← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 198

Sashe 95

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa Jamila tayi da sauri ta fita daga d'akin, amma zuciyar kowa a wuya take babu wacce tayi yunk'urin dakatawa sai aikawa juna ashar suke da son a sakesu. Jamila na zuwa a falo ta samu Hajia da sauran aminanta da suka rage, saida taje kusa da ita sosai ta sunkuya ta dafa kujerar da take zaune akai cikin k'asa da murya tace "Hajia, wai Ummy tace na fad'a miki ki zo ki ma su Hamna magana fad'a suke, kuma sun rabasu sun k'i su rabu."

Wani mugun kallo ta watso mata kamar ta kashe ta da mari tare da d'aga murya tace "Dallah malama b'ace min da gani daga nan, ku mahaukatan ina ne da baku san ta kamata ba? Ina cikin mutane ne zaki zo min da wata maganar banza, to kije ki fad'a musu nace su barsu su kashe kawunansu, tunda su 'yan iska ne ba za'a fad'a musu suji ba."

Jiki a sanyaye ciki da haushi Jamila ta juya zata koma, muryar Hajia ce ta tsinta tace "Tunda sun k'i rabuwa cikin lalama kije ki kira min Ammar, shi zai ci uwar kowace sai su zauna lafiya ai."

Juyowa Jamila tayi ta kalleta, Ammar kuma? Shine abinda ta maimaita, tasan in dai ya zo to fa sai sunji jiki dukansu, to amma ya zatayi? Wucewa tayi sumi sumi ta nufi b'angaren samarin, tana daf da kaiwa ta had'u da shi ya fito da alama fita zaiyi, saida gabanta ya fad'i ita kam dan sam bata san shiga shirginshi, saida ta d'auke kallonta daga kanshi kafin tace "Yah Ammar dama Hajia ce tace wai ka zo?"

Wani farrr yayi da idonshi ya kalli wata bishiyar mai kyau ya dafe k'ugu yace "Ebola, me kuma ya faru yanzun?"

Shiru Jamila tayi bata ko kalleshi ba hakan yasa ya daka mata tsawa yace "Da wani bakinki kamar na jab'a, ba dake nake ba kika min shiru? Da gulma ce da kin fad'a ko?"

D'agowa tayi kamar zatayi kuka tace "Nima ban sani ba yah Ammar, su Hamna ne ke fad'a a ciki, kuma su Ummy sun rabasu sun k'i su rabu, shine Hajia tace na kiraka ka rabasu."

"Wato ni d'an iska ko? Ni ne zan iya rabasu kenan? Ai dama ance kowane kare ma da ranarshi."

Jamila dai satar kallonshi tayi ta juya ta barshi, take ya canza tafiyarshi zuwa ta k'akk'arfan soja mai ji da izza ya tunkari b'angaren, fuskarshi kad'ai zaka kalla ta baka tsoro ta saka fargaba da fitsari a wando, dan alamu ne na babu wasa a tare da shi, da haka ya shiga ko kallon Hajia baiyi ba ya nufi d'akin Zeituna da yake jin hayaniyar kuma ya ga Jamila ta shiga can.

*Nagode da addua'r ku mutane na, na haihu lafiya haka ma ina cikin k'oshin lafiya ni da beby Khalid, Allah ya bar k'auna masoyana.*
09/09/2020 à 17:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_28_

Yana shiga d'akin babu sallama fuska a had'e ya soma kallon Hamna da Amna, Ummy na ganinshi had'e rai tayi ita ma ta kama hannun Hamna da nufin su fita, durk'ushewa tayi cikin wani irin kuka tana fad'in "Wallahi Ummy saina daki yarinyar nan, kawai ki tafi ki barni da ita."

Sake sunkuyawa tayi zata kama hannunta tana hararan Ammar dake tsaye yana kallonta tace "Tashi muje nace Hamna, bana son taurin kai fa."

