Sashe 132
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mik'ewa yayi yace "Ni zan koma, da yake matata ta haihu yau d'in nan."
Da fara'a sosai yace "Ah masha Allah, me aka samu?"
"D'a ne, aiki ne aka mata."
Tsaye ya mik'e shima yace "Allah sarki, Allah bata lafiya ya raya kan sunna, yanzu ku nawa ne ga Labaran?"
Murmushin yak'e ya masa yace "Mu biyar ne, maza uku mata biyu."
Ammar na zuwa gida ya samu Junaid zai shiga falon Hajia, gaisawa sukayi sai Junaid yace "Yawwa dan Allah muje tare ka rakani wajen Hajia."
"Lafiya?" Ya tambaya fuska a had'e, nan ya kora mishi bayanin abinda ya faru, kallonshi yayi yace "Yanzu kana nufin baka taimaka ba saika nemi izininta?"
"Ni ba izininta zan nema ba, zan dai fad'a mata ne kamar yanda ta buk'ata."
Girgiza kai yayi yace "Shashashu ta d'aukeku, wallahi na tabbata dan tayi gadara da an nemi alfarma ne a wajen zuri'arta shiyasa tayi haka, ko ka manta abinda Alhaji ya fad'a mana ne wanda yasa shine silar da bata shiga sabgar data shafi Alhaji Innusa da iyalinshi, dan haka kawai kaje ka taimaka musu indai zaka iya yan uwanka ne."
Cikin fargaba yace "To ai ina jin tsoron abinda zata iya yi kuma idan taji, ka fa san halinta."
Tsaki Ammar yayi ya shak'o bakin aljihun rigarshi ya fizge shi har zuwa motarshi ya bud'a ya jefashi ciki, zagayawa yayi ya shiga shima suka tayar, suna barin gidan yace "Allah ya baka dama amma ka kasa anfani da ita wai har saika nemi izinin wata hallita, wannan wace irin rayuwa ce kuke? Matar da ko dukanku ba zata iya ba tsabar k'arfinta ya k'are, yo ni duk hukuncin da zata yanke ko take yankewa a kaina ai alkairi yake zamar min, dan haka ta dad'e bata yanke hukuncin ba."
Bai tsaya ko ina ba sai cikin harabar makarantar, tare suka fito inda Junaid ke gaba har ofishin shugaban makarantar, bayan gaisuwa suka fad'i abinda ya kawosu, sosai suka bada baki tare da alk'awarin jan kunnenta hakan ba zai sake faruwa ba, nan komai ya wuce suka dawo bayan enveloppe d'in da Ammar ya aje mishi a matsayin ya sha ruwa, daga nan tare suka wuce d'an gulbi suka sanar dasu yanda ake ciki, farin ciki da murna basu misaltuwa wajensu.
*Tazarar* minti sha biyar ta saka tsakanin lokacin saukar jirginsu da lokacin data fad'a mishi ya zo d'aukarsu, a wannan tsakanin ne sanda jirginsu ya sauka ta samu ta tura Hamna gida, lokacin na cika kuwa sai ga lieutenant tare da dreba suka d'auketa, tunda ya karb'i Shureim ya kasa saki sai wasa yake mishi kai kace yana fahimtarshi, gidan Gambo suka sauka anan suka samu tarba ta musamman kamar wasu sarakai, sun ci sun sha Alhamdulillah kuma kwanansu d'aya, washe gari da safe kuma suka shirya dan jirginsu zai tashi lieutenant yace ba za ayi tafiyar mota da yaronshi ba *(Shureim Ammar)*, Hamna kad'ai ta rakasu filin jirgi, a lokacin da suka juya zasu shiga jirgi sai taji kamar Ummy na tafiya da zuciyarta, bugawar zuciyarta ce taji ya k'aru, bakinta sai rawa yake zuciyarta na karkarwa a tsakanin k'irjinta, suna daf da shiga Ummy ta juyo ta kalleta, idonta kad'ai suka ankarar da ita halin data shiga ganin za ayi mata nisa da abinda ta haifa, dawowa Ummy tayi ta tsaya gabanta ta mik'a mata shi, jiki na rawa ta karb'eshi ta sumbaci ko ina na fuskarshi, k'ura mishi ido tayi tana kallo wanda hakan yayi sanadiyar zubar hawayenta akan jikinshi, Ummy na gani tace "Hamna kuka kike?"
Kallon Ummy tayi tace "A'a." Mik'a mata shi tayi ta share hawayenta, cike da tausayinta Ummy tace "Hamna zan kula miki da shi kamar yanda ke ma zaki kula dashi, ki ci gaba da addu'a insha Allahu komai zai daidaita, ni zan d'auki alhakin duk abinda zai faru, ki kula da kanki kinji ko? Sannan kar kiyi wasa da shan magunanki akan lokaci saboda zasu taimaka miki sosai."
Kai kawai ta jinjina alamar to, tana kallo suka shiga sannan ne dreban da suka zo tare ya fara mata oda, juyawa tayi ita ma suka koma gida sai kuka take. Su Ummy kuma suna zuwa gida suma akayita farin cikin ganinsu, inda kowa ke karb'an beby yana gani.
