← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 198

Sashe 106

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gaskiya banyi tsammanin haka ba, sam abun baiyi min dad'i ba, cikar kamalarka tasa ban tab'a maka wannan zaton ba, tashin hankalin daka jefamu cikinshi Allah kad'ai yasan iyakarsa, amma yanzu a matsayinmu na manya ba zamu ce da kai bamu yafe maka ba, domin kuwa bayyana da kuma tonuwar lamarin nan a yanzu bayan tarin shekarun da aka kwashe ya isa yasa mu fahimci akwai wani al'amari mai girma, kuma gashi a bayyane auren *Maryama* da Junaid yayi, sai mu musu fatan alkairi."

Yana gama fad'a ya wuce shima inda colonel da kanshi ya bud'e mishi mota ya shiga suka wuce. Husseina na zuwa gida d'akinta ta wuce ta dinga kuka, sam bata so had'uwar ta da shi ba, amma gashi yau ta gani, haka farin cikinta ya koma bak'in ciki, haka shima Labaran, kana ganinshi zaka gane yana cikin damuwa, sai dai shi har zuciya yana so ya gana da mahaifinshi, *uba*, wanda ya rasa tsawon shekaru, bai tab'a d'ora idonshi akan ko da dangin ubanshi ba bare uban. Kamar yanda baya b'oyewa Soueiba komai yanzun ma bai b'oye mata ba, ita kanta abun ya d'an dameta sai dai bai hanata karb'an duk wani daya zo gidan dominta ba.

Tako kamar na gwiwa, d'aya bayan d'aya sai kace wata sarauniya, yayin da mai aikinta ke biye da ita a baya rik'e da jakarta, babbar riga ce jikinta mai kama da babbar rigar maza, d'aurin d'an kwalin ya hau kanta sosai, sai yalolon gyalen data d'ora a kafad'a d'aya da manyan waya har biyu a hannuwanta, zobuna da sark'a da yan kunnai duk gwal ne, dogayen takalma a k'afarta da suka dace da kalar kayan, da gani babu tambaya kasan mai yana aiki a wurin, jan nata har ya k'azamce ta yanda take d'aukar ido, ga kuma hodar data d'auka ta k'ara fito da ita, cike da k'asaita da jin kai da isa ta k'arasa tsakiyar filin da ake kad'in guitar. Yau a k'ofar gida ne ake kad'a guitar d'in sai tarin yan zaman biki da suka zagaye mawak'an suna kallon rawar da wasu maza keyi irin ta buzaye, bayan k'arar guitar haka wurin ya hargitse da shewa irin ta buzaye (ma Sajida nasan zaki fahimci irin shewar, 😂) wasu na karkad'a harshe abun birgewa ana rawa wacce tafi kama da tsalle tsalle, dan wani tsallen sai anyi k'asa sosai ake yin sama ana harba k'afafu 😂(abun birgewa). Zuwan *Aissata* yayi daidai da zuwansu Ammar shi da abokanshi wanda suka zo d'aukar abincin da yasa Zeituna ta girka mishi, zai shiga gidan Sayyada yar Fatime da kuma wasu daga cikin yan mata suka taho wurinshi, nan suka tilasta mishi sai sun d'auki hoto dashi, sun d'auki hoton zai shiga sai kuma ya kalli wurin taron, nan ya hangi Aissata ta bud'e bakin jaka tana watsa kud'i kamar hauka, murmushin zaki gane kurenki yayi mata ya nufeta, nan ya kutsa filin taron ya sameta yana murmushi yace "Uwarmu sannu da k'ok'ari."

Kallonshi tayi a sama tace "Cava."

Kallon mai bisa ruwa ya mata yace "Uwa irin wannan lik'i haka, kice dai aljihun uban namu yayi kuka yau?"

A wani yamutse ta kalleshi tace "Qu'est ce que tu remarque (Me ka lura dashi)?"

Murmushi ya mata yace "Eh to, da yake ai a lokacin aurenku da tonton munje Niamey, kuma har gidanku muje kafin ma d'aurin auren, in baki manta ba ai har d'akin Ummynki na shiga na ci abinci."

