Sashe 151
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammar dai ya tafi tare da iyalinshi, inda suka kwana biyu a garin Niamey a masaukin da mahaifin Amna ya tanadar musu, a kwana na uku ya gama musu shirin komai har da allura saida aka musu na shiga wajen k'asarsu, ticket ya cirar musu ya aje motarshi anan gidan suka tafi *cotonou*, a kwanakin da sukayi saida yayi magana da abokinshi likita wanda ya yarda da k'warewarshi kan ya ci gaba da duba mishi Inussa, sannan duk abinda ake buk'ata a mishi magana zai bayar, sun isa lafiya kuma da yake harka ce ta dala ya samu masaukin daya dace da tsarinshi da kuma iyalinshi, sun fara rayuwarsu kamar yanda suke yi a gidan, amma anan kullum zai fita waje sai Amna tace ya kula kar ya ja musu rigimar da za'a k'onasu da ransu, shi kuma abinda yake fad'a mata shine "Amna ke ma mahaukaci kike d'aukata, amma ba komai zan kiyaye ko saboda ke."
*A gida* fa abubuwa sun shiga juyin waina inda komai ya fara tafiya a hargitse, Hajia da kanta tace ta amince da auren Junaid da Salma, sannan ta bawa Amar dama ya nemi auren Farisa, ta b'angaren Junaid anyi matuk'ar farin ciki ganin zumunci zai had'u tanan wajen, amma a b'angaren Amar tashin hankali ne ya kunno kai daga wajen Umaimah, dan kuwa ranar da taji labarin saida ta mata dukan tsiya har cikin falon uwarta, hakan ya b'ata ran Amar yace ta je gida kawai saiya neme ta, Alhaji ne ya bashi hak'uri yace ya lallab'ata kishi ne, Zeinabu ma hak'uri take bata dan ita yanzu ta nutsu tun abinda ya faru, amma Umaimah sai botsarewa take wai akan me zai mata kishiya kuma k'anwarta data yarda da ita har take shiga d'akin baccinshi. Saboda gudun matsala yasa Soueiba da Labaran cewa in akwai matsala kawai a bari, Hajia tace ai bata isa ba Umaimahr banza ko uwarta bata isa ta hana auren ba, Farisa aka tambaya idan tana so to babu fashi, abinda ta fad'a kawai shine "Ni karatu nake so nayi."
Hakan yasa Amar d'aukar alk'awarin barinta tayi karatunta har aiki ma udan tana so, magana ta kankama sosai har anyi komai an gama an saka rana.
Duk da akwai mutane a gidan kuma ana hayaniya, amma kowa ya tabbatarwa da kanshi akwai mutum d'aya da babu a gidan, babu nishad'i ko wata raha, Hajia Alhaji da Ummy abun yafi damunsu fiye da kowa, ko kiransu a waya bai cika yi ba saiya kwana biyu, yanzu Hajia saita wuni ta kwana a kujerar nan zaune bayan gaisuwa babu wanda zai tsokaneta ko ya sakata dariya ko nishad'i, idan abinci ake ci haka kowa zai gama ya tashi, inba tashin hankali ba na auren Amar ko kuma sab'ani na zaman tare baka jin komai a gidan, dan haka yanzu kowa ya zama shiru zaman d'aki yafi yawa, kowa saiya had'a kan yaranshi k'ananan ya shige d'aki ya zauna abinshi, har Zeituna ma dake da yarinya d'aya, sai dai ita suna waya da Ammar kullum dan yana girmamata sosai.
Hamna ma gaba d'aya ta canza kamar ba ita ba, jikin nan nata duk ya rage yanzu sai lalacewa take, tafi son zama wajen aikinta fiye da ko ina, idan ka ganta gidan nan da dare ne, kuma gari na wayewa zatayi sammako ta fita, hatta Shureim yanzu ta rage kusanci dashi kamar da, sai dai tana waya da Amna akai akai suna gaisawa, wani lokaci haka zata tashi tayi ta b'ata rai a banza, a haka ita ma rayuwar ta godewa Allah kawai zata ce.
*A kwana a tashi* ba wuya a wurin Allah, sai gashi an sake d'aura auren Junaid da Salma da kuma Amar da Farisa sai Jamil da amaryarsa *Zeinab* shima, amare sun tare sun fara rayuwarsu mai cike da jarabawa, tunda akayi bikin aka gama Umaimah ke hushi da Amar bata kula shi, har ranar girkinta ya zagayo da safe ina abin kari tace ai bata dafa dasu ba, banza ya mata ya fita da rana ma bai dawo gidan ba, da dare ma daya tambayi abinci tace yaje amaryarshi ta bashi, murmushi ya mata ya fita daga d'akin, yana zuwa ya samu amaryarshi kam ta mishi dubaru ya cika cikinshi, ko da ya dawo bai kulata ba ya kwanta shima. Washe gari ya bata kud'i haka ma Farisa yace tayi girki, lokacin da take aiki a madafa Umaimah ta dinga masifa akan me zata karb'e mata ranar girki, ita dai bata ce komai ba saboda tana tsoronta.
