta saki mai ciwo kafin ya kalleta yace "Idan aka kira sallah la'asar ki tashe ni."

Da kallo kawai ta bishi tana tsaye bata gusa ba, tun yana kallonta yana murmushi har ta ga idonshi rufe dai alamar yayi bacci, cikin takonta na hankali kwance ta shiga ban d'akin ta d'ebo a murfin butar dake ciki ta fito, saida ta tsaya kanshi ta juye masa ruwan a fuska.

*Aiki ya kwaso ki Hamna.*

Da k'arfi ya firgita ya tashi yana zazzare ido yana kallonta, cikin goge ruwan fuskar tashi yace "Ke lafiyarki k'alau? Me ke damunki?"

Saida ta rik'e k'ugu tace "Abinda ke damunka."

"To miye haka?" Ya fad'a da k'arfi, tab'e baki tayi tace "Babu ta yanda za ayi kayi bacci wallahi bayan ni baka barni bacci ba, haka kawai."

A nutse ya kalleta yace "Hamna zaman lafiya kike so ko tashin hankali? Duk wanda kika zab'a shi zan zage damtse na nuna miki, tunda ni har siyarwa nake kuma ina koyar dasu."

Wata yar dariya tayi tace "...

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:39 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_72_

"Duk wanda kake ji nima shi nake ji."

Murmushi yayi yana sauka daga kan gadon yace "Hum!"

Fita yayi daga d'akin ya koma falo, nan ma ko da ya kwanta kan kujera tayi tsaye ai babu shi babu bacci, tashi yayi ya koma d'akin yasa key da sauri, babbugawa ta shiga yi tana kiran ya bud'e, dariya ya mata yace "Indai kina da zuciya ki rabu dani, na gane me kike buk'ata yarinya, tanadi nake miki har a jima da dare saina b'arar miki da ita."

Hak'ura tayi ta kwanta a falon ita ma, ko da aka kawo mata abinci ta ci ta sake shan magani dan jaraba ce kawai amma tana jin jikin sosai. Bata jimawa da kwantawa ba kawai amai ya sake taho mata, da gudu ta shiga ban d'akin dake falon d'an nesa da madafa, jin kakarin abun yake daga sama ba sosai ba, tasowa yayi yana fitowa ya tabbatar da abinda yake zargi, tsaye yayi yana mata dariya har ta ida ta juyo zata fito, wurga masa harara tayi zata fita yace "Madame ki fad'i gaskiya mana, duk yanda akayi an sake samun k'aruwa ne."

Wani kallo ta masa tace "K'aruwa fa, da kai? Shikenan dan na zama kaza daga tab'a ni sai d'aukar ciki? Allah ya sawak'e."

Hannunta ya kama tana ta k'ok'arin k'wacewa amma ya rik'e gam, saida ya kaita har d'akinshi ya kwantar da ita kan gado, k'afarta taga ya d'aga yana shirin saka mata hannu, da sauri ta yunk'ura ta tashi tana fad'in "Malam lafiya?"
Chapter 183 · 0% Book details