Kallonshi tayi da alamar rashin fahimtar zancenshi ko d'aya, hakan yasa tace "De quoi tu parles? (Akan me kake magana), je ne comprends rien (Ban gane komai ba)."

😂 _Hyahyahya, bata gane komai ba, yana nufin ya ga gidanku ke d'in ba yar kowa bace bare ace zaki iya fantamawa da kud'in gidanku._

Murmushi ya mata ya k'urawa fuskarta ido yace "Amma uwarmu powder nan fa ta karb'i fuskarki, wallahi yanda kika san wata kyakyawar sarauniya."

Dariya ya mata ya wuce cikin gidan, ganin babu isassar hanyar da zai wuce yasa shi tambayar *Farisa* k'anwar Jibril inda uwa Zeituna take, ita ta fad'a mishi suna gidan da za akai amare suna girki, da mamaki ya kalleta yace "Gidan da za akai amare? Wane gidan to? Bayan kowa da nashi gidan, Ina ne gidan?"

Nuna mishi gidan nan tayi tace "Yah Ammar gaya nan, yanzu ma ana kai kayansu ne ana gyaran d'aki."

Jim yayi alamar tunani, murmushi ya saki yace "Duk yanda akayi wannan aikin Alhaji ne, dan shine kad'ai yake matuk'ar son ya ga iyalinshi a wuri d'aya, baya son ganin sunyi nesa da juna, shiyasa duk da kowa na da hali amma suke manne gida d'aya." Kallon Farisa yayi yace "Je ki kira min ita."

Galala ta kalleshi jin yace wai ta kira mishi ita, Zeituna fa yake nufi, wucewa tayi shi kuma ya fito dan ya jirata a waje, sai dai yana tunanin yanda zasuyi rayuwar aurensu a kusa da iyayensu, a gaskiya ya so ya bar gidan nan ko ya samu salama, amma kuma ba zai iya yi wa Alhaji musu ba, yana cikin tunanin nan Zeituna ta fito cikin shirinta sai dai duk ta had'a gumi saboda aikin da suke, girki ya tambayeta tace an ida dan haka yasa aka fito da manyan kuloli aka zuba musu, su Amar na zaune a k'ofar gida suma suna nasu casun, sai dai ko magana bata had'a shi da ko d'aya daga cikinsu ba, sai Junaid wanda tuni wasu daga cikin dangin Alhaji da kuma dangin Soueiba suka tafi d'aukar amaryarshi Goûré tare da abokanshi.

Hajia ce tsaye a d'akin Alhaji ta tisashi gaba tana fad'in "Akan mene zaka musu gini ba tare dana sani ba? Sai yanzu kawai ana maganar gyaran d'akin sai ka wani ce wai ga gidansu nan, sun fad'a maka suna sha'awar zama anan d'in ne?"

Shiru Alhaji ya mata kamar bai jin me take cewa sai jan carbin hannunsa da yake, d'orawa tayi da "Babu wanda baya da lafiyayyen gida a cikinsu, an musu wannan tanadin ba tun yau ba saboda irin wannan ranar, kuma kai ma kasan da haka, amma ka had'e musu gida d'aya su hud'u, kuma wannan kurkukun gidan me zai musu? Sai kace wasu jarirai ne su da ba zasu iya kula da kansu ba saida taimakonmu, to ni gaskiya wannan gidan bai min ba, inhar kana son su zauna kusa da kai ne to sai dai in zaka raba musu gidan ko da hakan na nufin ka siye duk rabin unguwar nan ne."

A hankali cike da dattako ya d'ago kai ya kalleta, hak'ik'a shi d'an halak ne, kuma har yanzu yana tuna hallacin mahaifinta gareshi, wanda kusan shine silar arzik'in shi, ya mishi hallaci sosai a rayuwa, dan haka har yanzu yake iya shanye duk wani wulak'anci da k'ask'anci daga wajenta. Murmushi ya sakar mata tare da mayar da kanshi ya sunkuyar, hakan kuma k'ara b'ata mata rai yayi, cikin hassala tace "Wato ga mahaukaciya ko? Shikenan ba komai, yanzu fad'a min ita kuma waccen k'ofar da naga ana yi ta kusa da b'angaren samari ta mecece?"

