← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 198

Sashe 150

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon mamaki ya mata yace "Hajia Alhaji ne fa d'an uwan Alhaji na Abbanmu, ya zaki ce a masa haka?"

Cike da k'aguwa tace "To naji, idan ba zaka fitar dashi ba ka fad'awa Hajia tasan da zamanshi, kaga idan ta amince shikenan saiya zauna."

Tashi yayi tsaye ya juya mata baya yana fad'in "Hajia dai, Hajia dai, wai abun alkairi ma saika nemi umarnin Hajia, to wai ita ta busa mana rayuwar nan ne ko me?"

Mik'ewa Ummy tayi ita ma tace "Na sani dama ba zaka yi ba, ban isa na saka kayi ba saboda baka d'auke ni bakin komai ba, kaje kayi duk abinda kaga dama, amma ka sani shirme ko haukanka ba zai k'ara sani a damuwa ba, yanzu b'ace min a gani."

Kallonta yayi yace "Ummy me yasa kullum sai ki kore ni daga wajenki? Kina yawan fad'a min b'ace min da gani, me yasa?"

Cikin b'acin rai ta juya mishi baya tace "Saboda ban son ganin na ka."

K'uri ya mata da ido yana kallonta ta juya masa baya, rintse ido yayi yana sauke numfashi yana son zuciyarsa ta kwanta, bud'a ido yayi har sunyi ja sosai jijiyar kanshi duk ta fito, dunk'ule hannunshi yayi ya daki bangon wurin, juya baya yayi shima a lokacin ta juyo da sauri, yana juyowa suka had'a ido yace "Ba kya son gani na? Ni d'an halak ne Ummy kuma mai biyayya, tunda har kika fad'a da bakinki ba kya son ganina zan miki nesa da kaina ta hanyar samar miki da farin ciki, amma duk da haka duk ranar da kika buk'aci na zo gareki zan zo da saurina, saboda ke mahaifiyata ce kuma ina son ki, *ina sonki sosai* Ummy."

Fita yayi daga d'akin sai kawai Ummy ta durk'ushe ta fashe da kukan da bata san ma na miye ba. Shima yana fita bai kula kowa ba ya nufi b'angarensu, Amna na zaune cikin k'ananan kaya riga da wando sai yara dake wasarsu, cikin dakakkiyar murya yace "Ki shirya kayan yaran nan da safe zamu tafi Niamey."

Zaro ido tayi ta bishi da kallon mamaki shi kuma kai tsaye d'akin shi ya shiga, kamar hauka haka ya shiga had'a kayanshi yana turawa a akwati, jin Amna ta shigo shi kuma baya so ya zubar da hawaye gabanta ko ya sauke hushinshi akanta yasa shi saurin shigewa ban d'aki, da kallo ta bishi cikin sanyin jiki ta kalli kayan da yake ta bankawa a akwati, a hankali ta shiga gyara zaman kayan tana saitasu, tsawon lokaci kafin ya fito yana ganinta ya sunkuyar da kai yace "Bana no ki aje min kaya, kije ki had'a naki dana yaran nan, idan kuma ba zaki tafi ba ke kika sani zan d'auki yarana."

Da sauri tace "Amma yah..." Da k'arfi kamar zai tsaga d'akin yace "Amna bana son tambayar banza, kiyi abinda na fad'a miki kawai."

Shagwab'e fuska tayi ta sake takowa zata matso ya sake daka mata tsawa "Amna ki fita ki bani wuri, bansan ganin kowa a kusa dani, bana so na sauke b'acin rai na akan ki."

Da sauri ta sake takowa gabanshi tana fad'in "Na yarda ka huc..."

Wani bazawarin mari ne ya d'auke fuskarta dashi da yasa ta fad'awa kan gado da k'arfi ta kifa gaba d'aya, rintse ido yayi dan har cikin ranshi yaji marin, cikin hushi da fad'a yace "Na fad'a miki kiyi nesa dani, wai ke ba kya fahimta ne? Ki dinga yin nesa dani kamar yanda kowa keyi mana, yanzu gashi kinsa na mareki a banza."

Juya baya yayi da k'arfi yana dafe kanshi, cikin rawar jiki na bala'in marin data sha tana karkarwa ta mik'e, cike da k'arfin hali ta rik'o hannunshi ta juyo dashi gabanta, suna had'a ido ta fashe da kuka tana shafa kanshi ta ko ina tana fad'in "Dan Allah yah Ammar ka daina, tsorata ni kake idan kayi irin hushin, bana so ka daina kaji, na yarda ka huce a kaina amma karka cutar da kanka ko wani, dan Allah kaji."

Tsakiyar idonta yake kallo sai yaji hawaye na fitowa a idonshi, cakumarta yayi da k'arfi ya matse yace "Me yasa Amna? Me yasa Amna?"

Kuka kawai take har da ajiyar zuciya, jawota yayi jikinshi sosai ya rumgumeta, tun yana yi a hankali har ya fara saka k'arfi yana matseta sosai kamar zai mayar da ita ciki, duk da tana jin zafi amma haka ta daure, sun jima haka kafin ya d'ago ba alamar annuri ya saketa ya juya zai bar d'akin, da sauri ta rik'o hannunshi tace "Ina kuma zaka je?"

