← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 198

Sashe 54

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana jin ta saka makulli ya taso daga kan gadon ya lab'e jikin k'ofar, tana bud'ewa ta mayar ta rufe da niyyar shiga wanka, ta juyo kenan da nufin kunna hasken d'akin taji an cakumeta ta baya tare da rufe mata baki da hanci da tafin hannu lallausa wanda hakan yasa k'arar da tayi bata fito ba, tabbas tasan Abbas ne amma me yake nufi da haka bata sani ba? Take a wurin gyalenta da d'an kwali ya fita ta saki jakar data shigo da ita, ta bayanta ya d'ora hab'arshi a kafad'arta yace "Wato a gabana kike zagar min yara ko? Saboda kina tunanin bana gidan, ashe dama haka kike tsine min bayan ido na? To bari kiga yanda zanyi dake."

Cillata yayi akan gadon ya kuma bita ya taushe yana fad'in "Jiya nace ki zo, amma ki ka k'i zuwa dan kin raina ni, sannan kika cije ni nace zan rama kika ce na rama d'in, to bari kiga ikon Allah Sameera, ba dai dan kinga ina jin tausayinki ina d'aga miki k'afa ne yasa kika raina ni ba."

K'wafa yayi yasa k'arfi ya cire zip d'in rigarta da k'arfi, bata fara jin tsoro ba har saida taji ya rabata da komai na jikinta, da k'arfi ta k'walla kiran "Ammieeeee!"

D'aga hannu yayi kamar zai mareta yace "Wallahi kika k'ara d'aga min murya saina zabgeki da mari, fitsararriya kawai."

Yana fad'a ya fizgi k'afar ta da k'arfi babu alamar tausayi ya wareta, sake fashewa tayi da kukan shagwab'a tare da rufe kumatunta karya mareta, ai da iya k'arfin da Allah ya hore masa ya zage ya saisaita kansa zuwa hanya madaidaiciya ya durmiya cikin jikinta, rad'ad'in azabar da bata tab'a ji bane ya ziyarce ta lokaci d'aya, rikid'ewa idonta sukayi ta bud'a gaba d'aya bakinta zata saki k'ara yasa hannu ya rufe mata bakin...

*Takwara maganinki kenan ai😡*
12/06/2020 à 11:17 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕

_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_7_

Da sauri Abbas ya rik'o ta dan yasan me zatayi, juyowa tayi ta kalleshi ganin ya had'e rai sosai yasa ta fincike daga rik'on daya mata ta fice a falon da sauri tana hawaye, girgiza kai yayi yana sake jadadda kai kukanshi ga ubangiji akan Allah ya sanyaya mata zuciyarta, cikin sanyin jiki ya zauna inda Abba ya kalli uwar d'aki data fara magana kamar haka "Amma yallab'ai sai naga kamar gaskiya matar waziri ta fad'a, dan ko ni dake uwar gidan takawa kuma uwa ga sarkin yanzu bansan da wannan magana ba, amma abun mamaki wai har kuna cewa ma burinshi kenan."

Kallonta Abba yayi, shin nesan da sukayi da juna na tsawon lokaci ne yasa *Hafsatu* mantawa da waye shi? Ko kuma sanyin da yayi ya rage tijara ne yasa har zata iya kallonshi ta fad'a masa wannan maganar? Wane irin raini ne wannan suka d'ora mishi haka harda matar da bai ma gama saninta ba ko a fuska? Me zaiyi musu ne ma wai? Ya jima yana mata wannan kallon mai tattare da nazarin abinda zan fad'a miki kafin ya nisa yana kallonta ido cikin ido yace "Hafsatu kinsan dai da nine a gaba da mijinki ko? Sannan kinsan da mijinki ma kallo na yake kamar mahaifi tun bayan rasuwar iyayenmu? Sannan nasan kinsan cewa kaf yaranshi ina da hakk'in da zan iya yanke hukunci a kansu ba tare da sanin shi kanshi margayi ba? Dan haka ki saurara min tare da d'aga min k'afa, kar kisa nayi abinda za'a buga sunana a mujalla shafi na farko da zata fito safiyar gobe."

K'wafa yayi tare da juyawa ya kalli liman yace "Liman, kana da wata matsala idan aka d'aura auren nan a yau?"

Girgiza kai yayi yace "Babu ko d'aya ranka shi dad'e."

Imran ya kalla yace "Kai fa Imran? Kana da matsala da hakan?"

Shi ma girgiza kai yayi cikin ladabi yace " Babu Abba."

Mik'ewa yayi tsaye tare da fad'in "Duk mai farin ciki da auren nan ya fara shiri yanzun nan, dan ana idar da sallah la'asar zan d'aura auren Imran da 'yar wajen liman Safiyya."

A wannan karan kam uwar d'aki ba wai tsananin son da take sai Imran ya auri 'yar waziri bane yasa ta shiga rud"u da firgici illa yanda take ganin za'a nuna mata iko da d'an data haifa, kuma wai ba ma uban daya haife shi ba, wannan ne yasa ta mik'ewa ita ma kamar zararra tace "Me? Aure? Zaka wa d'an nawa ba tare da amincewata ba? Wallahi baka isa ba, *Mus'ab*, karfa kaga muna d'aga maka k'afa, can ma kawaici ne a matsayinka na yayan mijinmu, amma ka sani shi kanshi yanzu baya raye, dan haka wallahi ba zan tab'a yarda ka had'a auren Imran da wannan yarinyar ba yar matsiyata, indai ni na haifi Imran kuma ta hanyar aure."

