← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 198

Sashe 173

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin jin dad'i ya karb'a ya fita, ita kuma saida ta shafa turare sannan ta d'auki gyale ta yafa tasa takalmi ta fito, su Zeinabu ta samu a falo ta fad'a musu tayi bak'o a waje zata shigo dashi ciki, fatan alkairi suka mata ta fice.

Tana fita ta shiga mamakin wanda ta gani, kusa da salon d'inta yake nan take ganinshi zaune a wata fada, da mamaki tace "Kai ne?"

Murmushi yayi "Kin gane ni ashe? Na d'auka yanzu ma saina kwatanta miki."

D'an murmushi tayi tace "Na gane ka mana."

Gyara tsayuwa yayi yace "To ya kike?"

"Lafiya lau, mu shiga ciki ko, ba'a barinmu tsayawa kan hanya."

Gabanshi ne yaji ya fad'i sosai, tambaya ya wa kanshi to me ya kai na shiga ciki? Shi fa ba wata babbar magana bace ta kawo shi wajenta. Murmushin yak'e ya mata yace "Amma kafin nan mu gaisa ki san suna na, in ya so sai mu shiga ko."

"Amma ai duk zamu iya yi a ciki." Ta fad'a fuskarta a d'an had'e, kallonta yayi yace "Hakane, amma in d'an jin tsoro."

Wani irin kallo ta masa tace "Tsoron me kuma?"

Cikin rashin gaskiya yace "Eh to, kin gane? Kawai dai, gidan na ku ne, nasan mutanen cikinshi, akwai abokaina dayawa."

Wani kallo ta masa zatayi magana Imam ya fito daga cikin gidan da gudu yana kuka, tana ganinshi ta durk'usa ta rik'eshi tana fad'in "Imam me ye? Waya tab'a ka?"

Kafin yayi magana Shureim ya fito da wayarta a hannu ya zo ya tsaya yana fad'in "Aunty wai dan na ce ya bani nayi jeux (game) shine ya k'i."

Ranta a b'ace ta kalle shi tace "Shine ka fizga da k'arfi?"

Mik'ewa tayi tsaye ta kamo kunnenshi ta kwad'a masa mari tana fad'in "Shine zaka saka min yaro kuka? Dan ubanka ban hana ka tab'a min su? Wallahi ka sake karb'ar min a waya a hannun sai na ci ubanka a garin nan."

😂 *Hamna kin taro match fa, da kin duba bayanki kafin ki fad'i haka.*

*Ammar* da saida ya kusa kawowa gida motarsa ta tsaya, makanikenshi ya kira shi kuma ya k'araso k'asa saboda tafiyar ma na da anfani ga lafiya, tunda ya hangeta ya ganeta, k'ara hassala yayi dama a tafashe ya fita daga gidan, har yanzu yana nanata kalmar data fad'a ta *ina da saurayi*, ya rasa dalilin da yasa Hamna ta soka mishi wannan iskancin, a gaban iyayensu tace tana da saurayi kuma bata son auren shi. Sannan yazu ya dawo ya tarar da ita da saurayi a k'ofar gida tana hukunta masa yaro, wannan wace irin uk'uba ce? Bayan ta gaura masa mari kuma ta bishi da zagi, zagin ma ubanshi kawai take zaga, wato dan ta ga wani d'an iska a gabanta shine zata tsaya tana zaginshi, tunda dai ta zagi yaronshi ai da shi take.

Amma ba damuwa zaiyi maganin saurayin kafin ita, shi daya zauna yana kallo yana jin dad'i tana zagar masa yaro amma bai hanata ba, dan baisan darajar 'ya'ya ba saboda bai da su shi, da azama ya k'araso wajen ta bayansu ba tare da sun san da zuwanshi ba, saida ya tsaya da kyau ya toge sosai yasa k'afarsa ta dama a gaban k'afafun saurayin nan da ko sunanshi Hamna bata sani ba bare ta fad'a mana ya kwashi k'afafunsa.

Sai ji tayi kawai abu ya fad'i k'asa pamm, da sauri ta saki Shureim ta juya ta kalli ikon Rabb, bawan Allah bai san me ya faru ba, baisan wane shaid'anin bane a cikin shaid'anun, abinda ya sani kawai shine a cikin aljannun ma wannan gagararre ne, duk yanda akayi ko dai a gidansa ne suke tsaye ko kuma sun taka masa yara basu sani ba, amma wannan kwasa da aka masa ko jirgin sama yana shaida maka zai tashi ya d'aga ka daga kan k'afafunka bare kuma bil'adama.

Yana shirin bud'e idonshi daga k'asar da fuskarshi ta daduma yaji an tokara masa gwiwar k'afa a baya an hana shi tashi, bai yarda yayi gamo ba saida yaji an figi hannunshi ta baya anyi ciri dashi, yana jin sautin k'arar gotawar k'ashin shi sanda aka karya hannunshi, azaba ce tasa shi sakin k'arfinshi ya daka uwar ihu.

Yana jin k'ararshi ya sake cije leb'e yana fad'in "Au! Zaka iya ihu ashe."

Tsakiyar kanshi ya dafe ya rik'e hab'arshi da d'aya hannu da niyyar kawai ya juyar masa da wuya, an jima uban kowa bai mutu ba, Hamna data shiga firgici na abinda zai aikata bata san sanda ta rumgume shi ta baya ba ta rik'e hannayenshi gam ta fashe da kuka tana fad'in "Dan Allah Ammar sake shi baiyi komai ba, dan Allah karka kashe shi ka rufa mana asiri."

