← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 198

Sashe 165

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Ummy yayi daga nesa, ita ma shi take kallo kallon nima bansan komai ba, wucewa yayi d'akin ta bishi a baya, sua shiga ta zauna kan gadonshi tana kallonshi tace "Kana ji ko? dan Allah ka kula min da yarana, ka dinga kaisu makaranta kan lokaci, kaji ko?"

Shi mamakin yanda take masa magana kamar wacce ta haife shi ne ma yake, ganin bai ce komai ba yasa ta amso ledar hannunshi tana fad'in "Kawo to, watak'ila kallon nan da kake min dan ban karb'a bane."

Aje ledar tayi kan gado ta mik'e zata fita sai kuma ta juyo ta kalleshi tace "Kasan wannan k'awar ta mu Amie?"

Kai kawai ya jinjina mata yana ci gaba da kafeta da ido, dariya tayi sosai tace "Baka san ta hauka ce ba? Kasan haukan data zo min dashi gidan nan?"

Kai ya girgiza mata kawai dan jin maganarta yake kawai a sama, wata dariyar ta sake yi tace "Wai a haukanta cewa tayi kai da Ummy da yer uwata kuna cin amanata, kasan me ta fad'a min?"

Ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya daina kallonta, jinjina kai tayi ta matso kusanshi cikin rad'a tace "Wai cewa tayi Shureim d'an ka ne, kaji fa mahaukaciyar, ta manta Ummy ce ta haife shi, to kuma ni ko wa ma ya haife shi ina son shi, inda yer uwar ta wa ta haife shi wallahi da naji dad'i."

Kallon fuskarshi tayi da kyau sai tayi dariya tace "Kai ma ka girgiza ko? Karka damu ci gaba da abinda kake."

Ko da ta fad'a ta juya a hankali ta bar d'akin, shi fa tunda ta fad'i haka gabanshi ya yanke ya fad'i, kawai bata aje hankalinta bane data fahimci tashin hankalin daya shiga jin wannan magana, ita dai ta d'auki abun wasa da k'arya da kuma hauka, amma shi baya da dalilin da zai k'aryata Amie, hasalima zai iya cewa ya yarda da abinda ta fad'a d'in, yana da gamsassun dalilai da hujojji.

Yanda ya zazzare ido haka ya zauna bakin gado, tunani ya durmiya yana tuna faruwar komai sala sala, tabbas bayan faruwar al'amarin ne cikin Ummy ya bayyana, lokacin daya ga canji a jikin Hamna har ya so fallasawa Ummy ta jijjiga sosai har ta mare shi, sannan ta matsa sosai har saida aka mata hanyar data shiga sahun masu tafiya France kuma ta k'ara kan lokacin daya kamata ta dawo, kuma ai Hamna bata nan a lokacin, to kenan taya haka ya faru? Girgiza kai ya shiga yi yana ta tunanin abubuwa da dama, ji da yayi kamar kanshi zaiyi bindiga yasa shi mik'ewa da sauri ya fito.

Har tsakiyar mutanen da take zauna ya ja hannunta inda hankalin kowa ya koma kansu, janta kawai yake ita kuma tambayarshi take ina zai kaita lafiya? Saida ya kaita kusan d'akin mai gadi ya tsaya ya saki hannunta, rik'e k'ugu yayi da duka hannayenshi yana kallon fuskarta kamar ba gobe, ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfin gaske.

Cikin wata sanyayyar murya amma sautin ta zai nuna maka babu wasa a cikinta kuma mamallakin muryar zai iya yin komai a yanzun yace "...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_63_

"Ummy, da gaske wai Shureim d'ana ne?"

A firgice ta kalleshi yayin da taji har ruwan jikinta na neman tsayawa, yanda ta zaro ido zai nuna maka bata da gaskiya, gudun kar ya fahimta sai tayi saurin b'atar da firgicin ta jawo mamaki ta dasa a fuskarta tace "Ammar, wace irin magana ce wannan? Wane Shureim d'in?"

Da hannu ya mata alamar ya isa haka tare da cewa "Ummy, kin sani na sani abinda ya faru, idan zan iya kawo miki hujojji na sai mu kwana anan ban gama ba, tun waccen lokacin ma nayi shiru ne saboda gudun b'acin ranki, Dan Allah Ummy inhar gaskiya ne abinda naji ki fad'a min."

Cikin fad'a tace "Ammar wace maganar banza ce wannan? Ya zaka tasa ni a gaba kana tambayata wai Shureim d'anka ne? Zargina kake da cin amanar mahaifinka ko me? Ni sam ban ma fahimci me kake nufi ba."

Matsawa yayi daf da ita murya k'asa k'asa yace "Ummy ba haka nake nufi ba, Shureim an ce d'ana ne dana haifa tare da Hamna, shine nake so naji gaskiyar."

Cikin b'acin rai da d'aga murya ta rintse ido tace "Ammar bana son maganar banza, uwarka ce ya zaka sani gaba kana min wannan tambayar rashin mutumcin? Fad'a min wane d'an iskan ne yake son shiga tsakani na da kai da har ya fad'a maka wannan banzan shirmen?"

Cikin fitar hayyaci da b'acin rai da yanayin da shi kanshi baisan yayi magana dashi ba ya d'aga murya sama da ta ta yana fad'in "Ummy babu wani dake son shiga tsakani na dake, magana ce ta fito kuma ina so na sani nima, a matsayi na na d'anki ina da hakk'in da zan san haka."