Kamar ba da ita ake magana ba saboda yanda tayi bata ji ba, a hankali ya fara zago belt d'in shi daga jikin wandonshi cikin motsa labb'a a hankali yace "Ku fita ku barni dasu kamar yanda suke buk'ata, tunda 'yan daba ne su."

Kallonshi Ummy tayi tace "Kaga malam babu ruwanka, karka kuskura ka tab'a min yara wallahi, inba haka ba kuma ranka zai mugun b'aci."

Kallon Jamila tayi tace "Ke wa yace ki kira shi? Ba Hajia nace ki kira min ba?"

Cikin turo baki tace "Wallahi aunty na fad'awa..." Shiru tayi saboda kallon da Ammar ya mata, mayar da kallonshi yayi kan Amna wacce ke tsakiyar Zeituna da Zeinabu, cikin dakakkiyar murya yace "Meya had'a ki da ita?"

Duk bala'in zuciyarta da masifar dake ciciyarta saita samu kanta da jin fad'uwar gaba, hawaye taji suna neman cika mata ido yayin da jikinta ya fara d'aukar rawa, tafin hannunta tasa ta share 'yar kwallar ba tare da tace komai ba, zaro manyan idonshi yayi masu surkin launin ja ya daka mata tsawa yana fad'in "Tambayarki nake meya had'a ki da ita?"

Rintse ido tayi sosai dan mummunar fad'uwar da gabanta yayi, dunk'ule hannunta na hagu tayi ta bud'e idonta, hawayen da take so rik'ewa ne suka zubo, cikin rawar murya tace "Kawai daga zamu sakewa aunty Zeituna kwalliya ne fa, shine tace ita ba zatayi ba nace mu zamuyi, kawai shine tace idan ban daina shiga harkarta ba zata kifar dani, daga 'yar k'aramar magana kawai saita mareni, shine ni kuma..."

Shiru tayi ta kasa k'arasawa dan tasan babu abinda zai hanashi gaura mata mari, cikin yanayin muryarshi mai firgita tunani yace "Shine ke kuma me? Kina nufin kice kika rama?"

A hankali ta d'an ja baya tana k'yak'yabta ido da turo baki irin eh nima ramawa nayi, ba tare daya kula dasu Zeinabu ba yasa hannu ya jawo hannunta ya direta gabanshi, kallon Ummy take tana so ta bashi hak'uri kar ya daketa, cikin tsawa yace "Kalleni nan."

Matsakaitan idonta ta zuba cikin nashi, amma ina tsabar kwarjininshi da tsoronshi yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa hawaye na zubowa, sake daka mata tsawa yayi yace "Kalleni ido cikin ido, inba haka ba zan gurguntar dake a wurin nan wallahi, kin dai ji na rantse miki."

Kallonshi tayi cikin idon amma hawayen dake ambaliya sun kasa barinta ta fahimci asalin mugun kallon da yake mata, cikin saisaita murya yaja kunnenta sosai yace "Amna wannan sa'arki ce? Tsararki ce ita? Shin ba tana gaba dake ba?"

Bayan hannu tasa tana shan majinar wahala ba tace komai ba, sake murd'e kunnenta yayi yana fad'in "Bani amsa mana ina jinki."

Rintse ido ta sake yi saboda yanda taji har fitsari na k'ok'arin taho mata bata shirya ba, girgiza kai tayi hakan yasa yace mata "K'adangaruwa ce ta haifeki da zaki dinga juya min kai?"

Cikin masifar jin zafin murd'e mata kunne ta sake girgizawa da k'arfin ta tana fad'in "A'a, a'a nace, dan Allah kayi hak'uri yah Ammar."

Turata yayi gaban Hamna yana fad'in "Maza to bata hak'uri kafin ranki ya b'ace."

Juyowa tayi ta kalleshi alamar bata gane ba, belt d'in hannunshi ya gyara yana fad'in "Ko ba zaki bata hak'urin ba ne kike kallona haka?"