_Yan uwa rayuwa wata aba ce dake tattare da k'alubale da shubuha, wani lokacin zata iya zuwa maka yanda kake so, wani lokacin kuma ta zo da sab'anin haka, ka yarda ka karb'a ko kuma ka kafirce mata ya rage naka, so da dama mukan so abinda ba alkairi bane a gare mu, haka ma sau tari mukan fifita tsana ga wanda yake alkairi gare mu, shiyasa a kullum ya kamata kayi fatan zab'in Allah._
*Daren yau* duk suna zaune ana cin abinci Jamila ta shigo da gudu wai Umaimah suna fad'a da Farisa sai dukanta take, da gudu kowa yayi b'angaren nasu suka same su, tsaf tayi zaune kan yarinyar mutane tana mai k'aramin ciki tana bugu, ba tsayawa komai colonel ya d'auketa da mari, da k'arfi yasa k'afa ya turata tayi baya yana fad'in "Jaka kawai, yaushe haukan naki yayi tsanani har haka?"
Lieutenant ne ya rik'e shi yana fad'in "Ya isa dan Allah karka ji mata ciwo."
Tana mik'ewa Hajia ma ta kwad'a mata mari tana fad'in "Mahaukaciyar ina ce? Baki san halin da take ciki bane da zaki mata wannan dukan? Jaka ce aka kawo miki?"
Tsayuwar rashin mutumci tayi tana ta wani girgiza da gunguni, Ummy ce ta kama Farisa ta shiga d'aki da ita tana dubata, Hajia kuma kallon Umaimah tayi tace "Bari Amar d'in ya dawo kiga yanda zanyi dake, wallahi sai kin shiga taitayinki."
Wani par-par tayi da ido tana motsa baki tana fad'in "Ya dawo d'in a sa ya yanka ni sai me?"
Wani mari colenel ya sake datsa mata a kumatu wanda yayi sanadiyar gabcewar jini daga hancinta da bakinta, duk'ewa tayi rufe da bakinta ta fashe da kukan da ko sauti babu tsabar azabar marin, cikin bala'i yayi kanta zai sa mata k'afa yana fad'in "Dan ubanki uwar tawa kike fad'awa magana? Sa'arki ce Hajia ko nine kika raina?"
Da sauri lieutenant ya rik'eshi, jinjina kai Hajia tayi kawai ta fita a d'akin, bayanta suka bi sai ita da aka bari tana kuka, suna shiga falon akayi cirko cirko ana kallon Hajia data sunkuyar da kai, Alhaji dake zaune anan bai tafi ba dama ya tambaye su lafiya, kafin wani yace wani abu Hajia ta d'ago cikin dattako tace "Ba komai, zanyi maganinta."
Tana fad'a ta mik'e ta nufi kan teburin cin abinci ta zauna, kowa cikin nutsuwa ya je ya samu kujera ya zauna, Zeituna da Zeinabu ne suka zuba abincin suka aje ma kowa gabansa, amma abun shiru babu armashi kamar anyi mutuwa, Hajia ce ta d'ago kai ta kalli kowa sai kawai tayi murmushi ta tangale hab'arta da bayan hannunta tace "Hausawa sunyi gaskiya da suka ce *duk wanda ya tuna bara baiji dad'in bana ba*, tabbas mutum baya sanin abinda yake so sai ya rasa wanda yake hannunshi, *Ammar* yana raye amma yau ranar yabon ta zo, duk da wani mawak'i yace wai *kar Allah ya kawo ranar yabo*."
Nunfasawa tayi ta d'auke tagumin tace "Dukanmu anan mun sani da yana gidan nan a irin wannan lokacin da yanzu yasa kowa dariya koda kuwa tnda fad'in wata magana ne wacce mu zamu kalleta a rashin kunya ko fitsara, ko da bamuyi dariya ba akan shirmenshi zai zamana zuciyarmu bata tunanin damuwa, amma yanzu gashi rashin shi yasa kowa abinda ya ga dama yake yi."
Saida ta sake kallon kowa tana murmushi tace "Yana son kowa a gidan nan, yana tsayawa kan matsalar data shafi kowa, yana da kirki da kuma d'ab'iu masu kyau."
Dariya tayi ta kalli Alhaji da Husseina tace "Sai yanzu na fahimci dalilin da yasa tsofaffin gidan nan bamu da hawan jini, shine maganin ashe bamu fahimta ba tun wuri."
Dariya sukayi a hankali sai Alhaji da yace "Ni nasan wannan ranar tana zuwa, kune kuka kasa fahimtarshi, amma yanzu gashi kuna fad'a da bakinku."
Cikin sanyi murya tace "Kullum mukayi waya dashi ina tambayarshi yaushe zai dawo? Amma yanda na fahimta kamar bai saka ranar dawowa ba."
Kallon Ummy tayi a raunane tace "Sa'ada dan Allah ki kira shi ki ce masa ya dawo, ya zo ko naji dad'i."
Kallonta Ummy tayi tana tunani, sai kuma tayi murmushi tace "Hajia ke ma baiji maganarki ba ya dawo bare ni."
Murmushi Hajia tayi ta kalleta tace "Ko yaron da bai mallaki hankalinsa ba yasan Ammar yana fifita soyayyarki kan ta kowa, duk yanda zai rud'e ya birkice ya fara sababi idan kika masa magana yana ji, ko hankalinshi ya gushe saboda b'acin rai indai zaki masa magana to zai bari."
Kafe Hajia tayi da ido inda wasu kalamanshi suka dinga dawo mata a kai, da jimawa ya tab'a fad'a mata cewa "Ummy na so barin gidan nan tun a waccen lokacin, amma saboda tunanin halin da zaki shiga yasa ban tafi ba, ina tsoron na barki Hajia ta dinga takura miki."
Sai kuma ranarta ta k'arshe dashi da yace "Amma duk da haka duk ranar da kika buk'aci na gareki zan zo da sauri na, saboda ke mahaifiyata ce kuma ina sonki, ina sonki sosai Ummy."