Ba tare daya kalleta ba yace "K'ofar da zasu dinga shigowa kai tsaye ba sai sun shigo ta waje ba."

"Amma w..." Kallon daya mata yasa taji ta kasa k'arasawa, ita kanta tasan a cikin zamantakewarsu akwai ragowa da d'aga k'afa, ta kuma san yana k'yaleta ne kawai saboda mahaifinta, amma ba dan haka ba ko a zahiri tasan yafi k'arfin zama lusari a gidanshi, turo mishi d'an k'aramin bakinta tayi mai kama dana Ammar tare da jujjuyashi ta fice da sauri, murmusawa yayi tare da girgiza kai yace "Allah ya shiryaki Zeeya'atu, ina fatan ganin ranar nan."

Duk da a k'afa aka shigar da amare d'akunansu, amma hakan bai hana abokanan angayen yin kururuwa ba a k'ofar gidan kan ababen hawansu, saida suka tayar da k'ura sukayi juyi da motoci, Maryama ma sun iso lafiya ta shiga d'akin ta. B'angare hud'u ne a cikin gidan wanda daga waje ake mishi kallon k'arami, kowane b'angare matsakaicin doron zabuwa 😂 ce aka mishi, a kowane b'angare kuma yana d'auke da falo da d'aki uku a ciki sai k'ananun madafa (cuisine), a kowane d'aki kuma akwai ban d'aki a ciki bayan wasu ban d'akin dake akwai guda biyu a waje, idan ka cire Maryama da ita ma babu laifi an mata kayan d'aki, duka amaren saida aka cika dak'unan da kaya, Gambo da Labaran ne sukayi wannan k'ok'ari bayan doguwar musu da akayi, Labaran yace shi ya d'auka zaiyi musu kayan d'aki, colonel yace shi zaiyi, lieutenant ma haka, a k'arshe dai Gambo da Labaran suka barma, babu ce kawai babu a d'akin su, hatta kayan kallo basu bari ba saida suka zuba musu, kuma kayan duk sanfiri d'aya ne kala da abinda ba'a rasa bane ya banbanta.

*Party*

Kayan da Ammar ya d'inka mata ne ta saka, leshe ne da ak'alla kud'in zasu ishi wani talakan rayuwa na tsawon watanni, kalar ruwan madara ne da bleue wanda ya k'ona sosai, haka shi shi ma tanffatsetsen yadin dake jikinshi kalarsa take, mota dai ba wata tsiya ba kam kamar suyi magana, dan wajen ajiye motoci a babban hall d'in ma kasa d'auka yayi, duk girman gurin saida aka matsu akayita had'a gumi, har ya zama ba'a jin tashin kid'an dake wurin sai jininin mutane da kuma hayaniyarsu. Da gani kasan babban biki ne na manyan mutane kuma masu tarin dangi, kowa daka gani shafar gumi yake saboda matsatsi yayi yawa, abincin kam dama ko da colonel ya samu labarin jama'ar dake wurin ya sake odar abincin a restaurent har guda biyu, da hakane aka samu abinci ya wadata a wurin, duk wanda bai samu ba to baya kusa sanda aka raba. Hasken waya kam ta ko ina ganinshi kake ana d'aukar hoto, ana cikin wannan rak'ashewa aka ce Hamna ta zo a d'auki hoto kuma a dole su sa Ammar tsakiya.

Hamna na tsayawa ta wurga masa harara tana gunguni k'asa k'asa, Ammar dake amsa waya cikin akasi idonshi suka sauka kanta tana harararsa, kashe wayar yayi ya murtuke fuska yace "Ke uban wa kike harara? Allah kankana ki kiyayeni."

Murgud'a masa baki tayi tace "Ank'i a kiyayeka, da wani abu da zakayi ne?"
Chapter 106 · 0% Book details