← Book details Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 198

Sashe 38

Badak'ala Complète Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo suka bishi dukansu banda d'iyar baba data duk'e kai tana zubar da hawaye, hak'ik'a yaron nan ya birgeta dan ya fad'i abinda shekaru ta kasa fad'a, tabbas ta gane kuskuren da tayi a waccen ranar na yi wa Mari baki, amma ba'a je ko ina ba ta gane kuskurenta, sai dai ina mahaifiyarta ta d'auki zafi sosai dole taja baki tayi shiru, shiyasa ma har idan aka d'auko maganar mari take nuna kamar ita ma ranta a b'ace yake da ita, amma kullum addu'ar ta bata wuce Allah ya dawo mata da ita gida ba, kaka da ita ma sai lokacin ne taji jikinta yayi wani bala'in sanyi har hannayenta sunyi nauyi, tunanin abinda ya fad'a take, a hankali ta juya ta kalli d'iyar baba dake kuka, cikin harshensu tace "Ki kalleni d'iyar baba."

Saida ta gama shan majina da share hawaye kafin ta d'ago ta kalleta lokaci d'aya kuma tayi k'asa da kanta, juyawa kaka tayi ta kallesu tace "Dan Allah ina Mari take yanzu?"

Junaid ne yace "Tana Maradi."

"Kenan can ta tafi bayan munyi watsi da ita? To me take yi acan, wurin kakanta take malam Rabi'u ko kuma Khadi?"

Da mamaki Junaid ya kalleta, idan zai iya tunawa Iklima ta anbaci sunan nan, amma kuma a yanda tace ba mazauni ne shi ba, da wannan mamakin yace "Dama kakan nata acan yake?"

Cikin sanyin murya tace "Ba can yake da zama ba, amma yana da iyali acan saboda yana yawan zuwa can wajen harkokinshi."

D'orawa tayi da "Dan Allah in da gaske kana sonta ka ce mata ta dawo gida, wallahi a yau d'in nan na gane duk kuskuren nawa ne, bai kamata mu mata haka ba, amma ku fad'a min me take yi acan? Wajen wa take zaune?"

Junaid ne ya kalli Amar da Jibril kafin ya kalleta yace "Insha Allahu Hajia zan zan dawo miki da ita gida, na jima ina son Mari ta amince da soyayya ta, amma ta k'i yarda dani saboda waccen abun ma daya faru sam babu laifinta , tayi ne dan ceto rayuwar mahaifinta, da kuma ceton mahaifiyarta daga shiga takaba, yanzu haka ma bata san zamu zo nan ba, wata k'awar ta ce ta taimaka mana har muka zo nan, ina so na koma mata da tabbacin kun bar hushi da ita, idan har ta amince ta dawo to zan zo nan na nemi aurenta, dan nan d'in shi ya fi dacewa dana nemi aurenta."

Kamar daga sama d'iyar baba ta kalleshi tace "Ya cikin data tafi dashi? Ta haife shi?"

Cikin sanyin jiki yace "Ta haife shi Mama, 'yarta tana nan mai wayo sannan mai kama da mahaifiyarta, yarinya ce mai shiga rai."

Sake fashewa tayi da kuka harda rufe baki cikin kukan tace "Dan Allah ku ce ta dawo, ina son ganinta ita da abinda ta haifa, ku bata hak'uri dan Allah, nasan bamu mata adalci ba da muka koreta, bamuyi tunanin halin da zata shiga ba idan ta var gida, watak'ila ma taje ta fad'a karuwanci."

Shirun da sukayi yasa tayi shiru ta kallesu, ganin babu wanda yace mata komai yasa tace "Zaman kanta ta shiga?"

A hankali Amar yace "Mama karki damu, insha Allahu zata dawo gareki, dama mu abinda ya kawo mu kenan."

Kaka ce tace "Abinda kukayi ya nuna mana ku 'ya'yan manyan mutane ne masu dattako, da ace ni na haifi uban Mari wallahi da yanzun nan zan baka Mari halak malak, amma bana da wannan ikon tunda tana da dangin mahaifi, duk da suma sun k'i karb'arta a lokacin da mummunar k'addara ta sameta, amma dole hakk'in su ne mu sanar dasu abinda ke faruwa, anyi sa'a malam rabi'u yana garin nan, dan haka yau ba sai gobe ba zanje da kaina na sanar dashi duk abinda ke faruwa, idan zai yiwu ma sai muje tare daku wurinshi."

D'an kallon juna sukayi kafin Jibril yace "Ba damuwa Hajia, zamu iya tafiya dan ba anan zamu kwana ba, muna so ne mu sake komawa gida."

Da mamaki tace "Amma yaran nan kamar ana korarku, wannan doguwar tafiyar kawai dan wuni d'aya."

Nan dai suka nuna mata eh fa komawa zasuyi, dan haka tace bari ta shirya saita fito su tafi, d'aki ta shiga ta sauya kaya da mayafi ta shafo turare na barebari mai dad'i ta fito, nan suka mik'e suka wa Mama sai sun dawo, suna fitowa Ammar na cikin mota zaune da waya a kunne, Amar dai a zuciyar shi cewa yayi "Mai abun tsiya dana kirki, da kana da budurwa da sai nace da ita kake waya."