Har d'aki suka sameta tare da Amna suka gaisheta, zaune sukayi inda Ammar ya k'arasa gaban gadon ya sunkuya ya d'auke shi, a hankali yayi zaune yana kallon fuskarshi, kowane motsi nashi yana binshi da hankali da nutsuwa, shi kam har ga Allah abu na daban yake ji akan k'ananshi da bai tab'a jinshi akan kowace hallita a doron duniya ba, cikin nutsuwa ya rab'ashi a jikinshi ya rumgume sosai ya d'ora bakinshi kan wuyanshi, lumshe ido yayi sakamakon tattausan turarenshi daya shak'i k'amshinshi, bud'a ido yayi ya kai bakinshi kan labb'an shi da nufin sumbata, sai kawai yaron ya bud'a baki ya d'auka nono ne za'a saka masa, caraf ya karb'e leb'enshi na k'asa ya shiga tsutsa da sauri sauri, baisan sanda dariya ta kubce mishi ba saiya shiga k'yak'yatawa ba tare daya cire mishi leb'en ba, Amna na kallonsu sai taji ina ma nasu yaron ne a hannunshi, Ummy na ankarewa da haka ta taro mishi hannaye tace "Kawo shi yasha." Da k'yar ya cire leb'enshi daga bakinshi ya mik'a mata shi.
*Kwana uku*
Duk abin duniya ya shawa Hamna kai, sam yanzu ta daina jurar wulak'ancin Aissata, zuciyarta kawai tafasa take ita kanta bata san dalilin b'acin ran nata ba, yau ma hakane ya kasance da safe ta mata duk abinda takeyi, amma tsabar fitina sai Aissata tace ta gyara mata d'aki, ta shiga tana gyara ta shigo tana mata kinibibi, ganin tayi banza da ita tana aikinta yasa Aissata cewa "Kinga wurin nan bai fita ba."
A k'ufule ta kalleta tace "Saiki gyara da kanki mana."
Cikin d'aga murya tace "Hamna ni kike fad'awa haka? kin rainani ko?"
"An rainakin kiyi abinda zakiyi." Mik'ewa tayi ta kalleta sosai tace "Ke nafa gaji da abinda kike min, tun farko Allah ya isar mahaifina ce ta min katanga da dakuwa dake, amma wallahi badan haka ba ke baki isa ki min abinda kika min ba."
Fad'a Aissata ta fara yi da hausa da zarma da french saboda harshenta bai nuna ba, jefar da abun gugar tayi ta harareta sama da k'asa tace "Matsalarki ce."
Fita tayi daga d'akin ta shiga nata, bata tsaya komai ba ta had'a kayanta tsaf a akwati ta fito, dreba ta samu tace ya ciro mata ticket, shima bai b'ata lokaci ba ya ciro ya kawo mata ta ajiye.
Tunda asuba ko da tayi sallah ta shirya, *07:30* ta fito ta samu dreba yasa jakarta suka bar gidan, Gambo bai sani ba haka ma Aissata dake wurin motsa jikinta da babu wata tsiya da take ragewa. Suna zuwa ta shiga bus suka d'aga zuwa Maradi, ita kanta tasan saboda wannan d'ayan ne zata koma garin nan, wannan d'ayan kuma ba kowa bane sai *Shureim Ammar Hassan Suley Gaga*.
*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*BADAK'ALA*
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
👨👩👧👦 _*AHALI NA*_👨👩👧👦
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.N.A]* ☆🖊️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_48_
Tana shigowa gidan ma yer uwarta ce ta fara karo da ita tana d'an safa da marwaa tsakiyar gidan, suna had'a ido dukansu ihu suka saka Hamna ta saki jakarta suka rumgume juna, cikin farin ciki Amna dake tura tulun ciki tace "Ya kika zo mana haka ba zata? Ke da wa kika zo?"
Bata amsa tambayarta ko d'aya ba ta saketa tana k'are mata kallo tace "Amna dama haka kika koma? Yanzu kenan da ban zo ba da sai dai naji labarin haihuwarki?"
Hararanta tayi tana d'an kai mata duka a kafad'a tace "Haihuwata ko haihuwarki dai."
"Me?" Ta fad'a da k'arfin bala'i, ba iya gabanta bane kawai ya fad'i har jinin jikinta ma saida ya matuk'ar hawa, dariya ta mata tace "Idan Amna ta haihu ai Hamna ce ta haihu."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Wai Allah, amma dai cikin nan naki yan biyu ne ko? Wannan abu haka."
Cikin shagwab'a tace "Shiyasa na so nayi éco (scanning) amma yah Ammar yace sam bai yarda ba, yanzu haka gobe zan koma awo har na cinye sati biyun da aka bani, nak'udar tsaye kawai nake fama da ita."
"Karki damu, ai da sati biyu biyu ma kina iya cinye wata biyu, kawai ke dai karki zama lusara mai son jiki, ki dinga tafiya mai tsayi saboda ko nak'uda ta taso miki ma zata zo miki da sauk'i, amma kin fara zubar da ruwan zak'i?"
Waro ido Amna tayi a hankali sai kuma ta k'ank'ance su tana kallonta da mamaki, ba tare data daina mamakin ba tace "A ina kika san haka ke kuma sai kace wacce ta tab'a haihuwa?"
Tsuru Hamna ta mata da ido, saida ta k'ak'alo abinda zata fad'a kafin tace "Kiji
sai kace ba mace ba, to wannan ne sai mace ta haihu zata sani."
Jakarta ta d'auka suka nufi falon Hajia tana fad'in "Muje ki gaishesu sai muje b'angarenmu musha hira."