Sashe 18
Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya suka dinga yi mata har Ma'aruf ya saka rigarshi ya nufi k'ofar fita, ta gaban Salma ya bi inda take zaune k'ofar shigowar saboda abinda ta riska, ledar garin kwakwinta da sugar ya kalla yace "Gurguwa gari zaki sha? Bari idan na fita zan siyo miki kifi ki d'an ci dan nasan anjima ba'a had'u da abu mai lami ba."
Ma'aruf data zauna kan turmi ce tace "To ina za ta ga abu mai lamin, ai ta gama cinye nata rabon tun gidan waccen mutumin."
Ko da ya fita Salma ta yunk'ura da sandarta ta zauna kan tabarmarta, kallon Ma'arufa tayi tace "D'auko min kofi da cokali a d'aki."
Shiru Ma'arufa tayi kamar ba taji ta ba har saida tayi niyya ta mik'e ta d'auko mata, kawo mata tayi daga tsaye ta jefo kofin ta koma ta zauna, nan ta gyara kwakin tana ci tana kallon Ma'arufa cike da takaicin wayar da take jin tana yi da saurayi wacce batsa tafi yawa, saida tayi maganin yunwar dake damunta kad'ai nutsuwarta ta dawo jikinta, a hankali maganganun yaranta suka dinga dawo mata, sai kawai taji bata buk'atar tsayawa da yak'in daga nan, gashi tun ranar da *Tahir* ya harbe mata k'afa ta gama jinya ta dawo k'auyen nan bata sake ganin Abbas ba, tasan ba zai iya ci gaba da zama da ita ba, sai dai kuma bata san a wane matsayi take ba tunda bakinshi da bakinta bai had'u ba har yanzu, ga kuma tunanin Sameera wacce ta raina amma yanzu ta tabbatar ita ce sarauniyar gidan Abbas kuma sarauniyar zuciyarshi, da wannan tunanin ta riski wunin ranar, har saida zuciyarta ta sake durmiyata kan wani zunubin kuma, sai dai wannan karan ba ita za ta yi fad'an ba, tunda tana da yara kamar Ma'aruf da Ma'arufa, tana da yak'inin cewa su Abbas ba zasu iya shaida su ba tunda sun girma duk sun canza daga yanda suka san su, sai bayan magriba Ma'aruf ya shigo gidan da ledoji a hannu.
D'aya leda ya mik'awa Salma yace "Alk'awarin dana miki ne, ki ci kema kiji dad'i."
Sauran ledar kuma kujera yar tsugunno ya janyo ya zauna gaban Ma'arufa ya bud'e yace su ci, kallonshi Salma tayi ta kalli ledar taga gasassar zabuwa ce da kuma balangu, sai lemu mai sanyi guda biyu alamar dai shi da ita, aje ledarta tayi gefe d'aya tana kallonsu suna ci tace "Ku saurare ni da kyau muyi magana."
Ma'aruf ne kad'ai ya iya ma kallonta kuma take ya ci gaba da cin abincinshi, cikin d'aga murya tace "Da ku fa nake magana kuna jina ku min banza."
Ma'arufa ce tace "To wai ba kunne ne ke ji ba, ki fad'a mana amma ki tabbatar serious magana zaki fad'a."
"Akan Abbas ne." Ta fad'a tana kallonsu dukansu, kallonta sukayi suka ce "Kamar ya Abbas, meye faru?"
Ba alamar wasa tare da ita tace "Ku yanzu kuna son ku k'arar da rayuwarku a haka kamar ni? Ni a wahalce ku a wahalce, abincin ma sai nayi bara na samu ke kuma sai kin sayar da matancinki, kuna ganin wannan ita ce rayuwar daya kamata mu ci gaba da yi? Ku tuna fa kuna yara irin gata da soyayyar da Abbas ya nuna muku, amma haka ya rabu da ku yanzu gashi kuna cikin wahala, shin ba kwa jin kuna son kuyi wani abu a game da haka?"
"Kamar me fa?" Cewar Ma'aruf kafin ya d'ora da "Duniya na da tabbacin mu ba 'ya'yansa bane bare mu ce muna da gadonshi, ke baki kyautata masa ba bare muce zai kallemu da mutumci ko dan zaman tare da akayi, duk da dai mutum ne mai son taimako musamman matasa, amma bana jin zai iya taimakonmu saboda abinda kika masa."
Kallonsu tayi da shu'umin murmushi tace "In tambayeku mana? Shin ya zakuji ace yau kun wayi gari kun samu million ashirin ashirin naku na kanku?"
Ma'arufa ce ta saki wata k'ara tace "Wooo! Ai wallahi Hajia kud'in nan suka shigo zaki sha mamakin irin rayuwar da zanyi."
Ma'aruf kam cewa "Ai gurguwa wannan kud'in suna zuwa ni da zama nigeria kuma sai dai in nayi sha'awa kawai insa a nuna min ita ta babban majigin allon kallona dake mak'ale a gadona na alfarma."
Cike da makirci Salma tace "Dan haka kuwa zaku samu wannan kud'in cikin sauk'i inhar kukayi abinda zan fad'a muku yanzun nan, ku zaku huta, ni ma kuma zan huta."
Ai da sauri suka gyara zama suna fuskantarta suka ce "Muna jinki Hajia."
Dalla dalla Salma ta musu na abinda take son su aiwatar duk da kuwa had'arin shi da kuma muninshi, su kuma dayake magana ce ta kud'i sam basu duba komai ba musamman Ma'arufa wacce ita ce zata fi shiga had'ari tare da rasa wani abu na ta, amma a wajen su wannan ba damuwa bane idan da kud'i, saida ta gama kitsa musu Ma'aruf ya bushe da dariya yace "Kai gurguwar nan har yanzu ashe kanki da sauran wuta, ai shirin nan yayi d'ari bisa d'ari wallahi."