Zeinabu ce tace "Ke Amna bansan taurin kai, ki ba yar uwarki hak'uri komai ya wuce."

Ummy ce tayi saurin cewa "Bata hak'uri kinji, shiyasa tun farko na so ku sulhunta kanku kafin kuji ba dad'i."

Yanda ta had'e fuskarta zai nuna maka tabbas zata bayar da hak'urin ne dan anfi k'arfin ta, amma ba dan haka ba ba zata bayar ba, wata harara ta gallawa Hamna da har yanzu ke durk'ushe tace "Kiyi hak'uri."

Tana fad'a ta juya da gudu ta bar d'akin ranta b'ace, cikin takon izza ya dawo gaban Hamna yana kallonta yace "Ke kuma malama kada ki sake saurin d'aga hannunki kika dakar min amarya dan ba jaka bace, bare har ki mareta a fuska wajen da yafi komai daraja, ko ni dole zan koyawa kaina yanda zan dinga tausar kaina ba tare dana mareta a fuska ba saboda tsaro, sannan 'yer uwarki ce ita kamata yayi ku zama kamar aminan juna."

Tunda yace amaryarshi Hamna ta d'ago kai da sauri, haka kawai taji kalmar ta daki zuciyarta sosai, sam bata ji dad'in maganar daya fad'a ba, mik'ewa tayi da niyyar zazzaga masa masifa, dan dama saurin hushin nata ya samo asali ne daga abinda ya mata, shiyasa har ta biyewa yar uwarta sukayi cacar baki, sai dai yana ganin ta mik'e ya juya ya bar d'akin da sauri yana mayar da belt d'in shi, ita ma bayanshi ta bi ta fita daga d'akin haka ma su Jamila da Umaimah, Zeituna kad'ai aka bari tsaye jikinta yayi sanyi ta rasa akan me zatayi tunani, a hankali taja k'afa ta koma ban d'akin ta cire katan jikinta ta shiga wanka, sosai ta jima tana goga sabulu mai dad'in k'amshi wanda taga har wata madara-madara ke fita tsabar kyawun sabulun (Dove kenan), tana idawa sabon maclean da brush data gani ta d'auka ta tsabtace hak'oranta kafin ta fito, mai ta shafa ta shafe jikinta da humra data gani a gaban madubinta sannan ta samu turare ta feshe jikinta, babu abinda ta shafa bayan wannan sai nufa da tayi wajen kaya ta fara dubawa, dama dai lefen da aka mata gaba d'aya guda bakwai ne aka d'inka mata wanda zata fara sakawa, kuma kaf d'inki babu mai kyawun wanda su Umaimah suka dare, dan haka kawai ka d'auki doguwar bak'ar riga ta saka wacce ke cikin lefenta mai kyau ta saka, ita kanta data tsaya gaban madubi sai taga ta canza, duk da babu kwalliya a fuskarta, amma ta haska tayi kyau komai nata ya fito, hatta hasken fatarta ya k'ara fitowa, kallabin kayan ta d'ora ta k'ara fesa turare sannan ta zauna kan gadon tana k'arewa d'akin kallo.

*Bayan wasu awanni* gidan yayi shiru sosai alamar kowa ya kwanta huta gajiya, lieutenant ne da kanshi ya shigo gidan, Alhaji na zaune a farfajiyar gidan, ledar dake hannunshi ya d'an b'oye bayanshi ya durk'usa yace "Alhaji barka da hutawa."

Cike da dattijantaka ya amsa da "Barka Babba, anshigo?"

"Eh Alhaji." Ya amsa kanshi k'asa, jinjina kai yayi yace "To ya hidima?"

"Alhamdulillah, ya gajiyarku?" Amsawa yayi da "Angode Allah."

Cikin girmamawa ya amsa da "Allah ya k'ara girma."

Mik'ewa yayi yana fad'in "Ni zan shiga ciki Alhaji, saida safenku."
Chapter 95 · 0% Book details