Saida ya dasa aya ya iya jiyo sautin muryarsa can sama, dafe kanshi yayi da hannu biyu yana d'an murzashi a hankali, kallonta yayi ya rik'o hannayenta duka buyu yasa idonshi cikin nata yayin da take mishi kallon mamaki yace "Ummy ki daure ki fad'a min mana, da gaske d'ana ne ko kuma k'arya aka fad'a?"

Cikin zubo da hawayen da suke nuna ta k'are min ta kafe shi da ido tace "Ammar waya fad'a maka maganar nan? Wane d'an banzan ne?"

Kamar zai fashe d a kula yace "Ummy abinda nake so naji daban, abinda ke ma kike so kiji daban, amsar tana da sauk'i fa Ummy idan kikayi niyyar fad'a min, kawai zaki ce min eh ne ko kuma a'a."

K'yabta ido tayi tana kallon gefenshi, jinjina kai yayi yace "Zan tabbatarwa kaina."

Ko da ya fad'a ya wuce da k'arfi ya tunkari falon Hajia, da gudu gudu ta bi bayanshi tana fad'in "Ammar ina zaka je? Me kake shirin yi ne wai? Ammar..."

Bai tsaya ba har saida ya shige falon, shigarsu yayi daidai da fitowar Hajia daga d'akin tare da duk yan kuci-kucin yaran suna ta mata shirme, da sauri ya tunkareta inda ya ga Shureim, hannunshi ya kama ya juya zai fita dashi Ummy ta rik'e hannun Shureim ita ma, juyowa yayi yace "Ummy dan Allah sake shi."

Matsowa tayi kusanshi tace "Ammar baka da hankali ne wai? So kake ka min terere cikin mutane? Ina zaka kai shi?"

Gyara tsayuwa yayi yace "Asibiti zamu je."

Ko da taji yace asibiti tasan me zaiyi acan, sunkuyar da kai tayi k'asa sai Hajia data matso kusansu tana kallon kowane tace "Ku kuma lafiya? Meya faru ne haka?"

Kallon Hajia yayi yace "Hajia, Shureimmm..."

Yanda Ummy tayi saurin rufe masa baki yasa shi jan k'arshen sunan, kallonta Hajia tayi ta fahimci bata so taji, sai kawai ta kama hannun Ummyn da Ammar ta tura su d'akinta, Shureim ta kama hannunshi shima suka shiga ta mayar da k'ofar ta rufe, zaune tayi kan gado ta kallesu ta nuna musu kujerar dake d'akin mai kama data gwal tace "Ku zauna dan Allah."

Ummy na kallon Ammar ta tsoma mazaunanta kamar tace wayyo ita wayyo kanta, a nutse ta kallesu ta tattara hankalinta gaba d'aya kansu tace "Me yake faruwa Sa'ada?"

Cikin in'ina tace "Hha.jia, ba kommai..hajia."

Murmushi tayi ta kalli Ammar tace "Ammar lafiya? Me yake faruwa da kake d'aga murya fiye data mahaifiyarka?"

Ummy ya kalla ya sunkuyar da kai yace "Kiyi hak'uri Ummy ki yafe min, wallahi bansan na d'aga murya fiye da taki ba, kiyi hak'uri dan Allah."

Dan motsa kanta tayi wanda yake nuna tace ba komai, Hajia ya kalla yace "Hajia, in baki manta ba na fad'a miki abinda ya faru tsakani na da Hamna shekaru kusan biyar kenan."

Sororo Ummy ta kalle shi da wani fitinannan mamaki, ya fad'a mata? Yaushe akayi haka bata sani ba? Kuma shine Hajia bata nuna mata ta sani ba? Tana kallon bakinshi taji yace "Shine yanzu aka fad'a min Shureim d'ana ne, Hamna ce ta haife shi, kuma ina tambayar Ummy amma ta k'i fad'a min, Hajia ina so na sani d'ana ne ko kuwa."

Hajia ma mamaki ne ya bayyana a fuskarta, kallon Ummy take tace "Sa'ada."

D'ago kai tayi ta kalleta, d'orawa tayi da "Da gaske ne abind yake fad'a?"

Cikin sanyin jiki tayi shiru ta kasa cewa komai, ba zata yarda ta sake yin k'arya ba, tunda gashi wacce tati shekaru ma yau ta fito, sai dai kuma ba zata iya amsa kai tsaye da eh ba, ganin wannan shirun na ta yasa Ammar kallonta da mamaki yace "Ummy me yasa kika yi haka?"

Kallonshi tayi saita sake yin k'asa da kanta ta fara zubar da hawaye, girgiza kai yayi kamar zai yi kukan shima na tausayin mahaifiyarshi yace "Ummy me yasa kika aikata haka? Dama har soyayyar da kike min ta kai wannan matakin?"

Fashewa ta sake yi da kuka sai kawai yace "Ummy in kinyi hakane saboda ki kare mutumci na dana Hamna, ai da fad'a min kikayi saina tayaki kare wa har zuwa lokacin da kike so kowa ya ji, idan kuma kinyi ne saboda gudun abun kunya da kallon da mutane zasu mana, Ummy ai naga ba akai na aka fara abun kunya ba, a gidan nan bani ne farkon daya fara aikata irin wannan laifin ba, Ummy ina kika kai tonton Labaran? naga shima ba da aure aka same shi ba kuma yana rayuwarshi hankali kwance, hasalima ba tare daya tab'a ganin mahaifinshi ya taka wani babban matsayi na rayuwa."
Chapter 165 · 0% Book details