Ma'arufa ce ta wani girgiza gaba har saida k'irjin ta suka motsa tace "Alaji yaka ganni gaban *oga Samuel* da millon ashirin a account d'ina? Kaga a ranar zan samu 'yancina kuma zai zama kawar bawa na."
"Gaskiya kam, duba kiga yau kafin ya barmu mu taho shege kamar wani ubanmu, harda jaddada mana yake kar mu wuce gobe."
Salma ce tace "Waye kuma Samuel? Kwartonki ne ko?"
Cikin nuna rashin damuwa tace "Um um, wanda muke zaune a gidan shi ne, tunda ya bud'a ido ya ga nice hasken gidanshi ni ke kawo mi shi manyan costumer yake nanik'e min, baya so ina nisa dashi ko nan da can, kuma dama lokacin da muka je gidan ba kud'in d'aki ne damu ba, shiyasa saiya bamu d'aki a cewa shekara zan biya shi, duk da yanzu yasan ina tare da mutanen da zasu iya biya min kud'in, amma baya so na bar gidan ne shiyasa baya karb'ar kud'in har yanzu, kuma yayi hakane saboda wanda suke zuwa gurina suna masa alfarma sosai a siyasance, a ikonce da kuma arzik'ance, sannan ga kyautar da suke mishi ta fitar hankali."
Tab'e baki Salma tayi tace "Inhar kukayi abinda nace to ba Samuel ba, har wad'anda ke neman naki zaki iya had'a kafad'a da su."
Ma'aruf ne yace "Ai ki kwantar da hankalinki, kamar anyi angama ne, goben nan muna komawa zamu fara shirye shiryen komai yanda ya dace."
"Da kyau." Cewar Salma tana murmushi, haka sukayi kwanan farin ciki da tunanin samun kud'i kamar wanda suka bayar ajiya, haka gari ya waye bayan Ma'aruf ya samo musu abin kari sun gama suka shirya komawa inda suka fito, abun mamaki saiga Ma'arufa ta dunk'ulo har dubu uku ta bawa Salma ta rik'e kafin su sake dawowa, Ma'aruf kuma ya bata k'aramar wayarshi saboda su dinga kirantatana sanin abinda ke faruwa cikin gaggawa, haka suka d'auki hanyar komawa zaria kafin su wuce abuja.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Zaune yake a farfajiyar gida akan kujera yayi shiru sai dai idonshi jawur suke da wani hoto a hannunshi yana kallo, ba zai iya tantace abinda yake ji ba a game da wacce ke cikin hoton, sai dai ko ba komai yasan har yanzu yana matuk'ar sonta, amma abinda ta mishi na k'ona masa rai sosai, haka kuma wata zuciya na tuna mishi da cewa ba laifin ta bane, laifin ta d'aya shine b'oye mishi da tayi harta aureshi da cikin wani a jikinta, yana wannan halin ne k'annan shi dake bi mishi ya shigo gidan kuma kai tsaye wajen ya nufa, tsaye yayi yana kallonshi ganin hawaye na neman zubo mishi yasa yayi gyaran murya, da sauri *Abbacar* ya kalleshi tare da sanya hoton aljihun gaban rigarshi yana k'ak'aro murmushi yace " *Saleem* kai ne? Yaushe ka shigo? Ai banji shigowarka ba."
Murmushi yayi ya rumgume hannayen shi yace "To dama ina zaka ji bayan *Zeenat* ta tafi da gaba d'aya nutsuwaka."
Murmushi ya sake yi da bai kai ciki ba yace "Hmmm."
Sunkuyawa yayi ya dafa cinyarshi yace "Yaya Abbacar wai sai yaushe wannan tunanin zai k'are ne? Baka tunanin kana shiga hakk'in iyalinka dayawa? Yanzu da ace *Sayyada* ce ta fito ta sameka da hoton tsohuwar matarka wacce ta cutar da kai ta ruguza mana farin cikinmu tayi d'aid'ai da rayuwarka, me kake tsammanin zata ji a ranta?"
Murmushi dai ya sakeyi yace "Hoton Zeenat ne fa ba ita d'in ba, kuma ita kanta Sayyada ai tasan da ina kallon hoton ina kuma tuna baya."
Cikin kulawa Saleem yace "Yaya Abbacar, na fahimci har yanzu kana son Zeenat a zuciyarka, amma kuma kana jin zafin abinda ta aikata maka ko?"
Girgiza kai yayi yace "Ko d'aya Saleem, kawai dai ina tuna rayuwar baya ne."
Murmushi rainin hankali yayi yace "Karka raina min wayo mana yaya, nasan abinda kake ji a ranka mana inhar zan kwatantashi da kaina."
Kawar da kai yayi yace "Ko kad'an Saleem babu haka a raina, sai ma addu'a da nake binta da ita Allah ya mata rahama."
Tsaye ya mik'e yana kallonshi yace "Kenan kana so ka ce sam baka jin zafin cin amanar da Zeenat ta maka? Kenan ko ka tuna cewa aminin yayanta ne ya lalata ta sannan ya mata ciki wanda ta zo da shi gidanka baka jin komai?"
Tapi ya dinga yi yana dariya yana fad'in "Amma gaskiya kayi k'ok'ari yaya, kaga kuwa idan da ni ne haka ta faru dani da tuni zuciyata ta buga, dan ni ba zan iya zaunawa a duniyar nan ba ina tunanin matar da ta shigo da cikin wani k'ato gida na ba, to taya ma haka zata faru? Matata ta sunna na haskota a ido na tare..."
" Stop it Saleem, ya isa."