A hassale yace "Yaro ne ni Amna da sai kin tambaye ni inda zanje?"

Girgiza masa kai tayi tace "A'a, amma ba zan barka ka fita a halin nan ba yah Ammar, idan ka fita ranka a b'ace zaka iya yin komai."

Tsabar neman fitina saiya rufe ido yace "Amna ni? Mahaukaci dama kike kallona ban sani ba, eh lallai yau ta tabbata kowa mahaukaci yake d'aukata."

Cikin zubo da hawaye ta girgiza masa kai alamar a'a, k'wafa yayi ya juya zai fita ta sake rik'e hannunshi, fizgewa yayi da k'arfi zai bar d'akin ta tare gabansa da gudu, rufe k'ofar tayi cikin kuka tace "Wallahi babu inda zaka je, nasan halinka yah Ammar in dai har ka fita yanzu saika nemi wani da masifa, ka bigeshi ko ya bigeka shine burinka, dan haka na zab'i ka zauna tare dani in ya so ni ka kashe ni, amma hankali ba zai kwanta ba dan bansan da wa zakayi rigima ba."

Belt d'inshi ya fara zagewa yana fad'in "Shikenan, bari na fara miki laga-laga sai na bi ta kanki na wuce."

Matsowar da yayi kusanta da sauri yasa tayi saurin duk'ewa tayi k'asa tana jingina a jikin k'ofar, yana ganin ya saki d'amarar cike da tausayinta ya sunkuya ya kamota, bud'a ido tayi ta kalleshi saiya rumgumeta yace "Amna baki da hankali ko kad'an."

Saida ta rumgume shi sosai tace "Na sani yah Ammar, shiyasa nake so ka dinga saita ni."

Tallabo kanta yayi ya had'e bakinshi da nata ya shiga tsutsa, shiru komai ya kwanta aka shiga wata duniya, ta d'auka an bar maganar tafiya ashe ko kad'an, cikin muryar bayar da umarni ya nuna ta yace "Ki tabbatar kin had'a kayanki dana yaran nan."

Kallonshi tayi, ba zata iya magana ba yanzu kam dan zasu sake samun matsala, sai kawai ta bishi da to da niyyar yin sun tafi ta lallab'a shi tasan meya faru haka.

*Washe gari* da sanyin safiya suka fito a shirye, ko falon Hajia bai shiga ba yace Amna dai taje ta fad'a musu zasuyi tafiya dan kar aga basu nan, haka ta shiga jiki a sanyaye bayan ta gaishesu ta fad'a musu, kowa yayi mamaki amma tunda tace tare dashi ne sai aka bisu da addu'a kawai, tare da Hamna suka fito suka tsaya farfajiyar gida inda suke iya hangenshi tare da yaran a mota yana jiranta, tsaye suke suna sallama inda Hamna ke d'agawa yaran hannu, idonshi na kanta ya fito da wayarshi, sak'o ya rubuta ya turo mata yana ci gaba da kallon fuskarta.

Tana jin wayarta tayi k'ara ta fito da ita ta duba, kallonshi tayi ta kuma kallon wayar, sak'o ne ba mai tsayi ba, amma ma'anarshi da abinda yake nufi da kuma yanda ita ta fahimci sak'on yayi kusa ya tsayar da tafiyar jinin jikinta, kad'an ne ya rage bata iya nuna abinda ke ranta ba, kafe wayar tayi da ido tana sake maimaita karanta sak'on mai d'auke da wasu tsirarun kalmomin kamar haka _"Bansan me yasa ke da Ummy kuka tsane ni ba, amma zan tafi nayi nesa daku dan na hutar da zukatank'u."_

Suka tsaneshi fa yace, shin yasan me take ji a zuciyarshishi a game da shi kuwa? Bai sani ba, Amna dake kallonta ne tace "Yer uwa ko zamu tafi tare ne dan kar kiyi kewata?"

Cikin gigita, cikin rashin sanin madafa, cikin hargagi da son fitar da abinda ke ranta, cikin yanayin da bata san tayi magana dashi ba, yanayin da bata tab'a ma yer uwarta magana ba sai gashi yau dalilin *namiji* ta mata, tsawa ce mai ban tsoro ta mata ta hanyar fad'in "Ba zanje ba malama ki rabu dani, kiyi rayuwarki nayi tawa, duk ke ce silar komai."

Tana gama fad'a ta taka da sauri ta nufi motar, ta tafi da niyyar yin wani abu daban, amma Ameer na lek'o kanshi ta mota ta sauke ido akan yaron sai taji ta rasa kuzari da k'arfin halin, sai kawai ta juya ta nufi inda motar ta take da sauri. Amna da tayi mutuwar tsaye odar daya mata ce ta farfad'o da ita daga doguwar sumar, da k'yar ta iya d'aga k'afarta ta shiga motar suka fita daga gidan, saida ta ga fitarsu da wasu mintuna kafin ta fita ita ma tana kuka.

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_56_
Chapter 150 · 0% Book details