K'arama a cikin matan takawa ce ta kalleta a nutse tace "Haba uwar d'aki, sai naga kuma ko takawa baya raye ai akwai alak'ar data had'a ki zumunci da danginshi ko da kuwa ba kya so, wannan alak'ar kuma ita ce 'ya'ya, ki nutsu dan Allah sai a bi komai..."

Da hannu ta dakatar da ita da cewa "Dakata min malama, 'yan bak'in ciki kawai, ai dama nasan ba son yaya na kuke ba shiyasa hakan ba zai dameku ba, to ke ki bada d'an ki mana sai a had'a shi da wannan bak'in irin, amma ba ni ba."

Imran da tunda ta fara magana yake kallon yanayin Baffan nashi, sai jimk'e hannunshi na hagu yake yana ji kamar zai kai duka, inda yake d'an lumshe idon shi yana bud'ewa duk da haka saida sukayi ja, yasan zaman nan ba zai k'are musu da kyau ba, dan haka ya kalli uwar d'aki a sanyaye yace "Umma, dan Allah ki zauna muyi magana."

Cikin b'acin rai tace "Wane zama kuma zanyi, Imran a gabanka za'a tozarta mahaifata a nuna min ban isa da kai ba, aure? Ka manta aurenka na farko ma haka aka d'aura maka shi ba tare da ina so ba, shine yanzu ma zaka sake wani auren saboda mahaifinka, me kake so da ni? Kana so dole saika nuna min ka fi son mahaifinka a kaina? Imran uwa fa ba wasa bace, karka manta da haka, amma idan kace zakayi to ba zan hanaka ba, kaje kayi ga wurin nan."

Cikin tsananin rashin jin dad'i ya d'an girgiza kai, har zuciyarshi yana son auren yarinyar baisan me yasa ba, ga kuma abinda mahaifiyarshi take fad'a, d'agowa yayi ya kalleta a nutse cikin taushin murya yace "Umma, wallahi ba wai na fifita Abba a kanki bane, ba kuma zan bi umarninsa bane dan na b'ata miki rai, wallahi ni da kaina na shawarci takawa akan maganar auren da nake so na k'ara, kuma shi ya bani shawara ga 'yar liman nan, nasan ba zai min zab'in da zai cutar da ni ba shiyasa ma na amince da gaggawa, amma ina neman afuwarki idan ranki bai miki dad'i ba, kuma duk da haka ina rok'on alfarmarki da ki barni nayi auren nan Umma, shine cikar burin takawa, Umma idan kina so ma zaki iya bani wani umarni kema na miki alk'awarin zanyi duk abinda kika saka ni indai bai sab'awa shari'a ba."

Duk maganganunshi babu wanda ya shigeta bare har yayi tasiri a zuciyarta, amma kam maganarshi ta k'arshe tayi armashi, dan haka ma ta d'an saci kallon liman da shima ya kalleta a fakaice sukayi murmushi, saida ta gyara tsayuwa tace "Ka tabbatar zakayi duk abinda zan saka ka?"

Da ladabi yace "Eh Umma, insha Allahu zanyi indai baifi k'arfi na ba."

Kallon Abba tayi wanda ke tsaye yana kallon ikon Allah kafin ta kalli sauran kishiyoyinta, tab'e baki tayi sannan ta kalli Imran tace "Ina so ka auri 'yar waziri."

Da sauri Imran ya k'ura mata ido yana kallo, liman ya kalla ya kalli Abba dake tsaye har yanzu, kallon waziri yayi tare da matarshi da ya ga ita tuni harta washe hak'ora, a cikin ranshi kawai ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahumma ajirni fi musibati, wak-lufli khairan minha."

Kallonta yayi yaga ta kafeshi da ido, babu yanda zaiyi haka yace "Na amince Umma, Allah yasa hakan ya zama alkairi a gare ni."

Sai lokacin ta nutsu ta zauna tana kallonshi tace "Kaga kenan sai a d'aura auren tare ko?"

A hankali ya kalli Abba da kamar ka k'yarta mishi ashana ya kama da wuta, d'auke kanshi yayi daga kallonshi saboda tsoro da kwarjini ya kalli liman, cikin girmamawa yace "Ku gafarce ni Liman, idan babu damuwa ko za'a iya d'aga auren nan har nan da sati d'aya, dan bana so daga rasuwar takawa ace nayi aure kuma har mata biyu a lokaci d'aya."

Da fara'a liman yace "Babu komai mai martaba, wannan ma shawara ce mai kyau, sannan sati kamar gobe ne idan da rai da lafiya, Allah dai ya nuna mana yasa alkairi."

Haushi ne yasa Abba barin falon rai b'ace inda Ammie ta bi bayanshi, harsu Imranatu da su Naseer ma bin bayansu sukayi, Abbas ma cikin kamala ya fita tare da Imran d'in inda suka k'ara tattaunawa akan lamarin, daga nan shima gidan kakannin na su ya nufo wanda suka rasu shekaru da suka wuce yanzu sai yan uwan mahaifiyarsu ne a gidan da iyalensu, tun a k'ofar gidan ya had'u da Abba da su Bashir cirko cirko suna kallon Abba daya jefa jakarshi a mota, da mamaki Abbas ya kalli Ammie da ita ma take kallonshi jiki a sanyaye yace "Ammie lafiya? Ba dai tafiyar ce ba?"

Cikin k'asa k'asa da murya tace "Nima tun d'azu abinda nake tambaya akai kenan ya min shiru."

Abba daya rufe boot d'in mota zai shiga mazaunin matuki ne yace "Duk mai tafiya ya zo mu tafi, wanda ba zashi ba kuma saiya zauna."
Chapter 54 · 0% Book details