Junaid ne ya bud'e ata gida gaba ta shiga ya rufe, baya suka shiga su uku Ammar yaja motar ba tare da sanin inda zai nufa ba, mutanen da suka fito ganin k'wam ne suka koma tsegumi an tafi da *Magaram*, su kuma suna hanya ta dinga nuna musu wurin da hausarta da basu cika ganewa ba har suka isa dan babu nisa sosai ma tsakaninsu, sunyi sa'a samun malam rabi'u a d'akin shi na soro yana rubutu da allo, nan ma gaisawa sukayi za'a kawo musu ruwa suka ce a'a sun gode, cikin harshen barbarci kaka ta dinga mishi bayani, sun d'an jima suna hira wacce tasa suka fara tsarguwa musamman yanda suka ga malamin yana d'an d'aga murya yana magana cikin fad'a-fad'a, Ammar da ranshi ya gama b'acewa ne yace "Dan Allah ko zaku iya yin yaren da zamu fahimceku? Ko kuma idan maganar bata shafe mu ba ku fad'a mana sai musan inda dare zai mana, amma mu ba k'ananan yara ba, ba kuma jahilai ba mu zauna kuna yi damu."

Kallonshi kaka tayi, ita dai duk da ta lura yaron yana da yan matsaloli amma kan daya wayar mata yasa yake birgeta, malam rabi'u kallonshi yayi, (kunsan barebari da fad'a da zuciya) sai kawai ya ga ai tsagwaron marar kunya ne wannan, dan haka ya kalleshi da kyau yace "Magana nake a kan ku, shin ku su waye? Su waye iyayenku a duk garin maradi? Ina kuka san Mari?kuma kuna nufin kun zo neman auren Mari ne ko me? Ina iyayenku suke da ba zaku turo su ba? Ina son sanin amsar wannan tambayoyin yanzu daga bakinku."

Duka gira Ammar ya d'aga sama alamar mamaki ido bud'e sosai, gyara zamanshi yayi yanda zaiji dad'in magana, lura da hakan da Amar yayi yasa shi kallonshi yana mishi kallon "Karka siyar mana da halinka dan Allah ko dan Junaid."

Cike da jin masifa yace "Kai jira zan bashi amsa ne kawai, to ko tsohuwar gidanmu dake da k'wank'wamai ai ina ji da ita bare wannan malamin."

_Yan uwa a yanda labarin gasken ya kasance saboda Ammar yasa aka sha daga sosai kafin rabi'uya ya amince da auren Junaid da Mari, dan yace yaron k'arshen marar kunya ne bashi ba wannan zuri'ar, amma saboda yanayi yasa zan tak'aita masifar dan akwai abubuwa dayawa anan gaba da zasu faru._

Kallonshi Ammar yayi harda alama yake mishi da hannu danya gane yana fad'in "Ni, da wannan da kake gani, uwar mu d'aya ubanmu d'aya, ince dai a garin maradi kasan lieutenant Hassan Gaga? To in ma baka sanshi ba ka tambaya zaka sani, duk wani mai shige da ficen kaya zaisan waye lieutenant Hassan, dan shine babban douanee a garin nan, idan bai yarda ba sai kayanka su shekara dubu a ajiye kuma a wulak'ance."

Nuna Junaid yayi yace "Shi kuma wannan d'ane ga colonel Hussein Gaga, shi ma d'in idan baka sanshi ba ka fara kallon tv zaka san waye shi, ko kuma ka zama d'an tada k'ayar baya a cikin al'uma zaka fahimci waye shi."

Nuna Jibril yayi yace "In dai har garin maradi kake tabbas zaka san d'an kasuwa Labaran Gaga, wanda yan kasuwa suka bashi matsayin chairman d'in su, dan haka tsoho karka d'auka wata bishiya ce aka girgiza muka fad'o, da kuma nayi niyya wallahi ba zan zo nan da niyyar neman aurenta ba kawai, sai dai na zo da sadakinta a d'aura auren mu tafi da matarmu."

Malam rabi'u da al'amarin ya gama zund'umeshi shima kallonshi yayi zaiyi magana sai kuma Ammar yace "Kuma ka tambaye mu wai ina muka had'u da ita? Ai ina ga kamar kunfi kowa sanin inda zamu had'u da ita tunda kun koreta daga gareku, kenan ina kuke son tayi rayuwa?"

A hassale malam rabi'u yace "Ka ce idan da kayi niyya da zaka zo da sadakinta? To jini da kyau marar kunya fitsararre, ni kuma bawai ina raye ba, wallahi ko bayan ba raina auren Mari ya haramta gareku, dan ga dukkan alama baku samu tarbiyya a gidanku ba, na ga kuma shafaffe da man daya isa a kaf dangin nan nawa daya isa ya d'aura auren Mari ba da amincewa ta ba."

Wata dariya Ammar ya shek'a wacce ko hak'oran shi basu fito ba sai sautin kawai kafin ya tsagaita yace "Ni kuma Ammar in dai har d'an uwana Junaid bai janye k'udirinshi na son auren Mari ba, na rantse da Allah ko saceta ne sai nayi na kuma d'aura musu aure."

"A matsayinka nawa? Kai bari dai in mik'e kaga tsawona" Cewar malam rabi'u yana mik'ewa tsaye, Ammar na kallon idonshi yace "A matsayina na yayanshi, zan uya wakiltar iyayenmu akan al'amarin daya shafi dukansu nan, saboda babu wanda ban bawa watanni da haihuwa ba."

Jibril da shi dai tun shigowarsu yaji gabanshi sai fad'uwa yake, yana kallon tsohon kuma sai yake ganin wani yanayin mahaifinshi a tare da mutumin, baisan dalili ba amma yaji tsohon ya shiga zuciyarshi daga *kallo d'aya*, tunda suka fara musayar yawun nan yake jin baya jin dad'in abinda Ammar d'in keyi, yanzun ma mik'ewa yayiya kama hannun Ammar ya matse sosai ya kalli tsohon yace " Dan Allah kaka kayi hak'uri, yana da zuciya ne."
Chapter 38 · 0% Book details