K'arfin tartsatsin da yaji kamar k'arfin dake cikin wutar lantarki ne, ba wai tsayawa ba daga masifa, hatta numfashin shi ma ta kusa sawa ya bar jikinsa, har jikinshi ma ya shida ita ta musamman ce, sannan dokinshi ma ya tabbatar da yana kewar mace, dan a take sak'on yaje ya kuma haifar da sakamako mai kyau. Sakinshi yayi tare da mik'ewa tsaye yana kallon mutumin, shi fa ko fuskarshi ba bai gani ba, tsabar fitina ce kawai da neman wanda za'a mutu tare, sai lokacin ta sake shi tana k'ok'arin su kalli juna sai kawai ya taka da sauri yaja hannun Imam da Shureim wanda dukansu sukayi shiru da kukansu suna kallon babbar harka, cikin gida ya shige dasu.

Cikin jin kunya ta kalleshi ya tashi zaune yana karkad'e k'asa a fuskarshi yana furzar data bakinshi, a hankali cikin taushin murya tace "Dan Allah kayi hak'uri kaji, kayi hak'uri da abinda ya maka, yayana ne."

Shi dai da har yanzu bai gama gane komai ba ga hannunshi dake zugin bala'i na karaya ko kallonta baiyi ba, ko da taga haka ta mik'e ta shige gida da gudu da niyyar yau saita kawo k'arshen wannan bura'ubar da yake mata a gidan nan. Shima yana ganin shigewarta ya fashe da kuka na gasken gaske yana birkid'awa yana rik'e hannunshi da yake jin kamar zai cire ya barshi, gashi ba zai iya tuk'a motar ba bare ya kai kanshi wajen magani, baida nutsuwar da zai iya kiran wani ya zo ya d'aukeshi, mai gadin gidan ne yaji kukan babban mutum a waje ya fito da gudu, da taimakonshi ko da ya duba hannun yace karaya ce, tsaf ya mishi magani yasa mishi magani yanata addua'r Allah ya sawak'e, saida aka gama yace mi shi "Amma ba kaine bak'on da ka zo wajen Hajia Hanne (Inji shi)?"

"A'a." Ya fad'a yana tashi tsaye, shima tsaye ya mik'e yace "Amma garin yaya ka karya hannu haka? Gashi kuma banga alamar hatsari ba."

Huyowa yayi ya kalleshi, hatsari? Hatsari ma yake cewa baiga alama ba, bayan abinda ya faru yafi karon babbar mota muni, juyawa yayi ya ci gaba da tafiya a hankali yana d'an sosa bayanshi inda ya daka mishi gwiwa, motar ya bud'a ya shiga ya tayar ya fara janta a hankali yana tuk'i da hannu d'aya, sai dai ya ci alhwashin ko ma uban waye wannan yayan nata wallahi saiya tara masa yaran nan na unguwarsu yan zaman kashe wando sun ciro masa jijiyar dake sadar da ji da ganinshi.

*Allah yaba mai rabo sa'a.*

*Ko da* ta shiga da masifa a falon ta same shi yana wa Shureim bala'i yana fad'in "Akan banzar waya zaka zauna ana zagin ubanka a gaban k'aton banza, me yasa baka buga wayar a k'asa ba ta b'are? Duk duniya idan ka cire ni ubanka da uwarka da kuma yan uwanka ban yarda ka d'auki raini a hannun kowa ba, kaji na fad'a maka."

Girgiza kai Shureim ya shiga yi yana sako da hawaye, tana bayanshi a hassale tace "Wannan har d'ab'ia ce kake jin kana koya masa to?"

Juyowa yayi ya kalleta, kallon jin haushi da zan iya miki komai, ganin bai tanka mata ba yasa tace "...

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:38 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_67_

Ammar me ye matsalarka da samari na? Akan wane dalili ne kullum ka ganni da saurayi saika wulak'anta ni a gabanshi ko kuma ka muzantashi? Me yasa? Ka fad'a min idan ba haka ba yau ni da kai a gidan nan wallahi sai dai duk mu babbake."

Da fari da kallonta yake yana tunanin hannun da idan ya bigeta dashi zata fi jin zafi, amma data ce wai duk su babbake sai ta bashi dariya, dariya ya shiga yi hankali kwance wanda hakan ya sake hassalata cikin d'aga murya ta kalli Hajia dake zaune tana kallonsu kamar tv tace "Hajia ki mana tsakani da bawan Allahn nan ya daina shiga tsakani na da samari na, tunda dai ba zamansa nake ba kuma ba aurenshi ne akai na da zai addabe ni ba."

A hankali Hajia ta d'an dafe kanta dan ciwon kai taji suna neman sanya mata, lallai da taso a had'a aurensu, amma yanzu tunaninta shine yanda wannan yara zasu zauna in aka aurar dasu, lallai gaskiyar Junaid ne gidan nan zai iya kamawa da wuta, ganin Hajia ma ta k'yalesu saita k'ara jin haushi tace "To Allah idan na sake tsayawa da saurayi ka min iskanci Ammar saina soke ka da wuk'a."

Hajia ta kalla tace "A matsayinki na kakarshi Hajia ki fara nema masa magani, dan wallahi ya gama kwancewa."

Sama da k'asa ta bishi da harara ta giftashi zata wuce d'akinta, cikin salon da ka rantse bashi yayi maganar ba yace "Nan gaba ma wuyansu zan fara takawa, kin k'waci kanki da rumgumar da kika min, amma kika sake gigin zagar min yaro sai jini ya fita a bakinki, dan abu d'aya dana lura dashi shine baki k'aunarshi, to ni ina son kayana ehee."

Tab'e baki tayi tace "Akan me zan k'aunace? Wannan d'in?"
Chapter 173 · 0% Book details